Friday, 23 November 2018

Karta Kai Dozen Fatalwa Ce A Ruhin Dan Takarar Gwamna A Jamiyyar Apga 2015- Nura Tina


Mafi akasarin alumma sukan yi mafarkin abinda ke ran su, Maana suna fadin abinda suka fi tsana a rayuwar su fiye da komai.

A shekara 2015 Hon.Umar Tata ya fito neman kujerar gwamnan jahar katsina a PDP daga Nan ya koma APGA Mai alamar Zakara, Umar Tata yayi iyakar kokarin shi ya kuma bi dukkan hanyoyi domin ganin ya samu nasarar wannan Zabe, Amma sai gashi yazo na karshe ,Maana shine mafi karancin kuru'un. engr. musa tashuni da sen.yakubu Garba Lado danmarke suna gaban shi a Kuri'u.
Uncle Umar Tata idan mukai kididdiga zamu ga cewa yawan Kuri'un da ya samu a jahar katsina baya wuce ace kowa ne akwatin zabe ya samu kuri'uTara (9)
Idan muka dauki kaf Kuri'un da uncle Umar Tata Ya Samu kaf jahar katsina sune 42,302 Wanda muna da Rumfunan zabe guda 4,902. Mu kaddara cewa kaf akwatinan zaben dake gare mu na jahar katsina guda 4,902 kowa ya zabi Tata To Kuri'un basu  wuce ya samu Kuri'u Tara Tara (9)(9) kowane akwati.
Masu iya magana cewa "mi jiya Tayi bare yau" a baya Hon. Umar Tata da kanshi yake nema mawa Kudi, A Wancen lokacin da kudin shi jibge a Jika baya jiran wani attajiri ya bashi.
2015 Yana sabon fuska ga alumma ,baa San halin shi ba, baa San waye shi ba, alumma na ganin shi matsayin uba, suna hangen cewa yazo ya taimake su, Kuma ba kudi ko mulki yake nema ba. Alumma na ganin cewa da kanshi yazo ba aiko shi akayi ba, Kuma ba yaron wani bane, shine Mai gidan kan shi da kan shi yazo.
A Wancen lokacin Alummar jahar katsina basu da tabbacin cewa gwamnati ko wani attajiri ya bashi kudin yazo neman kuri'a.
Lokacin bai yi fada da wasu yaran shi ba, bai fada da wasu Jama'ar gari ba, bai je yayi magana ya chanza ba,(A Kori yunwa).
A 2015 kaf kowa na ganin shi a matsayin wani tauraro Yana tare da dukkan abinda za yayi amfani dashi wajan kawo Kuri'u Amma ya kasa samun kuri'a AKALLA 12 kowa ce rumfa .sai yanzu??
Gare ku APC nasan kunsan dukkan abinda yake ciki da Kallon kallon da kuke mashi na biri da ayaba, Amma Yana da kyau mu karu da shawarar juna ta hanyar yin amfani da kalaman Malam bahaushe na cewa "dukkan Wanda yace zan baka RIGA to dubi ta wuyan shi" Hon. Tata ko Rumfar da  yake zabe bai taba ci ba balantana yaci rumfar waje.
Gare ku yayan PDP nasan wannan maganar da Uncle Tata yayi magana ce Mai ban dariya magana ce da kuka dade Kuna Jin irin ta tun daga zaben mashi/dutsi na cewa zaya bada naira milyan goma goma ga dukkan inda suka kawo ward din su da Kuma ya ga lokaci ya kure sai yaje ya jawo Mana fada.
Kada in jaku da nisa yau Umar tata tsauri ba shike ne mama kanshi kuri'a ba gov.aminu Bello masari Yake nema mawa idan har a chan baya ya kasa samun kuri'a AKALLA sama da guda goma (10) kowace rumfa, yau Ina bukatar ganin yadda zayace kada takai dozin har masu biye da Dan Tata suji dadin maganar suna rantsuwar cewa tata na iya haka.
To nidai nace duk tatsuniya ce......

Comr.Nura Adam Kankara Tina
DG campaign buhari/masari MOST GO organization

No comments:

Post a Comment