Tuesday, 17 May 2016

Sanatan Daura Zone Ya Dauki Nauyin Koyawa Mata 3600 Sana’oi Tare Da Basu Jari


Sanatan Daura zone Engr. Mustapha Bukar fnim (madawakin Daura) ya fito da wani gagarumin shirin koyawa mata 3600 sana'oi tareda da basu tallafin jarin da zasu fara wadannan sana'u da zarar sun kammala amsar horo. wanda hakan zai basu  damar dogaro da kansu harma su koyama wasu. An kaddamar da wannan shirin koyan sana'a a garin ingawa bisa jagorancin senata mustapha Bukar wannan bukin kaddamarwa ya samu halartar manya manyan yan siyasar jihar nan musamman daga bangaren mata.


Sana'oin da za'a koyar dai sun hada da: Koyar da yadda ake yin sabulun wanka dana wanki, Man shafawa, Dettol, Air freshener, Hoda da Maganin kwarin da suka hada da sauro, Kuda, kyankyaso da sauran su da yadda ake kera murhu na zamani don magance yawan amfani da itace. Wannan sana'u dai wani kamfani da ya shahara wajen koyawa mutane sana'un dogaro da kai mai suna ICT Global plus Sanata Mustapha Bukar ya dauko hayarsu don su koyarwa mata musamman iyayen marayu dama mata marayu, zawarawa, mata masu karamin karfi da sauran ire irensu da suka fito daga mazabarsa ta Daura zone.



Wannan kamfani zai bayar da takardar shaidar kammalawa (certificate) ga dukkanin matan da suka amshi horo da zarar an kammala horar dasu. Wannan horaswar zata dauki tsawon wata daya ne a wasu kebabbun wuraren horaswar (training centers) guda uku a kowace karamar hukuma na kananan hukumomi goma sha biyu na Daura zone. Anyi kiyasin cewar wannan shiri zai ba mata  akalla 250 daga kowace karamar hukumar dake a Daura zone.


Mai bada wannan sanarwa Alhaji Hamisu Haruna Fadababban Daura kuma babban mai kula da dukkanin tsare tsaren harkokin siyasar Senata Mustapha Bukar yayi kira ga jama'ar Daura zone musamman matan da suka samu nasarar shiga wannan shiri da su tabbatar sun bada hadin kan da Yakamata don ganin anyi wannan shiri cikin nasara kamar yadda aka tsara shi wadanda kuma basu samu nasarar kasancewa cikin wannan shirin ba yayi kira garesu da su dan kara hakuri yanzu ne aka fara akwai tanade tanade makamantan wannan da dama da Sanata yayi ma al'ummar Daura zone tanadi.


No comments:

Post a Comment