Sunday, 15 May 2016

Karanta Sakamakon Taron Kungiyar Gwamnoni Yammacin Najiriya Dasu Gabatar a Kaduna


Taron kungiyar Gwamnonin Arewa maso Yammacin kasar nan yana ci gaba da gudana a Gidan Gwamnatin Jihar Kaduna a karkashin jagorancin Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari.
Taron wanda ya sami halartar Gwamnonin shiyyar, zai tattauna ne kacokan a kan harkar aikin Gona.

A jawabin shi na budewa, Gwamna Masari ya bayyana cewa an gayyato Kwamishinoni, Manyan Sakatarori da kuma Daraktocin Aikin Gona na jihohin da ke wannan shiyya.


Ya kuma kara da cewa, Shugaban Bankin Tallafawa Noma (Bank of Agric), da na Bankin Tallafawa wa Masana'antu da kuma na Bankin Tallafawa masu shigowa da kuma fitar da kaya kasashen waje za su gabatar da kasidu a wajen taron.

No comments:

Post a Comment