Thursday, 19 May 2016

Kungiyoyin Matasa a Malumfashi Sun Nuna Goyon Bayan Cire Tallafin Man Fetur



A yau alhamis ne 19/5/2016 gamayyar kungiyoyin matasa karkashin jagorancin kungiyar malumfashi Youth development association suka gudanar da nasu gangamin nuna goyon baya dangane da cire tallafin Man fetur da gwamnatin tarayya tayi wanda a dalilin kalubalantar hakan da kungiyar kwadago ta kasa ta keyi yasa ta aiwatarwa da tata zanga zanga tare da shiga yajin aikin sai baba ta gani wanda bisa alamu kungiyar kwadagon bata samu irin goyon bayan da ta saba samu a baya ba.

A tabakin shugaban kungiyar Malumfashi Youth Development Association kuma daya daga cikin manyan jadanen wannan zanga zanga Hon. Ahmad Nasir Lara yayi tsokaci da cewa ita wannan gangami ne don nuna goyon bayan su da matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na cire tallafin Man fetur dalilin su kuma shine tunda Sune suka zabi wannan gwamnati a dalilin sun aminta da ita saboda haka wajibin sune su bata cikakken goyon bayan da take bukata ga duk wata manufar ta mai kyau ga al'umma don ta samu damar yin nasarar kawo Canji da suke bukata.


Mun fahimci tallafi na makudan kudaden mu da gwamnati take dauka tana biyan yan kasuwar harkar man fetur baya da wani amfani ga talakan kasar nan illa kawai wasu yan tsiraru da basu wuce kashi uku cikin dari ba na adadin yan kasa wanda kuma basa tausayin talaka ne kadai ke amfana dashi. Dangane da batun kungiyar kwadago kuma ya nuna cewar sufa dama tuni suka dawo daga rakiyarta musamman shugabacin 2011-2016 saboda a cewarsa babu gaskiya a al'amarinsu wasu ne ke amfani da ku kungiyar don cimma wata manufa tasu saboda haka ne yasa gamayyar kungiyoyin al'ummar karamar hukumar Malumfashi basa tareda wannan yajin aikin da kungiyar kwadagon ta shiga hasali ma a ra'ayinsu rusa ta shi yafi fa'ida ga talakan Nigeria saboda a cewarsa a duk wata kungiyar na tara makudan kudaden haraji datake ansar a hannun ma'aikata amma ba wanda yasan me ake da wannan kudaden haraji.

Idan akayi la'akari da tarihin wannan karamar hukuma ta malumfashi yadda tayi fice wajen goyon bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari a siyasa nice daukar wannan matsaya ta goyon bayan matakin da gwamnatin sa ta dauka ba abin mamaki bane.

No comments:

Post a Comment