Saturday, 28 May 2016

Gwamna Masari Zai Mayar da Ma'aikatan Kana nan Hukumomi Malaman Makaranta

 Gwamna Aminu Bello Masari ya bada umurnin cewa duk wani ma'aikaci da aka gano yana amsar albashi daga Gwamnati alhali kuma yana aikin albashi a wata hukuma dabam, to ya dawo wa Gwamnati da kudin ta.

Gwamnan ya bada wannan umurni a lokacin da kwamitin tantance Ma'aikatan kananan hukumomi ya mika rahoton shi.

Gwamnan ya nuna matukar rashin jin dadin shi ganin yadda wasu mutane suka maida almundahana da kudin al'umma abin ado da tunkaho. Ya kuma kara da cewa wadanda suke wannan aika-aika suna sane haka kuma akwai wadanda suke taya su tare da daure masu gindi. Saboda haka, Gwamnati za ta dauki duk matakin da ya dace wajen hukunta wannan gungun mutane marasa kishin al'umma. Ya kuma bayyana cewa duk wani gurbi da aka samu ta wannan tantancewa da akai to za a cike shi ne ta hanyar daukowa daga cikin Ma'aikatan wucin gadi (Casual Staff) da suke aiki a wurin.

Tun farko a nashi jawabin, Shugaban Kwamitin Alhaji Maigari Salihu Danjuma mni, ya shaida wa 
Gwamnan cewa sai da suka ziyarci wasu kananan hukumomin kuma suka tattauna da ma'aikata domin tabbatar da sun bada rahoto mai inganci.
Ya kara da cewa sun sami;

1. Ma'aikata Dari Shidda da Sittin da Biyar (665) wadanda suke da takardar shaidar Malanta amma suna zaune a ofisoshi cikin kananan hukumomi, amma yanzu haka suna kan aikin yadda za tura su Makarantu domin ci gaba da koyarwa kamar yadda ya dace.


2. Akwai kuma wasu Malaman Makarantu su Dubu Daya da Dari Hudu da Talatin da Biyar (1,435) da suke da takardar shaidar Malanta ta Digiri na daya wasu ma kuma har da na biyu, amma suna koyarwa a Makarantun Firamare wadanda su ma za a mayar da su Makarantun Sakandire.

3. Jimillar ma'aikata Dari Bakwai da Sittin da Hudu (764) ne kuma suka bar wuraren aikin su na tsawon lokaci ba da wani dalili ba. A saboda haka suma an bada shawarar a tsaida albashin har sai idan sun taho da wani gamsashshen uzuri.

4. Akwai kuma wasu manyan Ma'aikatan jinya da suke zaune a cikin Makarantu domin kula da larurorin Dalibai alhali kuma an fi bukatar su a asibitoci. Suma an bada shawarar a musanya su domin cike gibin da ke akwai a asibitoci.

5. Alhaji Maigari ya kuma shaida wa Gwamnan cewar akwai Ma'aikatan lafiya guda Sittin da Hudu (64) da Kwamitin ya gano cewa suna aikin albashi a wasu hukumomin dabam amma basu bar amsar albashin Gwamnati ba. Kwamiti ya bada shawarar su dawo da duk albashin da suka amsa sannan kuma ayi masu hukuncin da ya dace, idan kuma Gwamnati ta ga da hali sai ta amshi kudin tare da ja masu kunne.

Wadannan Ma'aikatan suna aiki ne a hukumomi irin su DFID, UNICEF, WHO da sauran su.

No comments:

Post a Comment