Gwamna Aminu Bello Masari yayi kira ga Malamai da sauran al'umma da mu kara jajircewa wajen yi wa kasar mu da ma duniya baki daya addu'a domin samun dawwamammen zaman lafiya da karuwar arziki.
Gwamnan yayi wannan kira ne wajen rufe taron Maulidin Sheikh Ibrahim Inyass na wannan shekara, wanda ya gudana a filin wasa na Muhammadu Dikko dake nan Katsina.
Gwamnan wanda ya sami rakiyar manyan jami'an Gwamnati, yayi addu'ar Allah Ya maida kowa gidan shi lafiya.
No comments:
Post a Comment