Sunday, 29 May 2016
Mariya Abdullahi Da Kungiyoyin Mata Sun Ta Karrama Gwamna Masari
Gwamna Aminu Bello Masari ya jaddada kudurin wannan Gwamnati na kyautata rayuwar mata tare da daga martabarsu a wannan Jiha.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a wani taro da wasu kungiyoyin mata suka shirya domin karrama shi tare da Mataimakin shi Alhaji Mannir Yakubu.
Ya kara da cewa tun da wannan Gwamnati tazo, ta maida hankali ne wajen warware matsalolin da ta gada daga Gwamnatocin da suka gabata. Inda a matakin Gwamnatin Tarayya aka ciwo kan rikicin Boko Haram a nan Jiha kuma aka ciwo kan matsalar barayin shanu.
Gwamna Masari ya kuma yi godiya ga wadannan kungiyoyi tare da tabbatar masu da cewa da yardar Allah wannan Gwamnati ba za ta kunyata al'ummar Jihar nan ba musamman wadanda suka zabe ta.
Saturday, 28 May 2016
Gwamna Masari Zai Mayar da Ma'aikatan Kana nan Hukumomi Malaman Makaranta
Gwamna
Aminu Bello Masari ya bada umurnin cewa duk wani ma'aikaci da aka gano yana
amsar albashi daga Gwamnati alhali kuma yana aikin albashi a wata hukuma dabam,
to ya dawo wa Gwamnati da kudin ta.
Gwamnan ya bada wannan umurni a lokacin da kwamitin tantance Ma'aikatan kananan hukumomi ya mika rahoton shi.
Gwamnan ya nuna matukar rashin jin dadin shi ganin yadda wasu mutane suka maida almundahana da kudin al'umma abin ado da tunkaho. Ya kuma kara da cewa wadanda suke wannan aika-aika suna sane haka kuma akwai wadanda suke taya su tare da daure masu gindi. Saboda haka, Gwamnati za ta dauki duk matakin da ya dace wajen hukunta wannan gungun mutane marasa kishin al'umma. Ya kuma bayyana cewa duk wani gurbi da aka samu ta wannan tantancewa da akai to za a cike shi ne ta hanyar daukowa daga cikin Ma'aikatan wucin gadi (Casual Staff) da suke aiki a wurin.
Tun farko a nashi jawabin, Shugaban Kwamitin Alhaji Maigari Salihu Danjuma mni, ya shaida wa
Gwamnan cewa sai da suka ziyarci wasu kananan hukumomin kuma suka tattauna da ma'aikata domin tabbatar da sun bada rahoto mai inganci.
Ya kara da cewa sun sami;
1. Ma'aikata Dari Shidda da Sittin da Biyar (665) wadanda suke da takardar shaidar Malanta amma suna zaune a ofisoshi cikin kananan hukumomi, amma yanzu haka suna kan aikin yadda za tura su Makarantu domin ci gaba da koyarwa kamar yadda ya dace.
Gwamnan ya bada wannan umurni a lokacin da kwamitin tantance Ma'aikatan kananan hukumomi ya mika rahoton shi.
Gwamnan ya nuna matukar rashin jin dadin shi ganin yadda wasu mutane suka maida almundahana da kudin al'umma abin ado da tunkaho. Ya kuma kara da cewa wadanda suke wannan aika-aika suna sane haka kuma akwai wadanda suke taya su tare da daure masu gindi. Saboda haka, Gwamnati za ta dauki duk matakin da ya dace wajen hukunta wannan gungun mutane marasa kishin al'umma. Ya kuma bayyana cewa duk wani gurbi da aka samu ta wannan tantancewa da akai to za a cike shi ne ta hanyar daukowa daga cikin Ma'aikatan wucin gadi (Casual Staff) da suke aiki a wurin.
Tun farko a nashi jawabin, Shugaban Kwamitin Alhaji Maigari Salihu Danjuma mni, ya shaida wa
Gwamnan cewa sai da suka ziyarci wasu kananan hukumomin kuma suka tattauna da ma'aikata domin tabbatar da sun bada rahoto mai inganci.
Ya kara da cewa sun sami;
1. Ma'aikata Dari Shidda da Sittin da Biyar (665) wadanda suke da takardar shaidar Malanta amma suna zaune a ofisoshi cikin kananan hukumomi, amma yanzu haka suna kan aikin yadda za tura su Makarantu domin ci gaba da koyarwa kamar yadda ya dace.
Tuesday, 24 May 2016
Hon. Sani Saidu Ya Tallafawa Mutum Sama Da 300 A Mazabarshi.
Dan majalisar tarayya mai wakiltar Daura Sandamu da Mai'adua Rt. Hon. Sani Sa'idu fago ya bayar da tallafi ga mutanen mazabarsa a ranar talata 24/05/2016. Tallafin da ya hada da babura, kekunan dinki, generators, keke napep,da sauransu, ya bayar dasu ne ga mutanen da suka kai akalla sama da dari uku.
