Saturday, 18 February 2017

Kadara Tariga Fata Daga Comrade Abubakar Ismail kankara

Ita hidima ta rayiwar Dan Adam, Allah ne ke tsarata duk dacewa shi Dan Adam Mai guri ne da Kuma fatan yasama abunda Zuciyarsa take bukuta a kodayaushe.

Aduk lokacin da wani guri nasa yacika saikuma ya kara hangen wata damar wacce zatakasance gurinsa. Daka wanan lokacin saikuma tunanin maharsada da masoya yazama wani bangaren tunanin Dan Adam.

Dazaran tunanin makiya da maharsada yarinjaye tunanin masoya Sai Kuma wasu matakan hada Kariya takowace hanya domin Samun nasara akowace hidima ta rayiwar.

Itakuma rayiwar takasance rigar aro sabilida duk matsayin Dan Adam baya iya sayanta Saidai ya ingantata da abunda Ubangiji Allah yabashi ikon samar Mata.

Anma duk da haka al'uma sukan Mata cewa Ubangiji Allah shikebadawa Kuma shike karba Aduk lokacin dayaso, Sai su ringa alakanta dukan wani alamari gawani Dan Adam na nasarar ko rashin nasarar.

Duko dacewa Hausawa sunce murnar mutuwa murnar banzace, adan haka banga dalilin dazaisa mukasance muna murna akan wata jarabawa ko rashin nasara da wani ko wata Dan Adam yasama akan wata hidamar rayiwarsa.

Kuma abunda yafi dacewa dazukatarmu shine mukasance masu farinciki da fatan Alkhairi GA dukan Wanda yasama wata Dama da nasara Akan wani guri nasa.

Saboda haka yakamata muzamto mutane masuyin tsaptataciyar "Siyasa" muzamto marasa gabba ko harsada GA Wanda Allah yaba nasara ko rashin ta. Mu dauka cewa Allah shikebadawa Kuma shike karba Aduk lokacin dayaso.
Kuma mu zamto yan'uwan juna tafuskar Adalci a harkokinmu na yauda kulum

Shuwagabanin mukuma kuzamto masu Adalci GA Al'uma, masu shawara da Al'uma, masu tunanin Al'uma, masu Gina Al'uma.

Zan Kuma yi amfanida Dawanan damar Don mika sakon jaje GA Rt Hon Sabi’u Ibrahim Muduru, tsohon kakakin majalisar dokokin jahar Katsina akan wanan jarabawa da Ubangiji Ya jarabeshi da ita, Allah yaka ikon juriya da hakuri Kuma Allah yakawo wata Dama Mai girman anan gaba.

Akarshe Kuma zan mika sakon farinciki da taya murna GA sabon kakakin majalisar dokokin jahar Katsina wato Rt Hon Abubakar Yahaya kusada abisa GA runjaye dayasamu a majalisar. Kuma Allah yakare yakuma bada ikon yin Adalci.
Allah yasa ayi mulki cikin koshin lafiya yasa agama lafiya.

Asalam

 

 

No comments:

Post a Comment