Tuesday, 24 May 2016

Hon. Sani Saidu Ya Tallafawa Mutum Sama Da 300 A Mazabarshi.



Dan majalisar tarayya mai wakiltar Daura Sandamu da Mai'adua Rt. Hon. Sani Sa'idu fago ya bayar da tallafi ga mutanen mazabarsa a ranar talata 24/05/2016. Tallafin da ya hada da babura, kekunan dinki, generators, keke napep,da sauransu, ya bayar dasu ne ga mutanen da suka kai akalla sama da dari uku.


A yayin bada wannan tallafi Dan majalissar yayi kira ga wadanda Allah ya cida suka samu morar wannan tallafi da su tabbatar sunyi amfani dashi ta hanyar data dace don acewarsa hakan ne zai kara masa kwarin gwiwar cigaba da aiwatar da irin wannan tallafi.  ya kuma kara da kira da wandanda Allah bai sa sun shiga cikin wannan tsari ba da su dan kara hakuri akwai tanade tanade da dama makamantan wannan da yake da niyyar aiwatar ga mutanen wannan mazaba tasa wanda acewarsa shirin zai amfanar da dinbin mutane a mazabar tasa. Ya furta cewar yana matukar alfahari tare da jinjinawa al'ummar mazabarsa bisa hakuri da juriya da suke nunawa game da halin da gwamnatin tasu ta samu kanta.


hakan ne ma yasa ya bukaci mutanen mazabar tasa da su cigaba da bawa gwamnati hadin kan da Yakamata kamar yadda suka saba tareda yi mata addu'ar Allah ya bata ikon aiwatar da dukkanin shirye shiryen inganta rayuwar talakan Nigeria data kudiri niyya kuma ta tsayu akan hakan karkashin jagorancin adalin shugaba Muhammadu Buhari.

 A zantawar da Cliqqmagazine.blogspot.com tayi da wasu daga cikin wanda suka samu nasarar morar wannan romon demokaradiyyar sun bayyana matukar farin cikin su da Jin dadinsu bisa ga wannan kulawa da suka samu daga wakilin nasu. Daya daga cikin jadanan  raba wannan tallafi Alhaji Sani Ali Jarkuka ya jinjinawa dan majalissar bisa ga wannan namijin kokari da yayi tareda kira akan cewar ya zama wajibi ga yan siyasa zababbu dama masu rike da mukaman siyasa a gwamnati cewar lalle su rika daurewa suna jibintar al'amuran jama'a ta hanyar tallafa masu gwargwadon iko ko sun samu sassaucin rayuwa. Duk wanda ya tallafa ma wani to Shima fa Allah zai jibinci lamuransa yasa albarka a cikin sha'anin mulkinsa da dukiyarsa.

No comments:

Post a Comment