“Babu abinda nafi kauna a Rayuwata ayi min Kyauta [Gift] dashi kamar Turare. Na fara Madigo bayan na shaki kamshin turaren da Zara ta bani a matsayin kyauta dashi, daga wannan ranar duk abinda take so inayin shi ba tare da ko Musu ba”
***** ***** **** ***** ***** *****
Kamar misalin kwana biyu da yin rubutun ci gaban labarin Karshen Madigo kashi na Goma sha Hudu, ina cikin dakina ina aikin Littafin wata baiwar Allah data kawomin, wayata ta dauki ruri da neman agajin gaggawa,jin wayar ta isheni nima yasa nayi hanzarin dauka tare da karawa a kunnena.
“Salamu Alaikum” Na ce cikin kaguwa d agama wayar don ci gaba da aikin da nikeyi.
Muryar mace ta amsa sallamar, muka gaisa cikin girmamawa, a nan ne ta fara tambayata.
“Dan Allah ko kaine Sani Hamza Funtua marubucin Littafin Karshen Madigo?”
Na amsa da “Hakkun nine, ina fatan dai lafiya”
Tace “Lafiya lau, daman a kiraka ne in gaishe ka kuma in jinjina maka akan wannan namijin kokarin da kakeyi ba tare da nuna tsoro ko fargaba ba, duk da cewa naga kace wata Hajiya Babba ta kiraka tare da yi maka barazana. Nayi tunanin kiran nata zaisa ka dakata da labarin kamar yadda ka rubuta, sai kuma naga kaci gaba, hakan yasa zuciyata ta narke da al’amarinka.”
Na nisa kana nace “Aiko na gode kwarai ‘yar uwa”
Tace “Kasan nima na taba shiga irin wannan rayuwa, koma dai ince har yanzu ina kafa daya ciki—kafa daya waje.”
A nan ne na gyara zama da tambayarta.
“Kin taba shiga wannan rayuwar kamar ya ke nan? Kina nufin kema kinyi rayuwa ta Yan Lesbian?”
Ta amsa da “Kwarai kuwa nayi. Na kiraka ne musamman dan tattaunawa dakai, wata kila a cikin labarin nawa ka samu wani abun amfani da zaka kara sawa a cikin labarinka, ko ba komai na sanarwa duniya gaskiya koni wacece a baya, yadda na shiga wannan harka da kuma kiran da zanyiwa ‘yan uwana mata.”
Nace “Hakane wannan. Gaskiya kinyi namijin kokari tabbas, amma ya sunanki da kuma garinku?”
Ta ce “Sunana Fatima Sadik Al - Ameen. Ni haifaffar garin Kano ce.”
Dai dai wannan lokacin ne aka aiko ana sallama dani a kofar gida, na sanar ma Fatima ta amince da zamuyi Magana anjima.
Tsawan yinin wannan ranar ban samu zama ba, Fatima ta kirani kusan sau uku duka bamu samu damar yin Magana ba. A lokacin na yanke shawarar sanarwa dan Uwa Bashir Yahuza Malunfashi, watakil hakan ne zai zama dai-dai ga burinta Fatima na duniya ta san labarinta.
Na kira wayar Malam Bashir, muka tattauna akan maganar, ya aikomin da lamabr wakiliyarsu dake a nan Kano. Sai dai kafin nayi yunkurin wani abu kaddara tasa aka zo bayan na taso daga neman ilimin Addini aka tafi dani Ofishin Area Commander a nan Funtua. Bayan kwana da Yini daya na fito, washe gari sai ga kiran Fatima.
A nan ne t ace in tsaya in saurari Labarinta duk da taga cewa abubuwa na faruwa da suke hana ni amfani da wayata. Farkon maganar da na yi mata itace:
“Kin amince zaki sanarwa duniya labarin ki?”
Ta amsa da “Eh na amince”
Nace “Koda kuwa a Jarida ne ko gidan Radiyo?”
Tace “Eh zan iya, amma ni bana so a fito da sunan unguwarmu ko ainihin sunana, don kada na kusa dani su gujeni dukda cewa a yanzu banayi”
Nace da ita “Kada ki damu, hakan bazata faru ba, hatta hotonki ma ba zasu dora ba, suna da masu zane wadan dazasu zana dai-dai da labarinki, sannan za’a oya boye sunanki. Babban abinda suke so dai shine su samu labarin daga Original Source, ta yadda tabbas kece kika yi niyyar Comfessing”
Fatima ta amince da hakan, a nan ni kuma nayi mata alkawarin washe gari Wakiliayar Jaridar Aminiya zata sameta har gida ko kuma inda take ga zata fi sararin amsa mata tambayoyi.
