Gwamna Aminu Bello Masari yayi kira ga al'ummar Jihar Katsina, musamman masu kanana, matsakaita da kuma manyan Masana'antu da suyi kokarin cin gajiyar alfanun da Bankin tallafawa wa Masana'antu na Kasa (Bank of Industry) yake samarwa.
Gwamnan yayi wannan jawabi ne a yayin bukin bude ofishin reshe na wannan Banki da na nan Katsina.
Gwamna Masari ya kara da cewa Gwamnatin Jiha ce tayi Uwa kuma tayi Makarbiya wajen kawowa da kuma samar wa wannan Banki matsugunni domin al'ummar wannan Jiha su amfana ta bangaren habakawa tare da kafa sababbin Masana'antu.
Yace wannan dama ce da za ayi amfani da ita wajen sama wa mata da matasa ayyukan yi.
A nashi jawabin, Mai rike da mukamin Shugaban Bankin Mista Waheed Olagunju ya jinjina wa Gwaman Aminu Bello Masari domin jajircewa da yayi wajen ganin an kawo wannan Banki a Katsina domin karuwar al'ummar wannan Jiha.
Mista Olagunju ya tabbatar wa al'ummar wannan Jiha cewa kofar su a bude take, kuma yana kira gare su da kada suyi kasa a guiwa wajen shiga da kuma cin gajiyar shirye shiryen wannan musamman ganin ga shi an kawo shi har gida.
A karshen bukin bude ofishin, an sa hannu kan yarjejiniyar fahimta tare da aiki tare, tsakanin Gwamnatin Jihar Katsina da wannan Banki na tallafa wa Masana'antu.
No comments:
Post a Comment