Monday, 24 October 2016

Talla | Shin Ko Ka Ziyarci Hamdala Medicine Store [Gidan 'Yan-gantatcin Magani]

Hamdala Medicine Store
 
Shin ko kasan Hamdala Medicine Store ya shahara wajen kawo 'yan-gantatcin Magun-guna na lafia masu kyau?

Shin ko kasan Magun-gunan Hamdala Medicine Store na da farashi mai rahusa?

Saturday, 22 October 2016

ADDINI | Rikicin Masallacin Sultan Bello Kaduna: Da Sauran Rina A Kaba


Tun bayan dakatarwar da aka yi wa limamin masallacin Sultan Bello da ke Unguwar Sarki Kaduna, Shaikh Balale Wali, kawunan malaman da ke da hannu a sha’anin Masallacin ya rabu wurin nada wanda zai ci gaba da limanci.

Shaikh Ahmad Mahmud Gumi da wasu da suka kira kansu da almajiran Shaikh Abubakar Gumi sun fitar da sanarwar cewa ba su yadda da nada Babban Sakataren Jama’atul Nasrul Islam, Dakta Khalid Abubakar Aliyu a matsayin sabon limamin masallacin ba. Sun bayyana cewa hanyoyin da aka bi wajen zaben sa sun saba wa koyarwar Alkur’ani da Sunna.

Friday, 21 October 2016

Talla | Karanta Yadda Za Ka Amfana Da Kanfanin "ALI EXPRESS TRAVEL & TOWERS" .


Ina Masu tafiya aikin Umrah, Hajji, Dubai da kuma harkokin kasuwanci zuwa kasashen waje?
Ina masu sun zuwa asibiti a kasashe irin su India?
Ina dalibai masu Neman visa don tafiya karatu kasashen waje?

To ga wata dama ta samu a saukake domin kamfanin nan mai suna ALI EXPRESS TRAVEL & TOWERS ya kasance yana samar da visa ga jama'ar jihar Katsina da kewaye don saukake masu wahalar samun Visa.

Saturday, 15 October 2016

WATA MAGANA TA DAWO,WATA MAGANA TA TAFI! Daga Real Bahaushe

Duk da a satin nan na shiga cikin hidimomi sosai masu yawan da na dade ban shiga irin su ba,amma hakan duk bai hana ni dan lekowa kafofi da kofofi ba da shan abin kofunan labarun da ke karakaina ba.

Al'amurran daga ciki akwai batun maganganun Uwargidan Shugaba Buhari,tasiri ko suka ko yabonsu duk abin duba ne,inda na ga da yawan masu sharhi sun kasa kallon bangarori,su dai fatansu su karawa Borno dawaki.


Kamar yadda maganganunta suka zo da mamaki,gaskiyar magana ba a yi tunanin za ta aikata haka ba.Amma mijinta don bai yi wa wahalallun jam'iyya aiki ba wannan ba laifi ba ne,muddin dai sun cancanta kuma sun fi wahalhalun,me ya kawo maganar tsoron bore ko tada jijiyoyin wuya a nan,ko kila ta rasa wasu daman maki ne kuma?


Martanin Shugaba Buhari ga maganar sun sa an sake jin kunya a kasar nan,wasu na cewa ya raina darajar mata, wasu kuma na nuna ya bi sahun gaulan nan Donald Trump wai ya yi batsa,daga baya dai ya nuna wasa yake yi maganar tana kula da falo da kicin da dakunansa kadai!Amma me zai sa ba zai ce haka ba?kwancewa miji zane a kasuwa irin wannan!Gaskiya ko ma mene ne ta saki bakinta da yawa;domin duk abubuwan tsegumi ne ba shawarwari ba,ai yanzu an daina yayin irin wannan duniyar,kuma kowa ya sani dole ne Buharin ya yi irin maganganun nan.

Friday, 14 October 2016

Dalhat Usd Danja -:|:- BAKORI DA DANJA

Alhamdullillah Tabbas Social Media ta zama Tsani da mukan Iya Isar da kokenmu wajen da Mukeso yaje, Social media tana taka mahimmiyar rawa wajen Ganin cigaban Al'umma da kake rayuwa dasu Dole muyima Allah Godiya da wannan Ni'imar Ta Social Media daya kawo mana.

