MATASAN KATSINA MASU SON CANJI
(KATSINA YOUTHS FOR SUSTAINABLE
CHANGE) (KYSC).
MARTANI KAN BAYANIN DA DANDALIN APC
BIYAYYA FORUM, TA FITAR A KATSINA RANAR 22 GA DISAMBA, 2018.
“ … Darakta-Janar na SMEDAN da Manajin
Darktan FMB ne kawai suka ba da tallafin karfafa gwiwa don samun nasarar
tafiyar sake zaben SHUGABA MUHAMMADU BUHARI a 2019…”
A iya saninmu wannan ikirari da ke
sama, wanda aka jingina shi ga Mai girma Gwamnan jihar Katsina da Ciyaman na
jam’iyyar APC a jihar Katsina karya ne, kuma kwata-kwata ba gaskiya ba ne!
Manajin-Daraktan Hukumar tashoshin
jiragen ruwa (NPA), HAJIYA. HADIZA BALA USMAN ta hanyar ayyukan taimakon jama’a
da Hukumar NPA take yi, tare da hadin gwiwar kungiyar da muka ambata a sama,
KYSC, sun ba da tallafi mafi tasiri a jihar Katsina.
HAJ. HADIZA BALA USMAN ta ba da
gudummawa da tallafi ga raunana da marasa galihu a al’ummarmu a dukkanin
Kananan Hukumomin jihar Katsina. Wadannnan ayyukan sun kama daga samar da
kujeri a makarantun firamare, samar da fitilu masu amfani da hasken rana da
barguna 280 ga makarantun almajirai, samar da kekunan dinki, injin markade ga
mata da famfunan injinan ban ruwa ga manoman karkara kamar yadda yake bayyane a
kasa.
Hajiya Hadiza ta ba da gudummawa fiye
da kowane dan siyasar da aka ba shi mukami a tarihin jihar Katsina, a matakin
jiha ne ko na Tarayya wajen ba da tallafi da gudummawa ga raunana a al’ummarmu.
GA JERIN WASU AYYUKAN DA HAJIYA HADIZA
BALA USMAN TA YI A JIHAR KATSINA KAMAR HAKA:
1. An ba da kujeri 4,000 ga makarantar
firamare ta Musawa.
2. An gina azuzuwan karatu a Musawa da
Jikamshi.
3. An rarrabar da injin makarde guda
40 a Karamar Hukumar Musawa.
4. An ba da N25,000.00 kowanne ga
matasa 50 a Karamar Hukuma.
5. An rarraba injinan famfunan ban
ruwa guda 40 a Karamar Hukumar Musawa.
6. An rarraba kekunan dinki guda 50 ga
mata a Karamar Hukumar Kafur.
7. An rarraba injinan ban ruwa guda 50
a Karamar Hukumar Dandume.
8. An rarraba injinan ban ruwa guda 50
da injinan markade guda 50 a Karamar Hukumar Katsina.
9. An rarraba injinan markade da na
dinki guda 70 a Karamar Hukumar Katsina.
10. An rarraba injinan ban ruwa guda
50 na Karamar Hukumar Sandamu.
11. An rarraba kekunan dinki da injin
markade 10 a Karamar Hukumar Daura.
12. An rarraba kekunan dinki guda 50 a
Karamar Hukumar Malumfashi.
13. An rarraba kekunan dinki guda 50
da injinan markade guda 50 a Karamar Hukumar Ingawa.
14. An bai wa mata 200, mata 20 a
shiyyar Funtua (Kananan Hukumomi 11) kaji masu yin kwai, wanda aka yi a Funtua.
15. An rarraba barguna 4,000 ga
makarantun Almajirai a duk fadin Kananan Hukumomin jihar Katsina, inda aka
kaddamar a Karamar Hukumar Daura.
16. An kakkafa fitilu masu amfani da
hasken rana guda 282 ga makarantun Almajirai 282 a duk fadin Kananan Hukumomin
jihar Katsina guda 34.
17. An ba da motar Bas ga kungiyar
FUTURE ASSURED Organization wacce Haj. Ambaru Wali take shugabanta.
Dukkan wadannan ayyukan taimakon
jama’a a sarari suke kuma za a iya tabbatar da su, da ma an ce GASKIYA BA TA
NEMAN ADO.
A karshe, HAJIYA HADIZA BALA USMAN,
wacce ta fito daga gidan da aka san su da neman tabbatar da adalci da daidaito
a al’umma, za ta ci gaba da jajircewa wajen taimakon matalauta a al’ummarmu duk
da irin wannan farfaganda na karya, wanda ba zai rage ta da komai ba saboda
wadanda suka ci gajiyar ayyukanta za su ci gaba da yaba mata da godiya gare ta
a yunkurinta na tabbatar da sahihin canji mai dorewa a jihar Katsina da kasa
Nijeriya gabaki daya.
Daga ALH. SALLAU ARAWA
D.G. 1 KYSC KATSINA
08032515386
No comments:
Post a Comment