Wednesday, 1 February 2017

Karanta Cikakken Jawabin Alh Umaru TATA Daya Yi A Oficin PDP Na Katsina


JAWABIN MAIGIRMA ALH. UMAR ABDU TSAURI (TATA) A WURIN TARON KARBA TARE DA KADDAMAR DASHI DA MAGOYA BAYAN SHI CIKIN JAM’IYAR PDP. RANAR TALATA, 31/01/2017, A BABBAN DAKIN TARO NA SAKATARIYAR JAM’IYAR PDP DAKE GARIN KATSINA, A JIHAR KATSINA.

Jama’a Assalamu Alaikum!

Na farko ina godia ga Allah madaukakin Sarki da ya hada mu a wannan wuri babba mai albarka a wannan rana ta talata. Cikin taimakon Allah yau a cikin Jam’iyar PDP, a cikin sakatariyar PDP tare da manya manya jami’an ta. A cikin ikon Allah yau lema ta bude gani a karkashinta nike gudanar da ayyukan taimakon ubangiji.

Ina neman taimako a yafe mani bin protocol, wannan ba komai yasa ba sai don ganin an dade kuma ga lokacin sallah na karatowa, don in gaggauta ko munyi abinda ya kawo mu don mu samu muje mu bada farali.

Na farko ina son Al’umma su sani, ni da nazo wannan wuri na zo ne domin kauna da biyayya. PDP dama cen Jam’iya tace, kuma har yanzu Jam’iya tace, koda na tafi APGA zuciyata tana cikin PDP. Allah cikin nashi iko, yau na dawo gida, kuma gidan ya karbe ni, ba karba kadai akayi mani ba, an kuma karrmani. Lokacin da akayi shawarar ayi wannan taro, kwata-kwata awa 24 da suka wuce, na ce aikuwa babu lokacin da zan shirya, in kuma sanar da al’umma ta. Amma aka ce inzo da mutane na ko ya ya suke. To chairman ga mutane na, Allah cikin nashi iko na kawo gare ka. Mu masoya ne, kuma ina tabbatar maka mu masu biyayya ne ga jam’iya.

Kowa in akace Tata, abinda ake kallo shine abu biyu ; Na farko shine za’ayi fada, Na biyu da ance Tata, za’ace Gwamna yake nema. To ni nazo nan a matsayin mai neman sulhu. Fada in anyi shi an yishi akan kuskure kuma ya riga ya wuce. Na biyu, naji Hajia Binta Dubai tana gabatar dani a Matsayin Dan takarar Gwamna, a’a ni din nan nazo ne a matsayin Yaro na Jam’iyar PDP. PDP ita keda yancin tura ni inda ya dace. Yau in PDP tace inje inyi takarar Kansila a Dutsinma ‘A’, to gobe zanje in fara takarar kansila. Amma ina da yakinin adalai ne akan teburin nan, sun san kansila already akwai kansila wanda suna court so muke su dawo da kujerar su, inshaa Allah. Sun sani, already muna da chairman, shima suna court so mukeyi kujerar shi a dawo mashi da ita. Amma kowa ya sani Katsina bamu da Gwamna. Saboda haka anan, in yanzu cewa nayi so nike muje mu shiga wancen gidan to dama ai mu muka gina shi. Maigirma Chairman, kamar yadda na fada maka ni mai biyayya ne umurni nike Jira, in kace mu tafi wallahi zamu tafi yanzu.

Nazo wannan wuri domin in gaya maku da yardar Allah Katsina sai mun karbo ta. Katsina sai ta dawo wannan gidan da yardar Allah. Duk wanda ke wannan wurin ya gode ma Alla, tunda suka shiga wancen gidan, sun shige shi ne a karkashin Darajar wani, amma su basu da darajar data isa ta kaisu wancen gidan. Mu tsaye muke da kafafunmu. Ayyukanmu sun ishe mu. Yau in akace Jihar Katsina sai ance Umaru Musa Yar’adu (Allah ya jikanshi), to Umaru Ya tafi, Umaru ya dawo. In akayi maganar Jihar Katsina, sai ance Ibrahim Shehu Shema, to Shema ya tafi, ga Tata ya dawo.

In aka duba duka bangarorin guda biyu, ina da kafa gidan Umaru, ina da kafa gidan Ibrahim. Ina mai tabbatar maku ayau da aka mika ni ga hannun Chairman, inda ba don biyayya ba, da sai ince nafi kowa halatta a cikin jam’iyar PDP.

Al’ummar Jam’iyarmu dake wannan wuri, aikin dake a kanmu babba ne. na fada na maimaita, kar mu koma mu kwanta muce shirme suke yi. To in su shirme suke yi in muka kwanta to kaga mu kwance muke. Da wanda ke tsaye yana shirme da wanda ke kwance yana barci, ni ina ganin wanda ke tsaya yana shirmen nan ya fi mai baccin nan. Kar mu dauka cewar nasara ajiye take kawai tashi za’ayi a dauke ta. A’a, Allah akwai aiki a gaban mu. Yau cikin taimakon Allah, ni dai ina gaya maku na shirya aikin nan kuma gashi na fara. Saidai ina so ku sani, shi aikin Katsina, ba aiki bane na raggo, shi aikin Katsina, ba aiki bane ba na marowaci, aikin Katsina ba aiki bane ba na matsoraci, kuma aikin Katsina ina mai tabbatar maku sai mun yishi.

