Friday, 10 February 2017

Gwamna Masari Ya Kai Ziyarr Duba Ayyukan Tsanyoyi Tare Da Hon.Tanimu Sada


Mai Girma Gwamnan Katsina Rt. Hon Aminu bello Masari ya kai ziyarar gani ido domin duba ayyukan tsanyoyi da a ke aikin su a yau Asabar da misalin karfe 2:26AM.

Mai ba Gwamnan Shawara akan ayyuka na musamman Hon. Tanimu Sada ya baiyana hakan a shafin shi na Facebook akan yanar gizo-gizo.

Tanimu Sada ya kara da cewa wadan nan ayyuka sun zama wajibi don gane da ambaliyar ruwa da unguwuyin ke fuskanta a lokacin damina. Karanta cikakken labara da Tanimu Sada ya saka a yanar gizo.  

“A Daren yau Asabar 11th /2/2017 da misalin karfe 2:26 am Maigirma gwamna yasamu zua duba ayyukan tsanyoyi da gwamnatinsa takeyi domin shawo kan ambaliyar rua dake addabar wasu unguwanni dake cikin garin katsina.

Wuraren daya samu zua sun hada da Bakin Babbar Asibitin katsina, sai kuma babbar tsanya da tataso daga gadar nayalli zua gadar adeleke, Sai kuma tsanya wace ta taso daga titin hamada carpet zua bakin makarantar family sports, da kuma tsanyar da tataso daga titin shararrar pipe zua bakin Asibitin kofar kaura. Maigirma gwamna ya nuna gamsuarsa ga yadda ayyukan ke tafia.

Dafatan Allah yayi mana jagoranci yayi ma gwamna jagoranci yataimaki jamaar jihar katsina”.

 

No comments:

Post a Comment