Wata kaddarar ta sake faruwa a washe gari da muka koma Belin da aka badamu, sai dai daga nan aka wuce da mu Katsina, inda muka yi kwana Biyu, daga baya muka dawo gida. Dukkan Wayoyina suna hannunsu, bani da ikon hawa Facebook, Kira ko kuma tura sako ga kowa, musamman saboda Rashin lambobin mutane, wannan yasa ban kara ji daga Fatima ba, ban kuma kira Malam Bashir ko Wakiliyar su dake a Kano ba.
Bayan komai ya lafa a daga wannan Kaddarar data kaini gaba zuwa Daukaka, na bude akwatin sakunana naci karo da sakon Email daga Fatima Sadik Al-Ameen. Na shiga kai tsaye don da farko banyi zaton ita bace, amma ganin rubutun da ke a ciki yasa na hakikance lallai ita dince.
Labarinta ne a gajarce, da kuma yadda ta fara Madigo, Kalubale, da kuma Kiran da tayi wa Yan uwa Mata masu yin wannan harka da kuma masu son farawa. Duk da wannan sakon nata, hakan bai sa nayi kasa a guiwa ba wajen kiranta. Cikin ikon Allah kuwa ta dauki wannan kiran nawa.
“Nayi maka wani laifi ne da ya zama baka kirana ni kuma in na kiraka kullum wayarka a kasha ko Not Reaceable?” Ta fada bayan ta daga.
Nace da ita cikin sanyin murya “Kiyi hakuri Fatima, abubuwa da dama sun faru wadan da sune suka sanya kika jinni shiru ba tare da kin kara ji daga gareni ba.”
Tace “Koma dai me nene ai ka aiko min da sakon Message ko Email ko kuma ta wata hanyar don tabbatar min da cewa kana tare da ni, rashin ji daga gareka yasa na fara tunanin janyewa daga kudiri na, wata kila ko ban dace da fadin rayuwata ga kowa ba, babu wanda zai tsaya ya saurare ni?
Na ce da ita cikin sauri “Ki daina wannan tunanin, zan iya ce maki babu wanda yake so yaji labarin ki kamar ni, kuma na tabbata duniya zata so taji wannan labarin naki, don zai taimaka wajen rage yaduwar wannan bala’in”
A nan ne ta fara sakkowa. Tace da ni “Kaga sako na na Email?”
Na amsa da Eh na gani, shi yasa ma na kiraki, don nafi son na ji labarin daga bakinki.”
Tace “Har nakanji kunya idan nazo bada wannan labarin”
Na katse tad a cewa “Meye abin kunya a ciki? Iftila’I ne Allah ya dora maki, cikin ikon shi kuma ya yaye maki, kamar jarabawa ce yayi maki, don haka banga dalilin jin kunyarki a wannan lamari ba.”
Tace “Kamar yadda ka karanta a Email din da na aika maka, ni dai sunana Fatima, kuma an haifi a garin Kano, nayi karatu a nan cikin kano har zuwa sakandire, inda nikeyi Jeka-Ka-Dawo. A nan ne na hadu da Fatima amma ita ana ce mata Zara.
“Hakikanin gaskiya iyayena sun bani tarbiya, naje islamiya sannan kullum cikin fada da nasiha sukeyimin akan na yi taka tsan-tsan da matan da zanyi mu’amala da su, har sukan ce “Yafi kyau ka nisantar da danka daga matan banza akan mazan banza. Domin matan banza ne zasu iya shigowa har cikin gidanka su yaudari yarka har zuwa waje wajen mazan banza.”
“Na kulla kawance nida Zara, ko ina muna a tare, takan rika zuwa gidan mu nima nakan je gidan su. Wannan duka iyayen mu suka san kawancen dake a tsakaninmu.
“Kamar ko wa’anne kawaye, muna yin waya da juna don jin inda muke da kuma abinda mukeyi, ko kuma inda zamu hadu a cikin makaranta, Ko kuma dai don wata harkar da ta taso ta daban.
