Gwamna Aminu Bello Masari ya tabbatar da haka, a lokacin da ya kaddamar da Kwamitoci guda Hudu; na farko wanda zai tantance Ma’aikatan da suke da hakkin a rika biyansu albashi da tsarin CONHESS ta amfani da dokar da ta samar da sabon tsarin albashin, sabanin yadda ake yi a halin yanzu.
Sauran Kwamitocin kuma sune wadanda zasu duba tare kuma da bada shawara a kan koke-koken Ma’aikatan da basu haye tantancewar da ake kan yi wa Ma’aikatan ba (Kowace shiyya ta Danmajalisar Dattawa tana da nata Kwamiti da zai duba koken).
Gwamnan wanda ya bayyana cewa Gwamnati ta kafa wadannan Kwamitoci ne domin tabbatar da adalci ga kowa, ya kuma yi kira da ‘yan kwamitocin da su sa tsoron Allah a cikin wannan aikin da za suyi.
A jawabin da yayi a madadin Kwamitocin, Shugaban Kwamitin da zai tantance CONHESS, Alhaji Maigari Salihu Danjuma mni, ya tabbatar da aniyar su ta yin wannan aiki cikin gaskiya da tsoron Allah.
No comments:
Post a Comment