Za mu so ka gabatar mana da kanka?
Bissimillah Rahamanin Rahim. Sunana Tanimu Sada Sa’ad, haifaffen
cikin garin Katsina ne. Yanzu haka ni ne mai baiwa Gwamna Aminu Bello Masari
shawara kan ayyuka na musamman da kuma ayyukan da suka shafi Majalisar Dokoki
ta Jihar Katsina.
Duk da kai ne mai baiwa gwamna shawara kan ayyuka na musamman, sai ga shi ka
kafa wannan kungiya ta House-To-House Youth Awareness, ko wadanne dalilai ne
suka jawo hankalinka ka kafa ta?
Babban dalilin da yasa na kafa wannan kungiya ta House-To-House,
kungiya ce ta kowa da kowa madamar mutum matashi ne. Mun lura cewa matasa Jihar
Katsina suna bukatar wata hanya wadda za su rika haduwa da juna domin kara
fadakar da junan su da ba da shawarwari da kuma sanin manufar inda gwamnatin
Aminu Bello Masari ta dosa saboda gwamnatinsu ce. Ba kuma sai dan jam’iyyar APC
ba ce, duk matashin Katsina muddin yana da muradin shiga to muna maraba da shi
domin ba da gudumuwarsa ta ci gaban Jihar Katsina.
Idan na fahimce ka, ba lalle sai dan Jam’iyyar APC ba kadai?
Kwarai kuwa. Shi yasa muka sanya mata wannan suna na House To
House Youth Awareness Forum. Gwamnati dai Jamiyyar APC ce, akwai wuri da ake
taka rawa ta siyasa da akwai kuma wurin da ba a sanya siyasa. Misali akwai
bangarori guda uku wadanda mai girma gwamna bai kawo siyasa kwata-kwata a cikin
su, kamar bangaren ilmi, lafiya da kuma bangaren da ya shafi ci gaban al’ummar
Jihar Katsina. Mai girma gwamna bai duba bangaren siyasarka ko wata akidarka, zai
tsaya tsayin daka.
Wannan shi ya sanya mu mukarrabanshi muke koyi ala kulli halin.
Muka ce ina ne ya kamata mu baiwa wannan gwamnati gudumuwa; saboda a tarihin
siyasa Jihar Katsina ba a taba samun gwamnatin da take tare da zunzurutun
matasa ba irin wannan gwamnatin, shi ne muke son mu fadakar da matasa da su
fito su nuna gwamnatin ta su ce, maimakon matashi ya yi ta korafin cewa
gwamnati ba ta kaza da kaza, to taho ka shigo. Koda kana wata kungiyar
bukatarka kuma taka ma nan.
Wannan yasa muke kira ga sauran kungiyoyi da su taho mu tafi tare
domin ganin hakarmu ta cinma ruwa, domin samun wakilci a cikin kungiyarmu.
Wadanda ba su da rijista mun ce su zo za mu dauki nauyin yi masu rijista domin
su zamanto cikakkun ‘ya’yan kungiya. Har ila yau ina kara jadadda cewa ba
kungiya ce ta siyasa zalla ba, kungiya ce mai son ci gaban al’ummar Katsina
gaba dayansu, musamman matasa. Domin Gwamnan Jihar Katsina mutum ne na al’umma,
kowane dan jihar yana da hakki akan sa. Shi yasa muke son yin amfani da wannan
kungiyar domin kara jawo hankalinsu a ciki, saboda ko adawar zaka yi ta na
ma’ana.
Kungiyata ba mun kafa ta ba ne dan azo ayi banbadanci ko fadanci
ba, muna son a rika fadin gaskiya da nusar da gwamnati inda ba ta yi daidai ba,
domin kawo ci gaba mai dorewa a Jihar Katsina.
Ta wadanne hanyoyi ne za ku rika gudanar da ayyukanta?
