Lafiya da ilimin al'umma abubuwane
masu muhimmanci a rayuwa dan babu abinda ke yiwuwa saida lafiya koda lafiyar
kuma saida ilimi, ya kamata kamar yadda adalin shugaba gwamnan wannan jihar
yasha alwashin maida ya'yayenshi makarantun al'umma mallakin gwamnatin jihar
mungani ya aiwatar alhamdulillahi muna godiya.
Abu na biyu da muke fatan gani
shine ziyartar asibitoci mallakar gwamnati yayin rashin lafiya wannan ko shakka
babu zai inganta yanayin aiki a wadannan asibitocin, tare da farfado da
asibitocin daga mummunan yanayin da suke ayau.
Kamar yadda ake cigaba da
gine-gine a Babban asibitin na katsina, muna fatan ganin a kammala bada jimawa
ba. Sannan kuma bayan kammalawa akwai bukatar ziyarar bazata ga mai girma
gwamna akai-akai badan komai ba sai don ganin anyi abinda ya dace musamman ga
majiyata da kuma su kansu ma'aikatan.
No comments:
Post a Comment