A Sakamakon Koken Gyaran Islamiyya da Abokin gwagwarmaya Wato Rabiu Yakubu Mila yayi Yanzu haka DanMajalisa mai wakiltar Bakori/ Danja wato Hon. Amiru Tukur Yayi Alkawarin Gina Aji guda biyu a wannan Islamiyyar kuma Tuni Har an Hada Rabi'u Yakubu Mila da Wanda Zai Jagoranci Aikin!

Monday, 10 October 2016

MALUMFASHI-:|:- AN KAMA TUKUR YANA SA MAGANIN BERA A NIKA


A yau mutanen bayan Nitel suna cikin wani tashin hankali,sakamakon wani mummunan al'amari da yaso ya faru, wani mutum mai suna TUKUR wanda yake zaune a bayan nitel din yaje injin nika da niyyar sayen dusa, bayan yabada kudin dussar sai yasa hannun sa aljihu ya fiddo maganin bera ya barbada a cikin gari na jama'a,.cikin hukuncin Allah sai Mai nikan mai Suna MALAM SANI ya gansa. lokacin daya kama TUKUR da shinkafar beran nan take aka sanar da jami'an tsaro dake MTD MLF.

Thursday, 6 October 2016

Kamal Nasir Nasiha: GYARAN ASIBITIN FUNTUA | GYARAN GANGAR AUZINAWA NE

"Batu akan gyaran asibiti, hakika mu munyi zaben tumun dare, chanjin da muke tunanin gaba daya munyi kumumuwar munyi da sunan anyi canjin gwamnati to ba shine muke gani a yanzu ba."
Muhammad Kamal Nasir Nasiha, sakatare ne na kungiyar Arewa Youth Development, ya kasance cikin masu yin sharhi akan abubuwan da suka shafi mulkin gwamnati da kuma batutuwan dake faruwa a kowane bangare dake cikin kasar nan musamman Jihar Katsina. A wannan karon, Muhammad Kamal Nasir Nasiha ya ziyarci Wakilin CLIQQ Magazine inda ya dauki batu akan Gyaran Asibitin da Gwamnatin Aminu Bello Masari takeyi na General Hospital Funtua.
Kamal Nasiha ya ke cewa: "A zahirin gaskiya, idan ka dubi wannan asibiti ta General da aka ce ana anayin gyara, to ni a tunanina ba wani gyara bane gilla Gyaran Gangar Auzinawa. An Gina wannan asibitin tun a lokacin Murtala, a lokacin an ginashi ne da zummar cewa zai iya biyawa mutanen Funtua bukatunsu na wancan lokacin.

Wednesday, 5 October 2016

General Hospital Funtua: DOKAR ZIYARA KARFE 3 TA DAWO

A safiyar yau Talata, 5 ga watan 10, 2016. Kofar shiga Babban Asibitin garin Funtua [General Hospital] ya cika da mutane sakamakon hanasu Shiga da jami'an kula da Kofar shiga cikin asibitin sukayi.



Wannan ya biyo sabuwar dokar da dama can akwaita amma aka banzatar da ita, wato dokar ziyara ta karfe Uku na Rana zuwa Karfe Biyar na yamma na ranakun Aiki da kuma karfe Sha Biyu na Rana zuwa Biyar na yamma a ranakun Asabar da Lahadi. Sabo da rugujewar dokar a da ya sa duk Jama'ar da ke amfani da wannan asibiti sabawa da zuwa ziyara ko wane lokaci, amma dawo da dokar a dai-dai lokacin da ake ganin dokar bata dace tayi aiki ba ya sanya masu kula da marasa lafiya cikin Rudani da kuma nuna rashin goyon bayansu da maido da dokar.

