Jaridar leadership
tasa Kanun labarin hirar da su kayi da mai ba Gwamna Masari shawara akan
harkokin siyasa kamar haka :"Jam'iyyar PDP bata da tacewa a shekara sha
shidar da ta kwashe tana mulkin Jihar Katsina"
Kanun
labarin da katsina post ta fitar dangane da wannan hira kamar yadda ta chanza
kuma ta wallafa a bangon Jaridar ta da ta wallafa a 1:5:2016 tace " mai ba
Gwamna Masari shawara ya hakikance akan cewa Marigayi Yar'adua da Shema basu
tsinana komai ba a jihar katsina"
Labarai
suna daga cikin manyan hajoji masu daraja a wannan duniya tamu. Yadda masu
karatu suke sha'awar karanta labari da yadda zasu fahimci labari da kuma yadda
sukanyi tsokaci dangane da labari mafi akasari ya danganta ga yadda mai bada
labari ya tsara kanun labarinsa. Wannan yasa da yawa daga wasu masu karanta
labari a wasu lokuttan sukan dogara kaco kam aKan kanun labari batare da
karanta gangan jikin labari ba.
Tasirin
samun labarai ta kafar yanar gizo musamman ta fejikan sada zumunta wato
Facebook yana akan sahun gaba a wannan zamanin a wurin al'umma ganin yadda yake
da saukin kawo labarai yadawa har ma da tofa albarkacin baki wannan ne ya
haifar da matsalar yada jita jita idan har kafar yada labari ba sahihiya bace
ko kuma yadda kafar data yada labarin batayi taka tsantsan ba wajen fadin
sahihin zance dangane da labarin data bayar.
Cliqqmagazine.blogspot.com ta samu tattaunawa da Mai ba Gwamna Masari shawara akan
harkokin siyasa kuma tsohon kakakin majalissar jihar Katsina Rt. Hon. Alhaji
Usman Bala Zango ta wayar tarho dangane da hirar sa da yayi da wakilin Jaridar
leadership sannan ta wallafa wacce itama katsina post ta dauka ta yada wanda
hakan ya haddasa kace nace.
Jaridar
leadership ta wallafa kanun labarin nata kamar haka "Jam'iyyar PDP bata da
abinda zata nuna a shekara sha shidar da ta kwashe tana mulkin jihar
Katsina"
A hirar
da sukayi da Jaridar ba inda mai ba Gwamnan shawara kai tsaye ya kalubalanci
Marigayi tsohon shugaban kasa Umaru Musa yar'adua ba kuma inda ya anbaci
sunansa haka kuma ba inda ya anbaci sunan tsohon gwamnan Jihar Katsina Shehu
Shema.
Da dan
jarida ya tambayeshi "wani Lokaci a baya kai cikakken dan jam'iyyar PDP ne
amma daga baya sai gashi kuma kana Kan
gaba wajen kalubalantar PDP to ko me ya kawo hakan?
Mai ba
Gwamna Masari shawara sai yaci gaba da cewa kasan PDP tayi tabargaza da yawa.
Wannan tasa basu iya sun tabuka abin azo a ganiba kowa yasan barnar da PDP ta
aikata. Abinda ya tunzura ni nabar PDP kuwa shine almubazzaranci da kudin
al'umma rashin tsaro da kuma kasa cika alkawurran da suke daukar ma
jama'a. Mutanen PDP ba da gaske suke ba.........
Wakilin
na jaridar leadership ya kara tambayar sa shin baka ganin gwamnatin PDP data
shude tayi kokari fiye da wannan gwamnatin taku?
Sai ya
kada baki ya bashi ansa kamar haka anan ai masu zabe Sune alkalai kasan ai
bazaka gina tituna ba kuma ga mutane na cikin yunwa da matsanancin talauci.
Hakane gwamnatin PDP data shude ta giggina makarantu amma kuma zaka samu
makarantun ba kujeru ba isassun malamai ba kayan da malaman da daliban zasu yi
amfani dasu wajen koyo da koyarwa. Sai a yanzu ne wannan gwamnati mai ci yanzu
ke kokarin shirye shiryen daukar kwararrun Malamai, tareda samar da isassun
kujeru har ma da isassun kayan aikin koyo da koyarwa. Yanzu taya gwamnati zata
gina kasuwa akan kudi N100 million ga Mutanen karkara a kowace karamar hukuma
na kananan hukumomin 34 dake jihar nan bayan su Mutanen nan suna cikin
mawuyacin halin da ba gina kasuwa bane a gabansu? PDP ba ruwanta da neman
shawarar jama'a tanayin duk wani abu da take ganin shine dai dai awurinta
batareda tuntubar jama'ar da take mulka ba.
Wannan
wani bangare ne na yadda firar tasu ta kasance kuma idan akabi diddigin
amsoshin sa za'a samu cewa suna Kan
hanya don rashin kyautatawar jam'iyyar PDP ne yasa Mutanen jihar katsina sukayi
mata mummunan kayi a zaben daya gabata
Dangane
da kanun labarin da katsina post data wallafa game da wannan hirar wanda ya
canza daukacin ma'anar hirar gaba daya kuma ya haddasa kace nace a cikin
al'ummar jihar katsina mai ba Gwamna Masari shawara ya shaidama
Cliqqmagazine.blogspot.com cewar sunyi mar kage saboda a firar da sukayi kaf ba
inda ya anbaci abinda katsina post tace wai shi ya fada
Yayi
kira da babbar murya ga masu wallafa labari ko kuma yan jarida da su guji yada
labarin karya ko wanda basu da tabbas a kansa musamman ma labarin da basune
ainahin wanda suka samo Shiba sannan ya kara da cewa lalle ne katsina post su
rika tunrubar ita jaridar leadership kafin su chanza mata kanun labari
No comments:
Post a Comment