A yayin bada wannan tallafi Dan majalissar yayi kira ga wadanda Allah ya cida suka samu morar wannan tallafi da su tabbatar sunyi amfani dashi ta hanyar data dace don acewarsa hakan ne zai kara masa kwarin gwiwar cigaba da aiwatar da irin wannan tallafi. ya kuma kara da kira da wandanda Allah bai sa sun shiga cikin wannan tsari ba da su dan kara hakuri akwai tanade tanade da dama makamantan wannan da yake da niyyar aiwatar ga mutanen wannan mazaba tasa wanda acewarsa shirin zai amfanar da dinbin mutane a mazabar tasa. Ya furta cewar yana matukar alfahari tare da jinjinawa al'ummar mazabarsa bisa hakuri da juriya da suke nunawa game da halin da gwamnatin tasu ta samu kanta.
hakan ne ma yasa ya bukaci mutanen mazabar tasa da su cigaba da bawa gwamnati hadin kan da Yakamata kamar yadda suka saba tareda yi mata addu'ar Allah ya bata ikon aiwatar da dukkanin shirye shiryen inganta rayuwar talakan Nigeria data kudiri niyya kuma ta tsayu akan hakan karkashin jagorancin adalin shugaba Muhammadu Buhari.
A zantawar da Cliqqmagazine.blogspot.com tayi da wasu daga cikin wanda suka samu nasarar morar wannan romon demokaradiyyar sun bayyana matukar farin cikin su da Jin dadinsu bisa ga wannan kulawa da suka samu daga wakilin nasu. Daya daga cikin jadanan raba wannan tallafi Alhaji Sani Ali Jarkuka ya jinjinawa dan majalissar bisa ga wannan namijin kokari da yayi tareda kira akan cewar ya zama wajibi ga yan siyasa zababbu dama masu rike da mukaman siyasa a gwamnati cewar lalle su rika daurewa suna jibintar al'amuran jama'a ta hanyar tallafa masu gwargwadon iko ko sun samu sassaucin rayuwa. Duk wanda ya tallafa ma wani to Shima fa Allah zai jibinci lamuransa yasa albarka a cikin sha'anin mulkinsa da dukiyarsa.
Saturday, 21 May 2016
Gwamna Masari Ya Halarci Kulle Mauludin Inyass a Katsina
Gwamna Aminu Bello Masari yayi kira ga Malamai da sauran al'umma da mu kara jajircewa wajen yi wa kasar mu da ma duniya baki daya addu'a domin samun dawwamammen zaman lafiya da karuwar arziki.
Gwamnan yayi wannan kira ne wajen rufe taron Maulidin Sheikh Ibrahim Inyass na wannan shekara, wanda ya gudana a filin wasa na Muhammadu Dikko dake nan Katsina.
Friday, 20 May 2016
SIRRIKAN LAFIYAYYAR RAYUWA GUDA 10
1. Ci nama kadan kaci ganye da yawa.
2. Ci gishiri kadan ka sha khal.
3. Ci abinci kadan kasha ruwa da yawa.
4. Sikari kadan 'ya'yan itatuwa da yawa.
Thursday, 19 May 2016
Kungiyoyin Matasa a Malumfashi Sun Nuna Goyon Bayan Cire Tallafin Man Fetur
A yau alhamis ne 19/5/2016 gamayyar kungiyoyin matasa karkashin jagorancin kungiyar malumfashi Youth development association suka gudanar da nasu gangamin nuna goyon baya dangane da cire tallafin Man fetur da gwamnatin tarayya tayi wanda a dalilin kalubalantar hakan da kungiyar kwadago ta kasa ta keyi yasa ta aiwatarwa da tata zanga zanga tare da shiga yajin aikin sai baba ta gani wanda bisa alamu kungiyar kwadagon bata samu irin goyon bayan da ta saba samu a baya ba.
A tabakin shugaban kungiyar Malumfashi Youth Development Association kuma daya daga cikin manyan jadanen wannan zanga zanga Hon. Ahmad Nasir Lara yayi tsokaci da cewa ita wannan gangami ne don nuna goyon bayan su da matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na cire tallafin Man fetur dalilin su kuma shine tunda Sune suka zabi wannan gwamnati a dalilin sun aminta da ita saboda haka wajibin sune su bata cikakken goyon bayan da take bukata ga duk wata manufar ta mai kyau ga al'umma don ta samu damar yin nasarar kawo Canji da suke bukata.
Tuesday, 17 May 2016
Labaran gaskiya cikin raha: Sadakar Mazakuta

Thomas Manning ya zama mutumin farko a Amurka da
aka fara yima dashen zakari [penis transplant] a wata cibiyar lafiya ta Boston .
Dashe kuma ? Ah! Eh mana, amma bana shuka ba na
jijiyoyin mutum, ina nufin an bawa Thomas Manning sadakar al'aura (zakari).
Kai! Da gaske sadaka , ban gane ba? Kwarai kuwa, sadakar al'aura sakamakon
ciwon-daji daya jaza rashin al'aurarsa wacce aka yanke a asibiti shekaru 3 da
suka gabata.
Sanatan Daura Zone Ya Dauki Nauyin Koyawa Mata 3600 Sana’oi Tare Da Basu Jari
Sanatan Daura zone Engr. Mustapha Bukar fnim (madawakin Daura) ya fito da wani gagarumin shirin koyawa mata 3600 sana'oi tareda da basu tallafin jarin da zasu fara wadannan sana'u da zarar sun kammala amsar horo. wanda hakan zai basu damar dogaro da kansu harma su koyama wasu. An kaddamar da wannan shirin koyan sana'a a garin ingawa bisa jagorancin senata mustapha Bukar wannan bukin kaddamarwa ya samu halartar manya manyan yan siyasar jihar nan musamman daga bangaren mata.
Sana'oin da za'a koyar dai sun hada da: Koyar da yadda ake yin sabulun wanka dana wanki, Man shafawa, Dettol, Air freshener, Hoda da Maganin kwarin da suka hada da sauro, Kuda, kyankyaso da sauran su da yadda ake kera murhu na zamani don magance yawan amfani da itace. Wannan sana'u dai wani kamfani da ya shahara wajen koyawa mutane sana'un dogaro da kai mai suna ICT Global plus Sanata Mustapha Bukar ya dauko hayarsu don su koyarwa mata musamman iyayen marayu dama mata marayu, zawarawa, mata masu karamin karfi da sauran ire irensu da suka fito daga mazabarsa ta Daura zone.
Monday, 16 May 2016
Tattakin Goyan Bayan Cire Tallafin Man Fetur A Daura

A zantawar da Cliqqmagazine.blogspot.com tayi da daya daga cikin jadanan tattakin Malan Rabe
Amfanin Na'a-Na'a Ga Lafiyar Dan Adam- Madinah Islamic Medicine
Na'a-na'a [Peppermint/mentha piperita or mint] wata
shuka ce mai albarka da ake amfani da ita a matsayin maganin gargajiya. Ganyen
na'a-na'a kore ne, kamshin ta nada karfi, tana da kamshi mai dadin gaske da
filebo mai sanyaya rai. Na'a-na'a nada sinadarin 'minti' ( wato 'menthol') mai
sanyaya rai da lafiyar jikin dan adam. Akanyi amfani da na'a na'a wajen sarrafa
wasu kayan amfanin gida da muke siya na yau da kullum, wato kayan amfani da
muke siya a kasuwa kamar irinsu makilin (toothpaste), sabullai (soaps),
man-shafawa (creams and vaselines), cingam (chewing gum), sinadarin wanke baki
(mouthwash) , magungunan shafawa (ointments), da sauransu , saboda kamshinta da
amfaninta ga jikin dan adam.
Bincike ya nuna cewa, shukar na'a-na'a dai ta samune asali ta hanyar auren-shuka , wato auren shuka mai suna 'watermint' da turanci da kuma wata shukar mai suna 'spearmint'. Bincike ya nuna cewa na'a na'a tazo ne daga kasashen turawa da larabawa. Mutanen wadannan kasashen da muka ambata kanyi amfani da ganyen na'a-na'a cikin abinci da kuma wajen shayi, a matsayin ganyen-shayi (tea leaves) haka kuma, akwai man -na'a na'a ( peppermint oil) da ruwanta (peppermint water) a kasuwa domin amfani na daban-daban.
Sunday, 15 May 2016
Karanta Sakamakon Taron Kungiyar Gwamnoni Yammacin Najiriya Dasu Gabatar a Kaduna
Taron kungiyar Gwamnonin Arewa maso Yammacin kasar nan yana ci gaba da gudana a Gidan Gwamnatin Jihar Kaduna a karkashin jagorancin Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari.
Taron wanda ya sami halartar Gwamnonin shiyyar, zai tattauna ne kacokan a kan harkar aikin Gona.
A jawabin shi na budewa, Gwamna Masari ya bayyana cewa an gayyato Kwamishinoni, Manyan Sakatarori da kuma Daraktocin Aikin Gona na jihohin da ke wannan shiyya.
Mutane Sun Fara Kuke A kan Hanyoyin Da HON.Abdulkadir Nasir Ya Zaba Don Tallafawa Jama'a
Korafi ya fara bayyana game da mai ba Gwamna
shawara akan tattalun ariziki da kuma tallafa wa kana nan masana’antu Hon.
Nasie Abdulkadir. Mutane na korafin cewa bai bin hanyoyin da su ka dace domin
tabbatar da shi a yanda day a dace.
Ga misalin irin magan ganu da mutane suke yi.
“Hon. Nasir Abdulkadir,
Kasani ba kai kadai bane SA da aka ba janragamar bada bashi ga matasa da masu Kananan masana'antu.
Kasani ba kai kadai bane SA da aka ba janragamar bada bashi ga matasa da masu Kananan masana'antu.
Salon daka dauka nabayar da bashin bakabi hanyar
adalciba wanda hakan xai iya jama maigirma gwamna matsala da sauran alumna.
KAJI TSORON ALLAH”.
KAJI TSORON ALLAH”.
Kakakin Majalisar Jihar Katsina Yayi Ma Malaman Wata Islamiya A Daura Ba Zata
A jiya ne 14/5/2016 madarasatul Shababul khairi kofar Arewa dake a garin Daura ta gudanar da walimar yaye dalibai dari hadu da suka samu damar sauke alkur'ani mai tsarki tare da karin wasu daliban talatin (maza ashirin mata goma) yan kasa da shekara sha biyu da suka samu damar hardace Alkuri'ani a cikin shekara biyu haka kuma da karin wasu dalibai matasa goma da suma suka samu damar hardace kur'anin gaba daya.
Wannan walima anyita ne akan jimlar dalibai dari hadu da arba'in da wannan makaranta ta yaye a karkashin shugabancin sheikh Malan Mansir Kamar yadda wakilin shugaban makaranta wato Malan Aliyu Salisu ya shaidawa Cliqqmagazine.blogspot.com cewar Malamai da dalibai na wannan makaranta harma da iyayen yara sun yaba kwarai da gaske kuma sunyi mamaki matuka da yadda kakakin majalisar jihar katsina Rt Hon Aliyu Sabi'u Muduru ya gudanar masu da jawabai masu matukar muhimmanci cikin harshen larabci da yadda ya nuna masu gamsuwarsa dangane da yadda ake gudanar da makarantar da kuma kulawa ta musamman da ya basu wajen bada lokacin sa don halartar wannan muhimmin taro, hakama sun yaba da irin shawarwari da yaba malamai da dalibai harma da daukacin al'umma dangane da muhimmancin neman ilmin addini sun nuna farin ciki kwarai dangane da hakan.
Yaushe Jami'an Gwamnati Zasu Fara Zuwa Asibitoci Na Gwamnati-Mallam Mansur
Wai yaushe jami'ai da mukarraban
gwamnati zasu fara zuwa asibitoci mallakar gwamnati idan basu lafiya su da
zuriyar su?
Lafiya da ilimin al'umma abubuwane
masu muhimmanci a rayuwa dan babu abinda ke yiwuwa saida lafiya koda lafiyar
kuma saida ilimi, ya kamata kamar yadda adalin shugaba gwamnan wannan jihar
yasha alwashin maida ya'yayenshi makarantun al'umma mallakin gwamnatin jihar
mungani ya aiwatar alhamdulillahi muna godiya.
Abu na biyu da muke fatan gani
shine ziyartar asibitoci mallakar gwamnati yayin rashin lafiya wannan ko shakka
babu zai inganta yanayin aiki a wadannan asibitocin, tare da farfado da
asibitocin daga mummunan yanayin da suke ayau.
Labarin KARSHEN MADIGO Ya Karkato da Zuciyar Fatima Sadik Al – Ameen. daga Sani Hamza Funtua
“Babu abinda nafi kauna a Rayuwata ayi min Kyauta [Gift] dashi kamar Turare. Na fara Madigo bayan na shaki kamshin turaren da Zara ta bani a matsayin kyauta dashi, daga wannan ranar duk abinda take so inayin shi ba tare da ko Musu ba”
***** ***** **** ***** ***** *****
Kamar misalin kwana biyu da yin rubutun ci gaban labarin Karshen Madigo kashi na Goma sha Hudu, ina cikin dakina ina aikin Littafin wata baiwar Allah data kawomin, wayata ta dauki ruri da neman agajin gaggawa,jin wayar ta isheni nima yasa nayi hanzarin dauka tare da karawa a kunnena.
“Salamu Alaikum” Na ce cikin kaguwa d agama wayar don ci gaba da aikin da nikeyi.
Muryar mace ta amsa sallamar, muka gaisa cikin girmamawa, a nan ne ta fara tambayata.
“Dan Allah ko kaine Sani Hamza Funtua marubucin Littafin Karshen Madigo?”
Na amsa da “Hakkun nine, ina fatan dai lafiya”
Tace “Lafiya lau, daman a kiraka ne in gaishe ka kuma in jinjina maka akan wannan namijin kokarin da kakeyi ba tare da nuna tsoro ko fargaba ba, duk da cewa naga kace wata Hajiya Babba ta kiraka tare da yi maka barazana. Nayi tunanin kiran nata zaisa ka dakata da labarin kamar yadda ka rubuta, sai kuma naga kaci gaba, hakan yasa zuciyata ta narke da al’amarinka.”
Na nisa kana nace “Aiko na gode kwarai ‘yar uwa”
Tace “Kasan nima na taba shiga irin wannan rayuwa, koma dai ince har yanzu ina kafa daya ciki—kafa daya waje.”
A nan ne na gyara zama da tambayarta.
“Kin taba shiga wannan rayuwar kamar ya ke nan? Kina nufin kema kinyi rayuwa ta Yan Lesbian?”
