Wannan dandali na Daura emirate social media forum
(DESOMF), muke so muyi amfani da wannan damar domin kira ga al'ummar jahar
katsina musamman matasa maza da mata, da mu kasance masu nuna halayan kirki a
yayin wannan muhimmin taron kamar yadda a kasan katsinawa dasu.
Bayan haka kira ga al'ummar jahar katsina da mu
kauce ma duk wani abu da zai zubar da mutumcin jaharmu da shuwagabaninmu.
Sannan munaso al'ummar jahar katsina su sani cewar wannan taro ba na siyasa
bane, taro ne na duk wani mai kishin ko mai son cigaban jahar katsina ne taro
ne na habaka tattalin arzikin jahar katsina.
Daga karshe mu sani cewar wani daga cikin
manyan da zasu halarci wannan muhimmin taron kila shi ne zuwansa jaharmu na
farko don haka fata matasa zamu bada hadin kai domin ayi wannan wannan muhimmin
taron lafiya a gama lafiya kuma kowa ya koma gidansu lafiya.
Wannan sakone daga kungiyar marubuta na masarautar
Daura emirate social media forum (DESOMF).
No comments:
Post a Comment