Idan mukayi la'akari da irin yadda
kasar nan ke wofantar da al'amarin daya shafi walwala da jindadin talakawanta
musamman ma wadanda basu samu damar yin karatun zamani ba. Abin, abin a tausaya
ne a kuma Waiwayo domin tallafama wannan bangare dan koba komai dai suma
yan'kasa ne, suna da hakkoki akan gwamnatocin kananan hukumomi, jihohi da kuma
tarayya.
Akan karbi haraji daga hannun su amma su babu ta
inda suke amfana Ko shakka babu Waiwayo abinda ya shafi ilimi da makomar talaka
mara galihu abune daya zama wajibi akan gwamnatoci na APC su duba wannan lamari
da idon basira da kuma hangen nesa, domin wadannan mutane suna bada gudunmowa
da dama da suka hada da: samar da abinci ga al'umma, samar da kudaden shiga ga
gwamnatoci, da kuma samar da tsaro a iyakokin kasa, gunduma ko shiyya.
Amma abin mamaki duk da wannan irin namijin kokari
da suke yi babu wani tsari daga cikin tsare-tsaren gwamnatoci da akeyi domin su
ko ake shiryawa domin su saidai kawai ayita fada a baki za'ayi ko kuwa anyi
amma a zahiri babu wani abu da mazauna yankunan karkara ke amfana dashi daga
bangaren gwamnatoci.
Amma da ance lokacin zabe yayi to sannan ne zasu
cigaba da ganin bakin fuska iri-iri dukkan su kuma da maganganu da alkawurra
iri-iri badai komai ba sai don asamu kuri'asu Meyasa babu wani tanadi na
musamman da zai tallafama wadanda basuyi karatun zamani ba?
Duk wani tsari na gwamnatoci zaka iske an
kirkireshi ne kawai domin wadanda sukayi karatun zamani, Anan ko shakka babu
ina zargin gwamnatoci da hana wadanda basu samu damar yin karatun zamani ba
damar daya kamata su samu a matsayinsu na yan'kasa bayan wasun su nada matukar
fasaha ta fannoni da dama Mutanen karkara musamman wadanda basu samu damar yin
karatun zamani ba ba'a daukar su da muhimmanci ta fuskar ilimin su, tsaron su
da kuma makomar su a rayuwa.ko shakka babu cigaba da tafiyar da al'umma a haka
bazai haifar da da' mai ido ba.
WAI SHIN TA INA TALAKA KE AMFANA DA GWAMNATOCI
MUSAMMAN MA MAZAUNA YANKUNAN KARKARA WADANDA BASU SAMU DAMAR YIN KARATUN ZAMANI
BA?
No comments:
Post a Comment