Tuesday, 27 September 2016

FITACCIYAR MARUBUCIYA | ZAHRAU BABA YAKASAI TA RASU


Marigayiya Zahrau Baba Yakasai


Shahararriyar Marubuciyar Littattafan Hausa, Zahra'u Baba Yakasai yau Talata 27 ga watan Satumba, 2016. Ta rasu bayan yar doguwar rashin lafiya wacce ta fara tun kusan 9 ga watan March, 2016, sauki ya samu gareta har sai wajajen 16 ga watan Satumba, 2016.

 Marigayiya Zahra'u Baba Yakasai, matar Tijjani Shuaibu Ringim, ta rasu tabar Yaya da dama.Daga cikin littattafan daga Rubuta akwai su:

1- Matar Yayana
2- Bagidajiya
3- Mugun Miji
4- Hamshakiya
5- Kanin Mijina
6- Salon So
7- Furen Kan Juji
8- Auren Kaddara
9- Uwar Miji ko Kishiya?
10- Nafi Karfin Kishiya
Da sauransu.

Cikakken tarihin Marubuciyar zaizo maku nan bada jimawa ba. Muna rokon Allah ya jikanta ya gafarta mata, Ya Sa Aljanna ce makomarta Amin.

Rahoto:- Sani Hamza Funtua.

2 comments: