A'a Abinda ake nufi anan shine Masu Gidajen man
'yan kasuwa an lamince musu su shigo da man daga duk inda suke so. Amma dukkan
Man 'yan kasuwa zasuna sayar dashi akan Farashin da bazai taba haura Naira 145
ba.
Amma kuma gidajen Man mallakin gwamnati irinsu:
NNPC, TOTAL da sauransu, zasuna sayarwa alumma akan farashi Mai rahusa. Idan
har gwamnati ta sakarwa 'yan kasuwar Mara suka shigo da Man Barkatai kuma ta
sanya ido sosai akan 'yan kasuwar akan yadda suke gudanar da hada-hadarsu. To
Insha Allahu Man zai zama tamkar "Ledar Pure Water akan titunan mu".
Kaga kenan 'yan kasuwar Mai zasu karu, kuma duk abinda yayi yawa to karshensa
zai fadi ne warwas .
Misalin abinda yake faru yanzu a kasuwannin Man Fetur
din ta duniya. . Hasalima Idan mukayi La'akari da Abinda ya faru ga Kamfanonin
wayar Salula a Nigeria.
A baya Layin wayar Salula guda daya taka wato "MTEL". wadda mallakin
gwamnati ne.
Amma tun daga Lokacin da gwamnati ta sakarwa kamfanonin Layukan
wayar Salula mara su zo su kafa a Nigeria irinsu MTN, V-MOBILE, GLO da
sauransu. Da farkon farawa sai da ake sayar da Layin waya Kusan Naira 13,000. Amma yanzu da abubuwan suka yawaita gashi
Layin waya Harda akwai na N50 ma. wani Lokacin ma Layin wayar kyauta za'a baka.
Kaga kenan Idan Allah ya yarda Shima wannan Bangare na Man-Fetur din yan kasuwa
zasu shiga zasu shiga gasar shigo dashi ta ko ina, babu kama
hannu yaro. Wadda daga karshe Farashin Man zai dinga rikirkitowa a kowanne
Lokaci da ikon Allah. ~ Muna da tabbacin Buhari bazaiyi abinda zai cutar da
alummar wannan kasa ba.
Ya Allah muna rokonka ka sa wannan mataki da
gwamnatin Nigeria ta dauka
akan Man fetur yazama shine silar kawo karshen wahalhalun da alummar kasa kan Sha wajen samun man.
Allah ka sanya wannan itace hanyar da zata sanya man ya zama ana sayarshi har
N50.
Allah ya kara kawo mana yalwatuwar Arziki amen
No comments:
Post a Comment