Gwamna Aminu Bello Masari ya jaddada kudurin wannan Gwamnati na kyautata rayuwar mata tare da daga martabarsu a wannan Jiha.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a wani taro da wasu kungiyoyin mata suka shirya domin karrama shi tare da Mataimakin shi Alhaji Mannir Yakubu.
Ya kara da cewa tun da wannan Gwamnati tazo, ta maida hankali ne wajen warware matsalolin da ta gada daga Gwamnatocin da suka gabata. Inda a matakin Gwamnatin Tarayya aka ciwo kan rikicin Boko Haram a nan Jiha kuma aka ciwo kan matsalar barayin shanu.
Gwamna Masari ya kuma yi godiya ga wadannan kungiyoyi tare da tabbatar masu da cewa da yardar Allah wannan Gwamnati ba za ta kunyata al'ummar Jihar nan ba musamman wadanda suka zabe ta.
Babban Bako Mai jawabi, Malam Bashir Ruwan Godiya, yayi dogon jawabi ne a kan irin gudummuwoyin da mata suka bada tsawon lokaci wajen gina al'umma.
Tun farko a nata jawabin shugabar gamammiyar kungiyar mata domin kawo ci gaba, Hajiya Mariya Abdullahi ta jaddada godiyar mata ne a kan yadda Gwamnatin Jihar Katsina a karkashin jagorancin Alhaji Aminu Bello Masari ta bada kashi Sittin bisa Dari na tallafin bashin sana'o'i ga mata.
A nata jawabin, Dokta Halima Adamu ta yaba wa Maigirma Gwamna ne a kan nasarorin da yake ta samu tun daga lokacin da yake aikin Gwamnati har ya zuwa yau tare da yi mashi addu'ar Allah Ya ci gaba da tsare shi cikin aminci da jagoranci.
Kwamishiniyar Ma'aikatar harkokin mata ta jiha, Hajiya Badiyya Hassan Mashi, tace mata basu taba samun damar shiga cikin harkokin Gwamnati ba irin yanzu, domin kuwa Gwamna Aminu Bello Masari ya nada mata har guda Ukku a matsayin Kwamishinoni da kuma Mai bada Shawara guda daya. Haka nan kuma akwai masu taimaka wa Gwamnan suma su Biyar.
Wannan, a cewar ta, yana daya daga cikin dalilan da yasa wadannan kungiyoyi suka karrama Gwamnan.
Ta kuma tabbatar wa al'umma, musamman 'yan uwan su mata cewa ba zasu bada kunya ba in shaa Allah.
No comments:
Post a Comment