Ta amsa da “Kwarai kuwa nayi. Na kiraka ne musamman dan tattaunawa dakai, wata kila a cikin labarin nawa ka samu wani abun amfani da zaka kara sawa a cikin labarinka, ko ba komai na sanarwa duniya gaskiya koni wacece a baya, yadda na shiga wannan harka da kuma kiran da zanyiwa ‘yan uwana mata.”
Thursday, 12 May 2016
JANYE TALLAFIN MAN FETUR- Malam Mansur
Abin Da Mutane Suka Kasa Fahimta Kamar yadda gwamnatin Tarayya ta bada Sanarwar
cire tallafin Man Fetur a wannan rana ta Laraba 11-may-2016 kamar yadda Minista
a ma'aikatar Man-Fetur din Mr. Ibe Kacikwu ya sanar. Abinda wasu mutane basu
fahimta game da wannan al'amari ba shine. Shi Man bawai ana nufin farashinsa
zai kama daga Naira 145 kwatsam a ko ina bane.
A'a Abinda ake nufi anan shine Masu Gidajen man
'yan kasuwa an lamince musu su shigo da man daga duk inda suke so. Amma dukkan
Man 'yan kasuwa zasuna sayar dashi akan Farashin da bazai taba haura Naira 145
ba.
Amma kuma gidajen Man mallakin gwamnati irinsu:
NNPC, TOTAL da sauransu, zasuna sayarwa alumma akan farashi Mai rahusa. Idan
har gwamnati ta sakarwa 'yan kasuwar Mara suka shigo da Man Barkatai kuma ta
sanya ido sosai akan 'yan kasuwar akan yadda suke gudanar da hada-hadarsu. To
Insha Allahu Man zai zama tamkar "Ledar Pure Water akan titunan mu".
Kaga kenan 'yan kasuwar Mai zasu karu, kuma duk abinda yayi yawa to karshensa
zai fadi ne warwas .
Misalin abinda yake faru yanzu a kasuwannin Man Fetur
din ta duniya. . Hasalima Idan mukayi La'akari da Abinda ya faru ga Kamfanonin
wayar Salula a Nigeria.
A baya Layin wayar Salula guda daya taka wato "MTEL". wadda mallakin
gwamnati ne.
Wednesday, 11 May 2016
Masari Ya Bude Ofishin Bankin Tallafawa Masana'antu [BOI] Rashen Jahar Katsina
Gwamna Aminu Bello Masari yayi kira ga al'ummar Jihar Katsina, musamman masu kanana, matsakaita da kuma manyan Masana'antu da suyi kokarin cin gajiyar alfanun da Bankin tallafawa wa Masana'antu na Kasa (Bank of Industry) yake samarwa.
Gwamnan yayi wannan jawabi ne a yayin bukin bude ofishin reshe na wannan Banki da na nan Katsina.
Gwamna Masari ya kara da cewa Gwamnatin Jiha ce tayi Uwa kuma tayi Makarbiya wajen kawowa da kuma samar wa wannan Banki matsugunni domin al'ummar wannan Jiha su amfana ta bangaren habakawa tare da kafa sababbin Masana'antu.
TA INA TALAKA KE ANFANA DA GWAMNATI MUSAMMAN MA WANDA BAIYI KARATUN ZAMANI BA? Malam Mansur
Idan mukayi la'akari da irin yadda
kasar nan ke wofantar da al'amarin daya shafi walwala da jindadin talakawanta
musamman ma wadanda basu samu damar yin karatun zamani ba. Abin, abin a tausaya
ne a kuma Waiwayo domin tallafama wannan bangare dan koba komai dai suma
yan'kasa ne, suna da hakkoki akan gwamnatocin kananan hukumomi, jihohi da kuma
tarayya.
Akan karbi haraji daga hannun su amma su babu ta
inda suke amfana Ko shakka babu Waiwayo abinda ya shafi ilimi da makomar talaka
mara galihu abune daya zama wajibi akan gwamnatoci na APC su duba wannan lamari
da idon basira da kuma hangen nesa, domin wadannan mutane suna bada gudunmowa
da dama da suka hada da: samar da abinci ga al'umma, samar da kudaden shiga ga
gwamnatoci, da kuma samar da tsaro a iyakokin kasa, gunduma ko shiyya.
Sunday, 8 May 2016
KORAFI AKAN DIREBOBIN TIFA Daga Abdulmumin Sabo
koke zuwaga Dan majalissa mai wakiltar Daura tare da hukumar kare hadura ta karamar hukumar Daura.
Kamar yadda kowa yasani ne Titin da ya tashi daga Daura zuwa Katsina titine da akoda yaushe yake dauke da ababen hawa a dalilin cunkushe shi da akayi da makarantun da suka hada da GDSS Daura, GGSS Daura, GPSS Daura, General Hospital Daura, Daura main market, school of health technology Daura, Daura local government secretariat, Himma nursery and primary school Daura, quality assurance Daura zonal office duka wannan dana zano wurare ne na hada hadar jama'a uwa uba gata hanya ce ta zuwa state head quarter wato garin Katsina. Haka kuma kashi tamanin da biyar na Kasa ko yashi da yan tifa ke daukowa su kawo cikin garin Daura ta wannan hanya ne suke kawo shi.