Alhamdulliahi. Yanzu dai kusan wata guda da rabi da kirkirarta, ba
mu kai ga fara yin komai ba. Amma mu nan muna shirye-shiryenta domin fara
ayyukanta wadanda insha Allahu matasa za su shaida nan gaba kadan.
Wannan kungiya ta kudiri aniyar karade lunguna da sakon Jihar
Katsina baki daya kamar yadda ka bayyana. Wane kokari take na ganin kowanne
matashi ya ba da gudummuwarsa ga wannan tafiya?
Farko dai wannan kungiya ta hada da duk wani mai ba gwamna shawara
yana cikinta, kuma kowane mai ba gwamna shawara yana da Karamar Hukumar da ya
fito. Haka kuma muna nan muna shirya wasiku ga ‘Yan Majalisar Dokoki na Jihar
Katsina, domin mika masu goran gayyata domin su ba da wakilinsa guda daya a
karamar hukamar da ya fito. Kuma a halin yanzu muna ci gaba da tuntuba domin
ganin sakon ya isa gida-gida a ko’ina a fadin jahar nan. Kwanan nan za mu fara
kai ziyarar ban girma ga iyayen kasa domin bayyana ma su manufar kungiyar domin
su sanya mana albarka.
Ranka ya dade ganin wannan ayyuka da ka bayyana suna bukatar masu
gida rana. Ta wadanne hanyoyi ne House-To-House Youth Awareness Forum ke samun
kudin shiga domin gudanar da ayyukanta?
Wannan takudin tambaya mai kyau ce. Amma kasan ba ka saurin fiddo
kayan yakinka da sauri haka. Amma muna da abokan arziki da mu kanmu tanan muke
samun kudin da muke tafiyar da ita.
Gwamnan Jihar Katsina yana kokarin yin adalci ga matasan jiharsa
baki daya. Wanne kokari kenan ku ke yi don sanya mata cikin wannan tafiya?
Kwanakin baya na ce masu ba gwamna shawara kafataninsu suna ciki,
kuma a cikinsa akwai mata da dama. A koda yaushe kuma suna bakin kokarinsu na
jawo mata a cikin wannan kungiya, kuma mun nemi hadin kan kungiyoyi da muka
tace su, wasu muka ga suna da tsarin shugabanci a kowace Karamar Hukuma, muka
ce su zo mu hadu mu kai sakon inda ya kamata. Akwai kungiyoyin daliban gaba da
sakandire da wadanda suka gama da ma wadanda ke cikin makaranta mun gayyato su.
Wasu na ganin kamar kishiya ce ga wata kungiya wadda kusan
manufofinku iri daya ne. Me za ka ce akan haka?
Kungiyarmu ba ta fada da kowace kungiya. Gurinmu shi ne ta zo mu
tafi tare; Saboda akoda yaushe ina fadin ban ce ta mu tafi ta kowa ba, ko ba
kungiyoyi ba ne. Sai dai ita kungiyarmu kungiya ce bude, kuma mun ce kowa ya zo
su kuma sun ce dan APC kadai ya zo madamar alheri ka zo da shi ko gudumuwar ci
gaba ka kawo.
Daga karshe, wane kira gareka ga al’ummar Jihar Katsina da masoyan
Gwamna Aminu Bello Masari?
Dan Allah don annabi mu yi wa kanmu adalci; idan ba ka san abu ba,
ka shigo ka san shi, sannan a guji yada labari marar tushe balle makama. Domin
ina tabbatar maka Mai Girma Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari
(Dallatun Katsina) ba ya da wani tunani illa ya ga ya sauke nauyin da Allah ya
dora masa. Mutum ne mai son ya ga ya yi adalci kuma ba ya kyamar jama’a gurin
shi a kullum ya ciyar da Jihar Katsina gaba. Don haka ina kara yin godiya ga
al’ummar Jihar Katsina na irin goyan baya da soyayyar da suke nuna ma sa.
No comments:
Post a Comment