Sunday, 15 May 2016

Kakakin Majalisar Jihar Katsina Yayi Ma Malaman Wata Islamiya A Daura Ba Zata


A jiya ne 14/5/2016 madarasatul Shababul khairi kofar Arewa dake a garin Daura ta gudanar da walimar yaye dalibai dari hadu da suka samu damar sauke alkur'ani mai tsarki tare da karin wasu daliban talatin (maza ashirin mata goma) yan kasa da shekara sha biyu da suka samu damar hardace Alkuri'ani a cikin shekara biyu haka kuma da karin wasu dalibai matasa goma da suma suka samu damar hardace kur'anin gaba daya.

Wannan walima anyita ne akan jimlar dalibai dari hadu da arba'in da wannan makaranta ta yaye a karkashin shugabancin sheikh Malan Mansir Kamar yadda wakilin shugaban makaranta wato Malan Aliyu Salisu ya shaidawa Cliqqmagazine.blogspot.com cewar Malamai da dalibai na wannan makaranta harma da iyayen yara sun yaba kwarai da gaske kuma sunyi mamaki matuka da yadda kakakin majalisar jihar katsina Rt Hon Aliyu Sabi'u Muduru ya gudanar masu da jawabai masu matukar muhimmanci cikin harshen larabci da yadda ya nuna masu gamsuwarsa dangane da yadda ake gudanar da makarantar da kuma kulawa ta musamman da ya basu wajen bada lokacin sa don halartar wannan muhimmin taro,  hakama sun yaba da irin shawarwari da yaba malamai da dalibai harma da daukacin al'umma dangane da muhimmancin neman ilmin addini sun nuna farin ciki kwarai dangane da hakan.


Shugaban makarantar ta bakin wakilin nasa yayi kira da cewa lalle shugabanni su rika daurewa suna halartar irin wannan taruka kuma suna gudanar da jawabai yin hakan acewarsa ba karamin kwarin gwiwa yake karama dalibai da Malamai ba wannan yasa suka kara da yaba ma Dan majalissa mai wakiltar Daura Hon Nasir Yahaya Daura bisa ga jawabin Jan hankali da ya gudanar ma dalibai harma da malamai da iyayen yara sun nuna Jin dadinsu dangane da hakan.

Hakama a zantawar da Cliqqmagazine.blogspot.com tayi da daya daga cikin iyayen yaran mai suna Malan Audu Salisu ya fadi cewar lalle suna godiya ga Allah da ya ba wannan yara nasu damar hardace alkur'ani tun suna yan kananan su bayan haka ya kara da yima Malaman makarantar addu'ar fatan alheri bisa yadda suke rike amanar yayansu kuma da yadda akoda yaushe suke kokarin ba yaransu ingantacciyar tarbiya sannan yayi kira da lalle gwamnatin jihar Katsina ta fito da wani tsari na musamman don tallafa ma makarantun islamiyya ganin jihar katsina Jiha ce da kashi casa'in na mutanen jihar Musulmai ne

Haka ma wani dalibi Umar Aliyu ya nuna farin cikinsa da Jin dadinsa da Allah yasa yaga wannan rana ya kara da cewa yana yima sauran yan uwansa dalibai fatan suma Allah ya basu ikon kai wa ga wannan matsayin. na samun damar haddace Alkur'ani mai girma.


No comments:

Post a Comment