Wednesday, 4 May 2016

Gwamna Masari Ya Kai Ziyarar Bazata A Asibitin Garin Daura



A kokarin da yake na tabbatar da ana aiwatar da ayyukan da Gwamnati ta bayar yadda ya kamata, a jiya litinin 2/05/2016, Gwamna Aminu Bello Masari ya kai ziyarar gani da ido a babbar asibitin garin Daura.



A yayin wannan ziyara, Gwamna ya zagaya duka sassan asibitin domin gane ma idon shi yadda aikin gyara da kuma fadada asibitin ke tafiya. Bayan nuna gamsuwa da nagartar aikin, ya kuma ja hankalin masu gudanar da aikin da su tabbatar da sun kammala shi cikin lokacin da aka kayyade.
Gwamnan ya kuma ziyarci marasa lafiya da suke kwance a asibitin tare da yi masu addu'ar Allah Ya basu lafiya.


No comments:

Post a Comment