Sunday, 8 May 2016

KORAFI AKAN DIREBOBIN TIFA Daga Abdulmumin Sabo


koke zuwaga Dan majalissa mai wakiltar Daura tare da hukumar kare hadura ta karamar hukumar Daura.


Kamar yadda kowa yasani ne Titin da ya tashi daga Daura zuwa Katsina titine da akoda yaushe yake dauke da ababen hawa a dalilin cunkushe shi da akayi da makarantun da suka hada da GDSS Daura, GGSS Daura, GPSS Daura, General Hospital Daura, Daura main market, school of health technology Daura, Daura local government secretariat, Himma nursery and primary school Daura, quality assurance Daura zonal office duka wannan dana zano wurare ne na hada hadar jama'a uwa uba gata hanya ce ta zuwa state head quarter wato garin Katsina. Haka kuma kashi tamanin da biyar na Kasa ko yashi da yan tifa ke daukowa su kawo cikin garin Daura ta wannan hanya ne suke kawo shi.
Don haka nake kira ga Dan majalissar jiha mai wakiltar Daura hadi da hukumar kare hadura shiyyar Daura duk da jama'ar Daura da dama na yaba kokarinsa to anan ma yakamata ya dauki matakin kawo karshen wata matsala dake damun duk wani ma'abocin bin wannan titi (Daura to Katsina) wato matsalar nan ta yan Tifa masu debo yashi ko Kasa tinya batareda sun rufe yashi ko kasar da suka dauko ba wanda hakan yana matukar takurawa duk wani mai binsu abaya akan babur ko keke har masu motoci abin na shafarsu don haka Yakamata gwamnati ta lura da wannan matsala ta tuntubi kungiyar yan tifa don nemo mafita bawai sai ranar da hakan ya haddasa hatsari ba Allah ya kiyaye sannan a fara laluben hanyar magance wannan matsala.

Ina bada shawara da a umarci yan tifa da su rika rufe yashi ko kasar da suka daukowa da tamfal ko su rika yayyafa mata ruwa wannan zai rage matuka yashi ko Kasa da iska ke daukowa zuwa idanun masu abun hawa. Tuni a wasu jihohi ko birane ake amfani da wannan doka. Da fatan Dan majalisa Hon. Nasir Yahaya Daura tare da hukumar kare hatsura ta shiyyar Daura zasu duba wannan koke ameen.

No comments:

Post a Comment