“Wata rana Zara ta kirani, take tambayata “Nikam don Allah Fatima in azan sami yarinya budurwa kamar ki? Wacce dai zamu rika yin harka tare”
Nayi mamakin jin wannan tambayar nace da ita “Wai kina nufin kamar a film? Ko kuwa yar film din kike Magana ne? Ban gane ba”
A nan dai Zara ta fito min a mutum, ta nuna min ita yar Madigo ce. Tun daga wannan rana na fara ja baya da ita, ko ta kirani bana dagawa, na daina zuwa gidan su, idan tazo namu ba a sake nike ba, a makaranta ma ba’a ganinmu tare.
Wata rana Zara ta turo min message tana rokona na dauki wayarta, bayan na dauka ne take cemin”:
“Fatima ni zaki yi wa haka? Don na nuna maki ko ni wacece kike gudu na ko? To kije zaki gani”
Nace da ita “Babu abinda zan gani sai alkairi”
A hankali dai Zara ta fara dawowa cikin rayuwata, ta bani hakuri akan maganganun da tayi a baya, har dai daga karshe muka dawo muka shirya, muka ci gaba da harkokin mu kamar babu abinda ya taba faruwa a tsakanin mu.
Wata rana ta kirani akan na rakata Super Market zata sai kayan kwalliya, kamar bazan je ba, ta matsa min har dai na amince muka je tare. Ta yi siyayyar su turaruka da kayan kwalliya, a nan ne ta bani wani turare tana cewa:
“Amshi wannan turaren na baki kyauta, naji kamshinsa yayi min kyau, kema nasan zaki so shi. Amshi ki shaka kiji?”
Na amsa ina cewa “Aiko dama kin barshi, don har yanzu ina da turare bai kare ba”
Na bude turaren na fesa a saman hannuna na shaki kamshi, har cikin kwakwalwata wannan kamshin ya shiga. Na dan ji “Dhuuum !” kana na dawo dai-dai.
Zara ta kalle ni tayi murmushi tace “Ya kika ji kamshin?”
Na ce “Yana da kamshi sosai”
Tace “Kadan ma kenan, wani abun sai anjima”
Tun daga lokacin da na shaki wannan turare, sai na kasance cikin yanayin bukatar Mace, naji na tsani maza bana ma so namiji ko Magana yayi min. Duk wani umarni da Zara zata bani ina hanzari zanyi mata shi.
“Babu abinda nafi kauna a Rayuwata ayi min Kyauta [Gift] dashi kamar Turare. Na fara Madigo bayan na shaki kamshin turaren da Zara ta bani a matsayin kyauta dashi, daga wannan ranar duk abinda take so inayin shi ba tare da ko Musu ba”
Mun shafe tsawan shekaru muna tare kullum aikin mu daya, biyawa juna bukata. A lokacin iyayena suka fahimci na canja gaba daya, suka fara bincike a kaina, har dai suka fahimci kamar Zara ce silar lalacewata, sukayi kokarin rabani da ita tare da gindaya mana sharadin kada mu kara zama tare. Duk da haka, mukan samu lokaci mu kebe don yin abinda ranmu yake so, anyi-anyi amma bana jin zan iya rabuwa da Zara.
Akwai wanda kusan dan uwana ne, da shi ake so a hadamu aure, ina sonsa yana sona, amma saboda zuwan Zara yasa ko sauraronsa ma bana yi, nace auren ma na fasa. Dakyar dai bayan iyayena sun hada da roko daga Malamai har na karkata gare su. A lokacin naji kuma sam bana sha’awar Zara.
Babar matsalar da nike fuskanta game da lafiyar jikina kuwa shine Nauyin jiki da nike ji, ga Kasala kamar wata mai ciki, bani da wata cuta don munje asibiti an gwada ni.
“To kaji a takaice ke nan, wannan shine labari na”
Bayan jin wannan labarin na Fatima, na sauke numfashi na kana nace da ita “Kamar yadda kika bani wannan labarin haka, zaki iya zayyana ma wannan Yar Jaridar da nace zan haka ki da ita?”
Ta amsa da “Kwarai zan zayyana mata, dama abinda yafi hakan, tunda kaga a nan way ace mukeyi kodon kada kudin ka su kare dole in gajarce abin”
Nace “Hakane Fatima, insha Allahu daga yau zuwa Litinin zata zo ta same ki, sannan abinda nike so dake shine, ki saki jikinki inda kuka hadu. Ki sanar da ita komai, don hakan ne kawai zai sai duniya ta fahimci sakon da kike son isar masu a cikin labarinki.
