Tuesday, 3 May 2016

Shin! Kuri'ar Ka Yan'cin Ka? by Comr Aliyu Mamman Sarki



A duk sadda da na tuna lokacin da nabi layi, na anshi takardar Kada kuri'a, na matsa wajen akwatin zabe na kada kuri'a ta, nikanji wani takaici yazo mani in kuma ji na kagara a Kara kada gangar siyasa.

Mafi akasarin wadanda muka zaba domin su wakilce mu a majalissun tarayya, to agaskia munyi zaben tumun dare. Domin suna wakiltar kansu ne kawai. Sun zame mana tamkar almajiran birni, babu kyuya babu biyan bukata.

Kullun sai kaji sunce suna Abuja, amma bama ganinin su suna fafutukar nemar mana hakkin mu a Zauren Majalissa. Sun tafi kawai yawon bude idanu dan kuwa duk badakalar da akeyi a zauren majalissa su idone kawai nasu.

Suna aikin me har wasu suka samu damar da  suka saka wasu ayyuka na yaudara da cin amanar kasa a mazabun su a cikin kasafin kudin wannan shekrar? Suna ina ne lokacin da ake karkatar da man fetur din da gwamnati ke bayar wa ya zuwa Kasuwannin bayan fage? Wace gudummuwa suka bada dan ganin cewa Shugaban Majalisar Dattawa,  Wanda keda hannu dumu-dumu a cin hanci da rashawa, da karya da cin amanar kasa ya bar shugabancin Majalisa? Wace gudummuwa suka bama Shugaba Buhari  a yaki da yake yi da cin hanci da rashawa da kuma ganin cewa ya kwato wa talakawa kudaden da mujarraban tsohuwar gwamnati sukayi awon gaba dasu?

Wane ayyukane suka kawo a mazabun su wa'anda zasu kara gina tattalin arzukin su?

Yaku Yan Majalissu ku tuna fa duk wadanda suke cikin ku suke kawo rudani a cikin kasar mu, da nufin su kawo ma Shugaba Buhari Cikas wajen gina Kasa, matsayin ku daya dasu, babu abinda suka fiku sai dai in kun maida kanku wadanda sukaje Abuja ci rani ko neman kudi. Ku tashi tsaye ku kare yancin kanku Ku kuma kare yancin talakawan da suka zabe ku. Ko Kuna goyon bayan su ne domin canjin da muka zaba ya gagara a aiwatar dashi? Ko kuna tsoron su ne? Kokuwa kuma akwai abinda kuke amfana dashi ku kadai wanda shike sa kuke bari anawa talaka yanda akaga dama.

Ya kamata ku hankalta, in bacci kukeyi to ku farka, dan kuwa kowa ya gane kune kusan fiye da kashi Tamanin cikin Dari na matsalolin Kasar nan.

Ku tsaya tsayin daka ku bama Shugaba Buhari hadin kai, kada ku zama butulu, dan sanin kowa ne in ba dan shi ba (Bihari), da dayawan ku bakuje inda kuke a yanzu ba. Kada ku yadda ace yayi maku Rana amma kunyi mashi Dare.

Ku tuna mulki ba akan ku aka fara ba, ba kuma akan ku za a kare ba. Kamar jiya ne aka dawo da dimokaradiyar duka, amma gaya yau har an shekara Goma sha Bakwai. Dayawa gasunan muna gani, babu kudin, babu mulkin, sannan, abin takaici babu mutunci a idon jama'a.

Ya ku Yan Majalissu ku aikata ayyukan Alkairi wadanda zamuyi alfahari daku  tun kafin dama ta kare maku. Da muna ganin Ku cikin talakawa, wajen daurin aure da wajen jana'iza, amma yanzu mun daina ganin ku, shin wai baku da gaskia ne kokuwa? Abokanan ku da aka sanku dasu tun ba mulki ba ko sisi yanzu mun bar ganin ku tare, kun canja sabbi, shin sunyi maku laifi ne?
Yan'uwanku ma mafi yawanci kun daina zuminci dasu duk dan dadin mulki. Ku tunafa mulki yana karewa sannan kuma akwai mutuwa, kowane dayan ku sai Allah ya tambaye shi.

Marokan Siyasa na dawo gareku. Abin mamaki kuma wai duk yadda wadannan yan majalissu suka ci amanar kuri'ar da muka basu, sai gaya wasu Maroka da za'a iya kiransu marasa buri, marasa aikinyi, marasa kishin kasa suna saka hotunan su a kafar sadarwa ta zamani suna masu kirari suna kara masu kwarin gwiwar rashin sanin darajar talaka. Shin dan Allah meyasa baku gaya masu gaskiayar cewa jama'a basa jin dadin wakilcin su? Meyasa Baku basu labarin irin zagin da jama'a keyi masu?

Ubangidanka ko dariya yayi sai ka sa hoton shi ka rubuta wai shi me adalci ne, idan ma da  Wani ya gaisa sai kasa hoto ka rubuta shi Adali ne. Wai angaya maku yanzu talaka yana bukatar ganin hotuna ne? Ni a gani na Talakawa suna so ne kawai suga kuri'ar su tayi masu amfani ne ta hanyar anfana da lagwadar dimokaradiya, cigaban tattalin arziki da samun ababen more rayuwa.
Aji tsoron Allah asan za'a mutu aje a amsa tambayoyi, sannan a tuna cewa in ma da rai, wata rana mulki zaya kare a dawo ma wadanda aka guda.

Comr Aliyu Mamman Sarki

No comments:

Post a Comment