Don haka nake kira ga Dan majalissar jiha mai wakiltar Daura hadi da hukumar kare hadura shiyyar Daura duk da jama'ar Daura da dama na yaba kokarinsa to anan ma yakamata ya dauki matakin kawo karshen wata matsala dake damun duk wani ma'abocin bin wannan titi (Daura to Katsina) wato matsalar nan ta yan Tifa masu debo yashi ko Kasa tinya batareda sun rufe yashi ko kasar da suka dauko ba wanda hakan yana matukar takurawa duk wani mai binsu abaya akan babur ko keke har masu motoci abin na shafarsu don haka Yakamata gwamnati ta lura da wannan matsala ta tuntubi kungiyar yan tifa don nemo mafita bawai sai ranar da hakan ya haddasa hatsari ba Allah ya kiyaye sannan a fara laluben hanyar magance wannan matsala.
Ina bada shawara da a umarci yan tifa da su rika rufe yashi ko kasar da suka daukowa da tamfal ko su rika yayyafa mata ruwa wannan zai rage matuka yashi ko Kasa da iska ke daukowa zuwa idanun masu abun hawa. Tuni a wasu jihohi ko birane ake amfani da wannan doka. Da fatan Dan majalisa Hon. Nasir Yahaya Daura tare da hukumar kare hatsura ta shiyyar Daura zasu duba wannan koke ameen.
Kungiyar Marubuta Katsina Ta Taka Rawa Wajen Sasunta Rikici Tsakanin Sani Hamza da Dan Majalisa Mai Wakiltar Funtua
Bismillahi!
Salamu Alaikum., 'Danmajalissar jiha, (Katsina) mai wakiltar karamar hukumar Funtua.
.
Tun da na ga fos din Malam Bashir Yahuza Malumfashi, wanda ya kattaba cewar an kama Sani Funtua ta dalilin rubutun da yake yi a kan d'anmajalissar karamar hukumarsu, musamman ma wata budaddiyar wasika da shi Hamzan ya rubutu zuwa ga Abubakar Total din, nan take na kira zababben shugaban Kungiyar Marubuta jihar Katsina (KMK) domin ganin abin ya shafi rubutu da marubuta ne, a nan yake shaida mini ba shi gari. Jin haka ya sa na tuntubi Jami'in Hulda Da Jama'a, wanda shi ma ba mazaunin cikin garin na Katsina ba ne, don haka sai na tafi ga Sakataren na KMK, inda na yi sa'ar samunsa, na kuma shaida mishi halin da ake ciki game da kes din na su Sani. Nan take ya fara bibiyar kadin lamarin cikin zama da kazar-kazar. Bayan shi sai na sake tuntubar Ma'aji da kuma Mataimakiyar Shugaba, su ma duk suka bazama don ganin lalubo bakin zaren. Kafin a jima dai duk zababbun shugabannin KMK muka dukufa ta ko'ina wajen sasanta wannan rikici, mun tuntubi abokan Sani don jin takamaiman abinda ke faruwa,
Salamu Alaikum., 'Danmajalissar jiha, (Katsina) mai wakiltar karamar hukumar Funtua.
.
Tun da na ga fos din Malam Bashir Yahuza Malumfashi, wanda ya kattaba cewar an kama Sani Funtua ta dalilin rubutun da yake yi a kan d'anmajalissar karamar hukumarsu, musamman ma wata budaddiyar wasika da shi Hamzan ya rubutu zuwa ga Abubakar Total din, nan take na kira zababben shugaban Kungiyar Marubuta jihar Katsina (KMK) domin ganin abin ya shafi rubutu da marubuta ne, a nan yake shaida mini ba shi gari. Jin haka ya sa na tuntubi Jami'in Hulda Da Jama'a, wanda shi ma ba mazaunin cikin garin na Katsina ba ne, don haka sai na tafi ga Sakataren na KMK, inda na yi sa'ar samunsa, na kuma shaida mishi halin da ake ciki game da kes din na su Sani. Nan take ya fara bibiyar kadin lamarin cikin zama da kazar-kazar. Bayan shi sai na sake tuntubar Ma'aji da kuma Mataimakiyar Shugaba, su ma duk suka bazama don ganin lalubo bakin zaren. Kafin a jima dai duk zababbun shugabannin KMK muka dukufa ta ko'ina wajen sasanta wannan rikici, mun tuntubi abokan Sani don jin takamaiman abinda ke faruwa,
Friday, 6 May 2016
TARON TATTALIN ARZIKIN A JAHAR KATSINA; SAKO DAGA DESOMF
Wannan dandali na Daura emirate social media forum
(DESOMF), muke so muyi amfani da wannan damar domin kira ga al'ummar jahar
katsina musamman matasa maza da mata, da mu kasance masu nuna halayan kirki a
yayin wannan muhimmin taron kamar yadda a kasan katsinawa dasu.