Yau a cikin Jihar nan, bayan Jam’iya ta PDP a Jam’iyance, nine na biyu da mutanen nan kullum suke so suga sun wulakanta. Da kunji ance za’ayi taro a karbi wasu mutane, cewa akeyi Jama’ar Tata ne, ni kuma Jama’ata gasu nan, wadancen dama ba nawa bane. To na fada masu da babbar murya, in sun karbi wasu ba Jama’ata bane, in sun karbi wasu ba yan Jam’iyar PDP bane, tarkace suka karba, aikin banza suka karba, kuma akanshi zasu kare.

Na sha fadi, ban taba ganin mutumin kirki ba irin dan Jam’iyar PDP, saboda PDP itace Jam’iyar dake mulki, amma kaga dan jam’iyar PDP bashi da ko kwabo amma ya fito yayi aikin don saboda jam;iya. In akayi maganar akida, wallahi akida tana cikin PDP, su wadancen da suke cewa su yan adawa ne, kuma adawa tana tafiya da aqida, to ba gaskiya bane. Suna adawa ne saboda bakin ciki. Mu kuwa yau in akace muna adawa, to muna adawa ne saboda bakin cikin ganin halin da al’umma ta ke ciki. Kudurin mu shine, ta ina zamu bi mu tsamo al’umma daga halaka.

Yau shekara biyu Kacal da hawan mulkin su amma komi ya canza. Ni da ana kamfen na sayi tirelloli na shinkafa, na sayi tirelloli na taki, na sayi tirelloli na masara mun bayar kyauta gudummuwa ga al’umma. Amma ina mai tabbatar maku kafin wani zaben yazo, kasar nan sai an nemi wanda zai sayi tirellar masara ya bada kyauta kasar nan an rasa. Domin ni da nasayi masara akan naira dubu hudu(4,000) nayi kyauta da ita, yau buhun Masara yana Naira dubu goma sha Shida (16,000). Kudin da na sayi tireller dasu, yau sai anyi da kyar zasu sayi mani buhu 50 dasu. Ana rayuwar duniya haka?

Sun ce mu barayi ne, in ma mu barayi ne to munyi sata mai amfani, domin mun yi satar kuma mun gina al’umma. Sun ce su basu sata shi yasa ma muke yunwa. To kenan da gaskiyar dake kashewa, da satar dake amfanawa, wace tafi amfani ga al’umma. Yau in gaskiyarsu tana da amfani to su take amfana, mudai bamu ga amfaninta ba ga al’umma. Kuma wallahi har gaskiyar mun fisu. Jarabawace ta Allah, ya karba daga garemu ya basu, kuma don ya nuna ikonshi, don ya nuna mu wadanne iri ne, suma al’umma ta gane wadanne iri ne.

Yau suna son su kawo Ibrahim Shehu Shema a cikin Jihar Katsina don su wulakanta shi. Yau ina son duk wanda ke wannan wuri ya sani, ana cewa Tata da Shema ba su shiri, wanene ya fada muku? Wallahi ni ina yima shema addu’a ta alkhairi, kuma duk inda zan tsare mutumcin shema dama na taba yi, kuma a sanya ni kan hanya zanyi da yardar Allah.

Yau duk wanda ya wulakanta shema ai mu ya wulakanta. Ina bada hakuri da wanda ke son shema da wanda bai son shema anan, ina so ku sani, dukkanin mu Jam’iya ta hada mu, kuma Jam’iyar nan ayau itace rigarmu itace wandon mu, kuma tana tafiya da wani abu da ake cema symbol, alama kenan, to alamar daukakar PDP a jihar Katsina ba kowa bane Ibrahim Shema ne, ko anqi, ko anso maganar kenan. To yau duk wanda ya karya Ibrahim Shema a cikin Jihar Katsina, wallahi mu aka karya. Saboda haka duk wanda zai iya bada gudummuwa akan Allah ya hana su samun nasara akan wannan danyen aiki, to ya bayar. PDP itace gare mu, PDP itace gaba, kuma akan PDP inshaa Allah shirye nike inyi duk abinda ya dace. Saboda haka ni bani gaba da kowa, bani fada da kowa, tarbiyyar gidanmu itace rungumar al’umma. Ban taba cewa sai mai so na zan amfanar ba. Buri na shine Allah ya bani abinda zani yi, in ya bani to zanyi, in kuma banyi ba, to bani dashi. Wallahi ban taba kwana da kowa ba a raina. Na shigo Jam’iyar PDP don in bada gudummuwa ta samu daukaka.

Ina so ku sani, a cikin masu taimakona, bangarori biyu ke taimako, na farko Jam’iyar nan da nike cikinta itace ta farko dake taimako na. Wanda ke yi mani jagoranci mai mukami ne a cikin Jam’iyar nan. Wadanda ke mani Jagoranci a Local Government, babu inda na samu mai gudummuwa ko mai Jagoranci ba tare da yarda ta Jam’iya ba. Ance a wancen lokacin nayi kuskure ban rungumi Jam’iya ba, to yau gani na rungumeta.

