Wednesday, 4 May 2016

KAMFANIN WUTA NA #PHCN, KUDIN WUTA SUKE KARBA KO KUDIN HAYAN GIDAJE ? Malam Mansur Halilu


 Ganin yadda al'umma suke kara fadawa cikin tsananin karancin wutar lantarki, a gefe guda kuma kamfanin nan na PHCN na cigaba da kara kudin wutar lantarki duk da cewar wutar lantarkin bata samuwa.

Inhar kudin da kamfanin na PHCN yake karba na wutar lantarki ne to ina wutar lantarkin? Inkuma kudin da suke karba na hayan gidajenmu ne, to sai sugayamana cewar ba #NEPA kadai aka sayar musu ba harda gidajen talakawa aka sayar musu shiyasa sukebi duk karshen wata suna karban kudin haya Ba'a bayan haka kuma jami'an ita wannan hukuma ta PHCN a duk lokacin da suka zo gida sukan buge da yin hira da matan mutane a maimakon aikin daya kawo su, wannan dabi'a na taimakawa matuka ga wadannan jami'ai masu neman neman matan mutane, bayan wannan matsala kuma ta magana da matan mutane akwai matsalar "karbar na goro" misali za'a kawo maka "bill" a tsakiyar wata a kuma baka wa'adin sati daya kachal!


Inajin wannan doka bata dace da kasarmu ba duba da irin yanayin tattalin arzikin mu. Yazama wajibi a duba wannan bangare na sha'anin wutar lantarki a Nigeria, idan har adalci ake nufi kuma CHANJIN da gaske ake.

No comments:

Post a Comment