Bayan haka kira ga al'ummar jahar katsina da mu
kauce ma duk wani abu da zai zubar da mutumcin jaharmu da shuwagabaninmu.
Sannan munaso al'ummar jahar katsina su sani cewar wannan taro ba na siyasa
bane, taro ne na duk wani mai kishin ko mai son cigaban jahar katsina ne taro
ne na habaka tattalin arzikin jahar katsina.
Thursday, 5 May 2016
Hon.Abu Total"Na Fi Karfin Ka Dan Ubanka Kuma Sai Na Wulakanta Ka" Zuwa Sani
Wannan ya faru tsakanin Hon. Abu Total da Sani.
Sani & Total.
Abubakar Total
Sani & Total.
Abubakar Total
"To ina nan ina jiranka in ba zan
karyaka ba kar Allah ya ba ni
abinda nike nema Duniya da
Lahira! Na fi karfinka don Ubanka (Lallai sak ta yi aiki) kuma na fi
karfin me sa ka ka yi min iskanci.
Duk Uban da za ka gaya wa, ka
gaya mishi. Idan ban sa an
wulakanta ka ba Allah ya tsine
min albarka! Idan akwai bashi tsakanina da kai, ko Ubanka yana
bi na bashi, to don Ubanka ku je
Kotu ku yi karata ku zo ku amshi
kudin ku. Amma na rantse da
girman Ubangiji daga rana me
kama da ta yau idan na kara ganin rubutunka a Facebook
(yanzu ma ka fara gani, tunda
karyaka ba kar Allah ya ba ni
abinda nike nema Duniya da
Lahira! Na fi karfinka don Ubanka (Lallai sak ta yi aiki) kuma na fi
karfin me sa ka ka yi min iskanci.
Duk Uban da za ka gaya wa, ka
gaya mishi. Idan ban sa an
wulakanta ka ba Allah ya tsine
min albarka! Idan akwai bashi tsakanina da kai, ko Ubanka yana
bi na bashi, to don Ubanka ku je
Kotu ku yi karata ku zo ku amshi
kudin ku. Amma na rantse da
girman Ubangiji daga rana me
kama da ta yau idan na kara ganin rubutunka a Facebook
(yanzu ma ka fara gani, tunda
Wednesday, 4 May 2016
Ga Budaddiyar Wasika Da Sani Hamza Ya Rubuta Ma Hon. Abubakar Total
BUDADDIYAR WASIKA Zuwa ga Danmajisalar karamar hukumar Funtua, Hon Abubakar Muhammad (Total). ©Sani Hamza Funtua.
29-04-206… 4:00pm.
Zan fara rubuta wannan wasikar da gaisuwa a gareka, ya aikin ofis da kuma na zagaye-zagaye? Allah ya tabbatar maka da alkairin abinda ke cikin zuciyarka Amin.
Kai tsaye ba tare da bata wani lokaci ba, zan je ga dalilan da yasa na rubuta maka wannan wasikar, da kuma son kasancewarta budaddiya wacce kowa zai iya karantawa. A ‘yan watannin baya, abubuwa sun faru tsakaninka da wani a mazabarka, inda har karshe dai ka aika rundunar ‘yan sanda don su kama maka shi.
Nayi mamakin yadda shugaba mai iko kamarka, kuma a matsayin mai majalisar mahukunta ta jaha zai yanke wannan danyen hukuncin, bayan ka san cewa muna rayuwane a karkashin demokaradiya, wacce kundin tsarinta ya bawa ko wane dan kasa daman a ya fadi albarkacin bakinshi matukar bai sabawa shari’a ba, koda kuwa suka ce ga gwamnati.
Sani Hamza Funtua kamar yadda nasan baka mance sunanshi ba, matashine da ke tasowa a turba ta Rubutu, yanzu zai zauna yanzu zai rubutu akan wannan zaman, sannan a cikin rubutun shi baka taba samunshi da amfani da kalmomi masu nuna jin tsoron abinda yake rubutawa. Idan har ka fahimci hakan, tabbas dole kai da akai rubutun kanka kaji tsoron abinda ya rubuta. Sai dai har yau har gobe, bai taba yin rubutun da zaisa hukuma ta kamashi har ace za’a daure shi ba.
Dan Majilissar Funtua {Total} Yasa Yan Sanda Sun Kama Wani Ma Rubuci A Katsina

Wani Dan Majalissar dokoki na jahar Katsina mai
wakiltar Funtua yasa yan sanda sunyi awon gaba da wani marubuci a farfajiyar
Facebook mai suna Sani Hamza Funtuwa saboda wata budaddiyar wasika daya
rubutama dan Majalissar.
Dan haka muna kira ga hukumar yan sanda datasan
cewa ba an kirkireta bane danta kare muradun masu madafun iko. Ba zaluntar
mutane akace tayi ba, a'a, kare hakkinsu akace
tayi, irin hakkin Sani Hamza Funtua da aka shiga.
