
Thomas Manning ya zama mutumin farko a Amurka da
aka fara yima dashen zakari [penis transplant] a wata cibiyar lafiya ta Boston .
Dashe kuma ? Ah! Eh mana, amma bana shuka ba na
jijiyoyin mutum, ina nufin an bawa Thomas Manning sadakar al'aura (zakari).
Kai! Da gaske sadaka , ban gane ba? Kwarai kuwa, sadakar al'aura sakamakon
ciwon-daji daya jaza rashin al'aurarsa wacce aka yanke a asibiti shekaru 3 da
suka gabata.
A yanzu dai Thomas ya samu sabuwar al'aura wadda
zai iya yin fitsari da jima'i kamar yanda sauran mutane masu lafiya keyi , nan
da 'dan wani lokaci zai fara amfani da ita. Manning ya zamo mutum na 3 a duk
fadin duniya da aka tabayi ma wannan dashen zakari kuma aka samu nasara.
Likitoci 50 ne su kayi karo-karo wajen aikin dashen
sabuwar mazakutar Thomas wanda aikin ya dauki awa 15 ana fama domin ta zauna
daidai. Dashen kam ya kama sosai, domin kuwa an samu nasara, Thomas zai cigaba
more rayuwa da jin dadi kamar yanda sauran mutane masu lafiya suke yi.
No comments:
Post a Comment