Monday, 13 February 2017

LABARI: Donald Trump Zai Yi Magana Da Buhari Ta Waya


Fadar shugaban kasar Amurka-White House tace shugaban Amurka Donald Trump zai yi Magana da shugabannin Najeriya da Afirka ta Kudu ta wayar tarho yau Litinin.

Tattaunawar da shugaba Trump zai yi da takwaransa na Najeriya Muhammadu Buhari yana daukar hankali saboda da ba a ji daga Buhari ko kuma ganinsa a bainar jama’a ba tunda ya tafi jinya London ranar goma sha tara ga watan Janairu.

Sabon shugaban kasar Amurka bai yi Magana a kan Afrika ko kuma batutuwa da suka shafi Afrika ba tunda ya hau karagar mulki watan da ya shige. Babu wani bayani daga fadar White House kan abinda shugabannin zasu tattauna a kai. http://bit.ly/2lBLPnW

Domin Karin Bayani: www.voahausa.com


 

No comments:

Post a Comment