Tuesday, 7 February 2017

Labari Da Tumin Sa | APC A Malumfashi Ta Dakatar Dan Majalissar Tarayya Hon. Babangida Mahuta-Karanta Dalili

Hon. Babangida Mahuta
Shugabannin jam'iyyar APC na kananan hukumomin Malumfashi da Kafur sun tsaida wakilinsu a majalissar tarayya.

Shugabannin jam'iyyar Alh. Samaila Garba Sabuwar Kasa da Alh. Yahuza Musa sunce wakilinsu Hon. Babangida Ibrahim Mahuta ya furta wasu kalamai a wajen taron da akayi na jam'iyyar na batanci ga gwamna, rashin ladabi da biyayya ga shugabanni inda wadanda sun saba ma manufofin jam'iyyar.

Haka kuma sunce baya halartar duk wata hidima data shafi ofishin jam,,iyyar na yankin

Alh. Yahuza Musa Dayi yace Hon.Babangida baya darattasu da kuma girmamà dukkan shuwagabanni.

Tuni suka mika takardar ga mataimakin shugaban jam'iyyar na yankin Funtua Bala Abubakar Musawa inda suke neman ya mika ta zuwa jiha da kuma tarayya.

Cliqqmagazinehausa ta samu wannan labari daga shafin Umar Bala Kofar Sauri a Facebook na yanar gizo.

Idan zaku tuna a can baya da aka yi taron Shuwagabannin APC na arewa maso yamma a nan jihar Katsina, Hon. Babangida Mahuta bai samu halartar wannan taro ba.
Haka zalika ma Mai Girma Gwamna Aminu Bello Masari yayi kira da mutanen yankin da su kuma su shirya tsakanin su domin kiyaye Baraka. Amma ga dukkan alamu Baraka ta riga ta faru, sai kuma a tari gaba.

 

No comments:

Post a Comment