BUDADDIYAR WASIKA Zuwa ga Danmajisalar karamar hukumar Funtua, Hon Abubakar Muhammad (Total). ©Sani Hamza Funtua.
29-04-206… 4:00pm.
Zan fara rubuta wannan wasikar da gaisuwa a gareka, ya aikin ofis da kuma na zagaye-zagaye? Allah ya tabbatar maka da alkairin abinda ke cikin zuciyarka Amin.
Kai tsaye ba tare da bata wani lokaci ba, zan je ga dalilan da yasa na rubuta maka wannan wasikar, da kuma son kasancewarta budaddiya wacce kowa zai iya karantawa. A ‘yan watannin baya, abubuwa sun faru tsakaninka da wani a mazabarka, inda har karshe dai ka aika rundunar ‘yan sanda don su kama maka shi.
Nayi mamakin yadda shugaba mai iko kamarka, kuma a matsayin mai majalisar mahukunta ta jaha zai yanke wannan danyen hukuncin, bayan ka san cewa muna rayuwane a karkashin demokaradiya, wacce kundin tsarinta ya bawa ko wane dan kasa daman a ya fadi albarkacin bakinshi matukar bai sabawa shari’a ba, koda kuwa suka ce ga gwamnati.
Sani Hamza Funtua kamar yadda nasan baka mance sunanshi ba, matashine da ke tasowa a turba ta Rubutu, yanzu zai zauna yanzu zai rubutu akan wannan zaman, sannan a cikin rubutun shi baka taba samunshi da amfani da kalmomi masu nuna jin tsoron abinda yake rubutawa. Idan har ka fahimci hakan, tabbas dole kai da akai rubutun kanka kaji tsoron abinda ya rubuta. Sai dai har yau har gobe, bai taba yin rubutun da zaisa hukuma ta kamashi har ace za’a daure shi ba.
Hamayya itace Kalma mafi sauki da zanyi amfani da ita wajen kiran abinda ke tsakaninka da Sani Hamza Funtua, hamayya kuwa ko dan da ka Haifa a cikinka zai iya hamayya dakai, shin don me zaka nuna tsantsar karfin mulki kasa a kamashi, saboda baka da gaskiya akan abinda yake fada? Ai kamar misalin Jam’iyyar PDP ce da sauran jam’iyyun adawa a lokacin da suke kan mulki, duk irin hamayyar da suka nuna me yasa PDP bata sa an kamasu ba, duk da cewar suna da cikakken iko akan hakan? Amsar daya cewa, Freedom of Expressing Views. Ina fatan zaka kara tunawa kanka cewa, dan da ka
Haifa ma zai iya hamayya dakai matukar ba jam’iyyarku daya ko alkiblarku daya ba.
Honourable sir, wannan wasika tawa ba zata kammalu ba har sai na tuna maka akan wasu abubuwa da suka faru kafin kahau da kuma bayan ka hau kujerarka. Nasan baka manta ba, kana sane, don lamurane bana wasa ba, sai ko in kaine kake kallon su a matsayin wasan. Batu na farko akan wani bawan Allah ne mai kishinka da son ganin ci gabanka, makaho ne shi, amma yafi mai ido muhimmanci a lokacin siyasarka. Yayi maka aiki ba dare ba rana, mawaki ne shi kuma takiyyi masani akan ilimin addini. Ya taimaka maka ta fannoni da dama, wadan da basai na fade sub a, kai ka fini sani. Sunan shi Aminu Makaho. Honourable Abubakar Muhammad, shin ko ka manta wannan bawan Allah? Ka manta irin gwagwarmayar da yasha duk don akanka duk da kasancewar shi makaho? Dame ka saka mashi? Illah ma sanya shi cikin buhun bakin ciki da kayi, ina fata dan majalisa bai manta rashin mutuncin da yayiwa wannan bawan Allah ba a lokacin da iftila’I ya fada mashi da damuna. Kayi hakuri dan nayi amfani da tsauraron kalmomi, ina kokari matuka wajen ganin na kiyaye harshe na.
Mutum na biyu kuwa, ba sai nayi maka dogon bayani akan shi ba, yana nan kwance da cutar barin rabin jiki, tashin shi abune da babu tabbas, ina fatan ka fahimci wanda nike nufi, duk dare, duk rana, duk sanyi da zafi, ko ana ruwa ana iska, yana tare dakai. Shima ka yi mashi tabon da bazai taba mantawa dakai ba, ka saka mashi da kishiyar abinda yayi maka, na tabbata idan har rayuwa ta tafi a haka, bana jin zai taba yafe maka. Wannan kenan.
Daga karshe inayi wa Dan majalisa fatan alkairi, Allah ya kara tausasa maka zuciya don jin kan wadan da suka tausasa maka a baya, Allah ya tsare ka da sharrin makiya don samun damar sakawa wadan da sukayi hidima akanka a baya. Allah ya baka tsawancin kwana don kawo ci gaba a wannan yanki namu na Funtua. Allah ya baka sa’a.
Wannan wasikar ta fito daga hannun Sani Hamza Funtua. Wanda yasha uwar rana don ganin ya dangwala maka, kullum tunanin shi kai mai gyara ne, zaka kawo ci gaba, ba kuma zai taba yanke kauna ga hakan ba.
Ka huta lafiya.
No comments:
Post a Comment