Sunday, 8 May 2016

Kungiyar Marubuta Katsina Ta Taka Rawa Wajen Sasunta Rikici Tsakanin Sani Hamza da Dan Majalisa Mai Wakiltar Funtua

Bismillahi!
Salamu Alaikum., 'Danmajalissar jiha, (Katsina) mai wakiltar karamar hukumar Funtua.
.
Tun da na ga fos din Malam Bashir Yahuza Malumfashi, wanda ya kattaba cewar an kama Sani Funtua ta dalilin rubutun da yake yi a kan d'anmajalissar karamar hukumarsu, musamman ma wata budaddiyar wasika da shi Hamzan ya rubutu zuwa ga Abubakar Total din, nan take na kira zababben shugaban Kungiyar Marubuta jihar Katsina (KMK) domin ganin abin ya shafi rubutu da marubuta ne, a nan yake shaida mini ba shi gari. Jin haka ya sa na tuntubi Jami'in Hulda Da Jama'a, wanda shi ma ba mazaunin cikin garin na Katsina ba ne, don haka sai na tafi ga Sakataren na KMK, inda na yi sa'ar samunsa, na kuma shaida mishi halin da ake ciki game da kes din na su Sani. Nan take ya fara bibiyar kadin lamarin cikin zama da kazar-kazar. Bayan shi sai na sake tuntubar Ma'aji da kuma Mataimakiyar Shugaba, su ma duk suka bazama don ganin lalubo bakin zaren. Kafin a jima dai duk zababbun shugabannin KMK muka dukufa ta ko'ina wajen sasanta wannan rikici, mun tuntubi abokan Sani don jin takamaiman abinda ke faruwa,


sun kuma ba mu hadin kai wajen bayyana mana zahirin abinda ya wakana. Daga nan sai aka fara motsi wajen ganin an saki shi Sanin da wani abokinsa da aka kama su tare. Tashin farko Mataimakin Sakataren Tsare-tsare ya taso tun daga Matazu har Katsina da safiyar yau juma'a, inda suka hadu da Sakatare domin ganawa da d'anmajalissa, Abubakar Total. Sun samu ganawa da shi, kuma ya jaddada musu cewar shi ba don wulakanci ko cin zarafi ya sa aka kama su ba, wai saboda a yi musu tsakani ne kawai, kamar dai yadda ya kira abokin Sani, Janare Funtua ya shaida mishi a shekaranjiya. Zaman nasu ya samu maslaha da haske kwarai da gaske, tun da a nan take ya kira ofishin yan sandan da su Sani suke, ya shaida musu kawai a sake su, komai ya wuce, amma fa a ja musu kunne don kar su sake shiga duk wata sabga tashi (Kasancewar ba jam'iyyarsu daya ba), har ma ya nuna cewar akwai wanda yake zargin shi ke tura Sani don yi mishi ''Fitsara!''
.
Daga karshe dai, kuma a takaice an saki Sani Hamza Funtua da kuma yin sasanci tsakaninsu da d'anmajalissa Abubukar Total a dazu da ranar nan.
.
Hakika Kungiyar Marubuta jihar Katsina ta taka muhimmiyar rawa a wannan kes din, duk da cewar Sani Funtua ba mambanta ba ne, sai dai da yake an ce ruwan da ya ci Doma, ba shi barin Awai, shi ya sa ba mu yi kasa a gwiwa ba wajen ganin komai ya sanyaya, sai fatar Allah kara sanyaya shi.
.
... A madadin d'aukacin shugabanni da mambobin kungiya muna mika godiyarmu ga Danmajalissa, Abubakar Total da jami'an yan sandan da suka ba mu hadin kai wajen ganin komai ya daidaita, muna godiya da wannan karamci.
.
Muna fatar Allah kiyaye gaba.
.
Mataimakin Sakatare;
Hafiz Adamu Koza, a madadin daukacin shugabannin Kungiyar Marubuta jihar Katsina (KMK).

No comments:

Post a Comment