Sunday, 5 February 2017

ASIBITOCIN KATSINA | KASHE MUTUM A LABORATORIES Daga Teburin Edita | Sani Hamza Funtua.

Jahar Katsina na daya daga cikin manyan Jahohi a yankin Arewacin kasar Nigeria ta fuskoki daban-daban. Babbar fuskar da zamu dauka a wannan karon, itace fuskar Lafiya, fuskar da wannan jaha tayi fice a ciki.

Daga kowacce karamar hukuma, akalla akan samu Manya da kananan Asibitoci Goma (sama-ko-kasa da hakan). Sannan an wadatar da wadannan asibitoci da kwararrun Likitoci da kuma Ma’aikatan Jinya da ke aiki ba dare ba rana.

Duk da kokarin da gwamnatin Jiha keyi na ganin ta gyara wannan fanni na Lafiya a fadin jahar, zamu iya cewa “Ana daure gaba ana Kwance baya” ne, domin kuwa, babban bangaren da yafi kusan kowanne bangare a cikin Asibiti na fuskantar kalubalen da ke haddasa mutuwar Majinyata ba tare da sanin dalili ba a fadin Jihar. Dakin gwaji da nazarin Jini da cututtuka “Laboratory”, shine daki mafi kusa da kusa da muhimmanci a dakunan asibiti. Duk wata cuta wacce za’a yi nazarinta, akan yi nazarin ne a wannan daki. Mafi akasarin cutukan da ake nazarinsu a wannan dakin sun shafi cutuka dake yawo ko rayuwa a cikin Jini. Wannan Jarida ta CLIQQ MAGAZINE ta samu bakuncin Buhari Shehu Faskari, wanda ya bayyana takaicin sa kan yadda ake yiwa wannan Sashe rikon sakainar kashi.

“Ba’a dade ba a cikin jahar Katsina, aka samu wani asibiti da ya sanyawa Wani Yaro Mara lafiya Jinin da ke ‘Karya Garkuwar dan Adam (HIV).” Cewar Buhari Shehu Faskari. Ya ci gaba da cewa: “Da yawa daga cikin ma’aikatan dake aiki a wannan sashi a asibitocin Jahar Katsina, basu cancanta suyi aiki a sashen ba. Zaka ga mutum yayi karatu a Makarantar Kimiyya da Fasaha (Polytechnics), inda aka basu horo don suyi aiki a Dakunan nazari na Cemistry ko Biology a makarantun Sakandire, sune ake turawa dakunan nazari da awon jinni na asibitoci.

“Ire-iren wadannan mutane bai kamata a same su suna aiki a Dakunan gwaji da nazari na Asibitoci ba, domin su [Technologst] ne kawai. Idan aka sanya su aiki a asibitoci, karshe sai su kasance suna samar da sakamakobn karya, ko kuma su sauya jinin mai lafiya da jinin mai wata cuta.

“Da yawan su na samun aiki a Asibitoci ne ta hanyar yin Aikin sa kai (Voluntary), ko kuma idan aka tashi tura aiki, mai makon a tura su Dakin gwaji da nazari na Makarantu, sai su samu hanya a tura su Asibitoci.”

Comr. Buhari Shehu Faskari sai kuma ya yi kira ga Hukumar Lafiya tare da bayyana hanyoyin da za’a bi don magance afkuwar wannan matsalar, inda yake cewa:

“Hukumar Lafiya ta Jihar Katsina ya kamata ta fara tantance dakunan Awo da Gwaji a asibitocin dake a fadin Jihar. Wannan tantancewar ne zai bada damar sanin dakunan awo da keda karancin kayan aiki, ko kuma wadanda SAM ! ba’a ma san da wanzuwarsu ba.

 
“Sannan Hukumar ta sanya kwamiti don yin bincike da fitar da sunayen sahihanan ma’aikatan da ya kamata suyi aiki a wannan daki, ta hanyar Tantance ma’aikatan daga matakin karatunsu”

Comr. Buhari Faskari ya ci gaba da cewa: “Wadanda ya kamata suyi aiki a dakin Awo da Nazari na asibitoci sune masu matakin karatu na: Medical Laboratory Assistant Medical Laboratory Technician Medical Laboratory Scientist “Duk wani karatun Lafiya ana yinsa ne a makarantu irin su: School of Health Technology Universities in Faculty of Medicine.

“Tantancewar da Hukumar Lafiya zatayi a bangaren dakin Awo a asibitocin Jahar zai magance sanyawa Marasa Lafiyan da basu-ji-ba-basu-gani-ba jini mai dauke da cutuka. Fitar da sakamako mara inganci, da kuma sanadiyyar rasa rayuka.” Daga karshe Comr. Buhari Shehu Faskari ya bukaci Hukumar Lafiya ta Jahar Katsina dama Gwamnatinm Jiha akan hukunta duk wanda aka kama ba tare da izinin yin aiki a dakunan awo na awo na asibitoci ba. “Sannan ya kamata Kwamitin Lafiya na Majalisai Jaha su samar da doka wacce zata kare wannan kuduri na samar da ingantaccen tsari a dakunan awo na asibitoci don kare asarar rayuka a fadin jihar”

CLIQQ Magazine na daukar ra’ayoyin makaranta musamman Yan Asalin Jahar Katsina dama makwaftan jaha. Burin wannan Magazine ta isar da sakon Al’umma ga shuwagabanninta tare da wayarwa Al’umma kai akan ayyuka da manufofin Gwamnatin Jaha daman a Tarayya baki daya. Karshen Rahoton kenan…
Sani Hamza Funtua |
EDITA. 07032183026

 

No comments:

Post a Comment