Fatima t ace “Insha Allahu zanyi hakan, na kuma gode da ka bani lokacin ka har ka saurari labarina, sannan don Allah ka kara zage damtse wajen ganin an kawo karshen wannan bala’in, duk da nasan cewa kawo karshen Madigo ba karamin aiki bane, amma ko ba komai ka bada gudunmawa wajen rage yin shi.
Tunda na fara karanta labarinka wallahi naji na kara tsanar wannan dabi’ar, na kuma kara nadamar rayuwar da nayi a baya, sai nike ji, Ina ma ace sauran Mata da suka yi rayuwa irin wannan zasu fito don fadima duniya tasu rayuwar ko don sauran Mata su dauki Izina.”
Nace da ita, “Insha Allahu nima zan yi iya bakin kokarina wajen ganin munyi yaki akan Madigo. Kuma bi’izinillahi zamu samu nasara koda kuwa hakan na nufin tsayar da numfashin da muke shaka. Daga Karshe kuma ina yi maki fatan Alkairi, duk ranar da na shigo Kano zan zo mu sada zumunci, ina yi maki fatan Alkairi a rayuwarki. Sai kuma naga labarin ki a Jarida.”
Tace “Nima na Gode, Allah ya baka sa’a ya kuma kareka daga sharrin Mahassada, don duk wanda yake son yaga bayanka to makiyin al’umma ne, bai san amfanin ka gare su ba, da za’a ce ya kawo misalign abinda kake kawowa da bazai iya kawo koda kwatar shi ba. Baiwa da fasaha ai gonar Mumini ce. Allah ya sa kafi haka.”
Na rufe wayar mu da cewa “Ameen nagode Fatima”.
Kawo zuwa yau ina ta kiran Lambar wayar Fatima amma ban sameta, ina so na cika wa Bashir Y Malumfashi alkawari kamar yadda na dauka, haka itama ina so nag a na cika mata nata alkawarin na son ganin ta cika burinta.
Idan Fatima Sadik Al – Al’ameen ta ga wannan rubutun, Ki sani cewa dani da ire-irena masu son ganin kakwo karshen wannan dabi’a a cikin al’umma muna nan muna tsumayin kara kasancewa tare dake, idan boyewa kikeyi, ina so ki sani cewa babu amfanin boyewa abinda ya wuce na daga rayuwarki, babban abinda yafi shine inganta abinda yai saura na daga rayuwar taki. Don haka Fatima ki tuntube ni kai tsaye da lambata ta Sama don cimma Gacin abinda muka fara.
Haka zalika, Mata kamar Fatima, wadan da suke da burin duniya ta san labarin su a zaman da sukayi cikin wannan dabi’a, suna da cikakkar dama ta fitowa dan fadi wa duniya labarin su. Babu wani aibu don ka tuna baya a niyyar gyarawa na gaba, babbar nasara ce ace ka gyara kanka ka kuma gyara wani. Don haka, kofa a bude take ga duk wacce ta taba shiga irin wannan rayuwa ta Madigo, ko wacce take cikin wannan rayuwar, ko kuma wacce take da sha’awar ma ta fara, data tuntubeni wata kila zamu iya taruwa don kawo karshen wannan Dabi’a tare.
©Sani Hamza Funtua.
Whatsapp @ +2347032183026
Email - Danhamzaa@Yahoo.com
Allah ya shirya masu wannan hali
ReplyDeleteya ganar dasu gaskiya in zasu bari su bari in kuma ba zasu bari ba
ya Allah kai masu yadda kace zakayi masu na fannonin azabarka
bissalam
zaidu rabiu faskari
08166381570
07040673469: MATAN KANO KAWAI! Budurwa ko Bazawara harma da Sugar Momy indai a cikin garin Kano kike kuma kin kasanceƳa mace mai tsananin sha’awar tarayya da Ɗa namiji to ga abokin tafiya ɗoɗar kin samu Dan sumulmulin saurayi Sugar boy indai a cikin kano kike zamu hadu duk sanda kikeso mujidadin junanmu cikin sirri da amana kedai kawai ki tuntu6eni awannan number ƙira,whatsapp ko text message: 07040673469.
ReplyDelete