Wanda duk zayyi magana yace Tata dan takara ne to ya sani, Tata dan PDP ne ba dan Takara ba, Takara bata zo ba. A cikin PDP kuma Tata dole ya samu masu Jagoranci da zasu dora shi kan hanya. To suwa zasu dora shi kan hanya inba wadanda suka san Jam’iyar PDP ba? To ina so ku sani duk wanda yake ganin nayi ba daidai ba akan na rungumi yan jam’iya suna Jagoranta ta a cikin jam’iya, ina so ya gane cewa, hausawa sun ce, Sai da Dan gari akan ci gari.

Na biyu akwai Matasa dake karkashin su, matasan nan akwai kungiyoyi daban daban, saidai a cikin su, akwai kungiyar da ake kira Tata Dawo Dawo, kungiyar nan tana aiki tukuru tsakanin ta da Allah. Akwai wuraren da takai wanda ni ban isa in kai ba. Saboda haka ina maku godiya Allah ya saka da Alkhairi.

Ina so Dawo Dawo ta sani, in dai dawowa ce to gani na dawo. Bance ku canza sunan kungiya ba, amma ku sani, wannan aiki kun yishi, kuma kun dora ni akan hanya, sannan akan hanyar nan akwai jagorori, ina rokonku kuyi masu biyayya. Babu Jayayya tsakanin Tata Dawo Dawo da sauran kungiyoyi, da kuma jagoranci dake karkashin Alhaji Umar Makauraci. Karkashin shi kuke, kuyi masu biyayya, in kuka yi mashi ni kun karrama ni.

Daga karshe ina so inyi kira ga Jam’iya, mu adalci muka sani. In akayi mana adalci wallahi duk inda ake zaton bamu iya zuwa za’a aike mu kuma zamu je. Yau Alh. Salisu Majigiri, Allah kai yaba shugabancin Jam’iyar PDP, Saboda haka ina so ka sani, kaine zaka tsaya gaban Allah kayi bayanin yadda kayi jagorancin ka, babu wanda zai iya tsaya maka a matsayin lauya. Saboda haka tsakaninka ne da Shi zaka yi.

Yau ita ce rana ta biyu dana taba haduwa da Majigiri, amma ranar dana fara ganinshi, nayi magana dashi, sai nake mamakin don mi abubuwan da ake fada mani basu yi daidai da mutumin dana gani ba? Akwai adawa cikin PDP yanzu haka a Jihar Katsina. Kuma adawar nan ba komai ya jawota ba rashin fahimta ne. Babu dalilin da zai sanya ace yanzu muna court saboda shugabancin Jam’iya. Shi dai shugabanci Allah ke bada shi ba alkali ba. Yau in ka kwace shugabanci daga hannu Majigiri wa zaka ba? Shi zabi Allah ake barwa shi, ba tilas ake yin zabi ba. Majigiri Allah ya zabe shi, to mu kuwa yi mashi biyayya. In ka cire Majigiri ba mu san cikin rikincin da za a sanya mu ba. Saboda haka Maigirma Chairman, nazo ina yi maka biyayya, kuma zan taimakeka akan wannan shugabanci da kake yi.

Ku kuma sauran Al’umma ina so ku sani, in kun shirya fada to gani, saidai wannan fadan ina tabbatar maku mai zafi ne. Yau a Jihar Katsina bamu da ko Councilor. Zamu tunkari Gwamnatin da ita keda sama, kuma ita keda Jiha, duk wani mukami da ake nema yana hannunsu. To a siyasa abinda aka koya mani, wanda duk keda Gwamnati ya tsera maka a wurin zabe. Saboda haka wannan aiki ne babba sai mun dage. Ni dai ina shaida maku wallahi na shirya.

Da duniya nike so baku gani na nan. An bani Minister don in bisu nace bani so, an bani Deputy Governor tun ina takara nace wallahi gwara a bani C-Class, saboda baiyi daidai da abinda nike bukata ba. Ni so nike in kai ga al’umma in taimake ta. Ba wurin boyo nike nema ba don in sami abinda zan sa aljihu. Talauci da Arziki duk na Allah ne. Yau idan na rasa na barwa Allah. Banzo nan don in yaudari wani ba. Buri na shine ta ina zan taimaki Addinin Allah ya sami gata, ta ina zan kawo gudummuwa ga talaka har ya samu saukin rayuwa.

Ba zan taba neman Gwamna ba sai in kun ce, duk ranar da kuka ce in fito, to zan fito, amma ba zan iya ba sai kun taimake ni. Ni kadai bani iyawa. Amma da yardar Allah in muka hadu, zamu kai duk inda ba’a zato.

Ina godiya ga manyan baki, ina godiya ga jam’iya data karrama ni. Ina rokon yadda Allah ya hada mu anan, Allah ya sake hada mu a gidan gwamnati 2019 inshaa Allah.

Na gode kwarai Allah ya saka da alkhairi.

 

 

No comments:

Post a Comment