Wednesday, 4 May 2016

Dan Majilissar Funtua {Total} Yasa Yan Sanda Sun Kama Wani Ma Rubuci A Katsina

Kira ga Jami'an Tsaro na Yan-sanda, Majalissar Jaha ta Katsina Dakuma Gwamnatin Jahar Katsina
Wani Dan Majalissar dokoki na jahar Katsina mai wakiltar Funtua yasa yan sanda sunyi awon gaba da wani marubuci a farfajiyar Facebook mai suna Sani Hamza Funtuwa saboda wata budaddiyar wasika daya rubutama dan Majalissar.

Dan haka muna kira ga hukumar yan sanda datasan cewa ba an kirkireta bane danta kare muradun masu madafun iko. Ba zaluntar mutane akace tayi ba, a'a, kare hakkinsu akace tayi, irin hakkin Sani Hamza Funtua da aka shiga.

Muna kira ga shuwagabannin Majalissar Dokoki na jaha dasu kira abokin aikinsu da yashiga hankalinshi! Yaza'ayi an zabeshi yakare hakkin mutane kuma yazama yana samasu takunkumi? Idan wanda aka zaba yayi dokoki dan Jin dadin al'umma, kuma yazama shine kan gaba akan karya doka? Muna kira da aja mashi hankali kuma yasa asaki Sani Hamza Funtua.

Harwayau munakira ga gwamnatin jaha data shiga wannan magana saboda anshiga hakkin danta bakan ka'ida ba.

Munada shedu inda Dan Majalissar yake barazana ga Sani Hamza akan rubutun dayayi.
Muna kira ga duk wani Dan Katsina dakuma abokanmu na sauran Jahohi dasu taimaka wurin wannan yakin kwato yancin dan'uwan mu danya zama darasi akan masu tinanin aikata haka.

No comments:

Post a Comment