Muna kira ga shuwagabannin Majalissar Dokoki na
jaha dasu kira abokin aikinsu da yashiga hankalinshi! Yaza'ayi an zabeshi
yakare hakkin mutane kuma yazama yana samasu takunkumi? Idan wanda aka zaba
yayi dokoki dan Jin dadin al'umma, kuma yazama shine kan gaba akan karya doka?
Muna kira da aja mashi hankali kuma yasa asaki Sani Hamza Funtua.
KAMFANIN WUTA NA #PHCN, KUDIN WUTA SUKE KARBA KO KUDIN HAYAN GIDAJE ? Malam Mansur Halilu
Inhar kudin da kamfanin na PHCN yake karba na wutar
lantarki ne to ina wutar lantarkin? Inkuma kudin da suke karba na hayan
gidajenmu ne, to sai sugayamana cewar ba #NEPA kadai aka sayar musu ba harda
gidajen talakawa aka sayar musu shiyasa sukebi duk karshen wata suna karban
kudin haya Ba'a bayan haka kuma jami'an ita wannan hukuma ta PHCN a duk lokacin
da suka zo gida sukan buge da yin hira da matan mutane a maimakon aikin daya
kawo su, wannan dabi'a na taimakawa matuka ga wadannan jami'ai masu neman neman
matan mutane, bayan wannan matsala kuma ta magana da matan mutane akwai
matsalar "karbar na goro" misali za'a kawo maka "bill" a
tsakiyar wata a kuma baka wa'adin sati daya kachal!
Gwamna Masari Ya Kai Ziyarar Bazata A Asibitin Garin Daura

A kokarin da yake na tabbatar da ana aiwatar da ayyukan da Gwamnati ta bayar yadda ya kamata, a jiya litinin 2/05/2016, Gwamna Aminu
A yayin wannan ziyara, Gwamna ya zagaya duka sassan asibitin domin gane ma idon shi yadda aikin gyara da kuma fadada asibitin ke tafiya. Bayan nuna gamsuwa da nagartar aikin, ya kuma ja hankalin masu gudanar da aikin da su tabbatar da sun kammala shi cikin lokacin da aka kayyade.
Gwamnan ya kuma ziyarci marasa lafiya da suke kwance a asibitin tare da yi masu addu'ar Allah Ya basu lafiya.
Tuesday, 3 May 2016
Shin! Kuri'ar Ka Yan'cin Ka? by Comr Aliyu Mamman Sarki

A duk sadda da na tuna lokacin da nabi layi, na anshi takardar Kada kuri'a, na matsa wajen akwatin zabe na kada kuri'a ta, nikanji wani takaici yazo mani in kuma ji na kagara a Kara kada gangar siyasa.
Mafi akasarin wadanda muka zaba domin su wakilce mu a majalissun tarayya, to agaskia munyi zaben tumun dare. Domin suna wakiltar kansu ne kawai. Sun zame mana tamkar almajiran birni, babu kyuya babu biyan bukata.
Kullun sai kaji sunce suna Abuja, amma bama ganinin su suna fafutukar nemar mana hakkin mu a Zauren Majalissa. Sun tafi kawai yawon bude idanu dan kuwa duk badakalar da akeyi a zauren majalissa su idone kawai nasu.
Monday, 2 May 2016
Rahotun Tattaunawa Ta Tsakanin Leadership Newspaper Da Katsina Post Ta Buga Ba Gaskiya Bane.-Zango
Jaridar leadership
tasa Kanun labarin hirar da su kayi da mai ba Gwamna Masari shawara akan
harkokin siyasa kamar haka :"Jam'iyyar PDP bata da tacewa a shekara sha
shidar da ta kwashe tana mulkin Jihar Katsina"
Kanun
labarin da katsina post ta fitar dangane da wannan hira kamar yadda ta chanza
kuma ta wallafa a bangon Jaridar ta da ta wallafa a 1:5:2016 tace " mai ba
Gwamna Masari shawara ya hakikance akan cewa Marigayi Yar'adua da Shema basu
tsinana komai ba a jihar katsina"
Labarai
suna daga cikin manyan hajoji masu daraja a wannan duniya tamu. Yadda masu
karatu suke sha'awar karanta labari da yadda zasu fahimci labari da kuma yadda
sukanyi tsokaci dangane da labari mafi akasari ya danganta ga yadda mai bada
labari ya tsara kanun labarinsa. Wannan yasa da yawa daga wasu masu karanta
labari a wasu lokuttan sukan dogara kaco kam aKan kanun labari batare da
karanta gangan jikin labari ba.
Tasirin
samun labarai ta kafar yanar gizo musamman ta fejikan sada zumunta wato
Facebook yana akan sahun gaba a wannan zamanin a wurin al'umma ganin yadda yake
da saukin kawo labarai yadawa har ma da tofa albarkacin baki wannan ne ya
haifar da matsalar yada jita jita idan har kafar yada labari ba sahihiya bace
ko kuma yadda kafar data yada labarin batayi taka tsantsan ba wajen fadin
sahihin zance dangane da labarin data bayar.
Subscribe to:
Posts (Atom)