Jahar Katsina
na daya daga cikin manyan Jahohi a yankin Arewacin kasar Nigeria ta fuskoki
daban-daban. Babbar fuskar da zamu dauka a wannan karon, itace fuskar Lafiya,
fuskar da wannan jaha tayi fice a ciki.
Daga kowacce karamar hukuma, akalla akan samu
Manya da kananan Asibitoci Goma (sama-ko-kasa da hakan). Sannan an wadatar da
wadannan asibitoci da kwararrun Likitoci da kuma Ma’aikatan Jinya da ke aiki ba
dare ba rana.
Duk da kokarin da gwamnatin Jiha keyi na
ganin ta gyara wannan fanni na Lafiya a fadin jahar, zamu iya cewa “Ana daure
gaba ana Kwance baya” ne, domin kuwa, babban bangaren da yafi kusan kowanne
bangare a cikin Asibiti na fuskantar kalubalen da ke haddasa mutuwar Majinyata
ba tare da sanin dalili ba a fadin Jihar. Dakin gwaji da nazarin Jini da
cututtuka “Laboratory”, shine daki mafi kusa da kusa da muhimmanci a dakunan
asibiti. Duk wata cuta wacce za’a yi nazarinta, akan yi nazarin ne a wannan
daki. Mafi akasarin cutukan da ake nazarinsu a wannan dakin sun shafi cutuka
dake yawo ko rayuwa a cikin Jini. Wannan Jarida ta CLIQQ MAGAZINE ta samu
bakuncin Buhari Shehu Faskari, wanda ya bayyana takaicin sa kan yadda ake yiwa
wannan Sashe rikon sakainar kashi.
“Ba’a dade ba a cikin jahar Katsina, aka samu
wani asibiti da ya sanyawa Wani Yaro Mara lafiya Jinin da ke ‘Karya Garkuwar
dan Adam (HIV).” Cewar Buhari Shehu Faskari. Ya ci gaba da cewa: “Da yawa daga
cikin ma’aikatan dake aiki a wannan sashi a asibitocin Jahar Katsina, basu
cancanta suyi aiki a sashen ba. Zaka ga mutum yayi karatu a Makarantar Kimiyya
da Fasaha (Polytechnics), inda aka basu horo don suyi aiki a Dakunan nazari na
Cemistry ko Biology a makarantun Sakandire, sune ake turawa dakunan nazari da
awon jinni na asibitoci.