Tuesday, 4 October 2016

DALIBAN FUNTUA DAKE JAMIAR UMYUK SUN KOKA DA SHUWAGABANNIN YANKIN

Da yawa daga cikin daliban dake karatu a jami'ar Umaru Musa Yar'adua dake Jihar Katsina (UMYUK), sun koka kwarai akan rashin tallafin da shuwagabannin yankin nasu Ke basu.
Mai magana da Yawun Daliban kuma P.R.O, Comrade Bashir Funtua, ya nuna bakincikinshi akan yadda shuwagabannin dake shugabantar yankin na Funtua sukayi watsi da su alhalin ko wane yanki na taimakawa daliban yankin.

KORAR RAHAMA SADAU | AN KASHE MICIJI NE BA A SARE KAI BA!!!


Bayan korar da hukumar MOPPAN reshen Jihar Kano ta yi wa Rahama Sadau daga harkar fina-finai, wata bakar kura ta lullube zauren fina-finan, inda wasu ke ganin ba ita kadai yakamata a kora ba, domin akwai iyayenta da kakanninta da yakamata a ce tuni an daina jin duriyarsu. Misali, ba tun yau aka fara irin wannan munanan dabi'u ba, domin Sani Musa Danja tuni ya jima yana yin kwatankwacin halayenta a industiri. Koma kan Ali Nuhu sanannen abu ne ya shahara wajen aika-aika sawa'un a fina-finai ne ko a wajensu. Bai jima ba, hotuna suka rinka yawo na irin lalata da yake yi da yan kudu. Haka abin yake ga Adam A Zango wanda yana daga cikin wadanda suka sabbaba lalacewar tarbiyyar matasa, ta hanyar mummunar shiga da sauran munanan halaye.

Ba wai ina goyon bayan Rahama Sadau ba ne, ko kadan, lalle na yi matukar farin cikin wannan kora duk da abin zai iya zama basaja. Sai dai korafin da nake, idan har za a kori Rahama Sadau wacce muka jima muna rubuce-rubuce akan lalle sai an dakatar da ita sakamakon mummunar shiga da daraktoci ko firodusoshi suka rinka umartarta, to wajibi ne a kori Ali Nuhu akan irin fasikanci da yake yadawa. Amma ba adalci ba ne ita a kore ta a bar iyayenta da kakanninta a fagen iskanci. Wani abu ma da ba a gane ba, ita ma wannan abin gada ta yi daga gurinsu, amma sai ta wuce gona da iri domin ne!arwa kanta karin matsayi da masoyi da wadanda za su taya ta domin fasikanci.

Har kullum abin da muke fada, tsarin fina-finan Hauda na yanzu, ya sabawa addini hatta na Kiristanci, da al'adun Hausawa. Mu Hausawa ne, bayan nan kuma daliban da muke nazarin harshen Hausa da al'adunsu a matakai daban-daban, babu inda muka taba karanta irin wannan karuwanci da iya shege da fitsara. Bal ma, a al'adun da muka sani, yau idan har yarinya ta zama karuwa, to nesantar garinsu take yi ma, amma sai ga shi yan fim a gidajen iyayensu suke abin da suke so. A irin wannan halin kuma a zo a ce wai za a yi Film Village, har aka samu wani shashasha, wanda a da muke kyautata masa zato saboda himmarsa da kwazonsa, musamman idan muka tuna rubuce-rubucensa na baya, da fina-finansa, irinsu Munkar da Salma-Salma-Duduf, ya yi rubutu mai taken KANWA TA KAR TSAMI...... inda ya ci mutuncin malaman Musulunci har ya rinka ambatarsu da aktocin fina-finan Hausa, ina nufin Bala Anas Babinlata. Yanzu gaya mini darasin da fim din ka na Salma-Salma-Duduf yake nunawa! Fim din da aka yi shi a gida guda har aka gaya! Yakamata mutane suna tunani kafin su yi magana, amma wauta da jahilci gami da sakarci ba za su haifar musu da komai ba face kaskanci.

Na'am, a cikin yan fim akwai wadanda muke kyautatawa zato, muke musu kallon dattijai, irinsu wane da wane. Wajibi ne a tsaya a tsaftace harkar, domin idan ba haka ba za su ci gaba da cutar da Musulunci, su cutar da al'adunmu da harshenmu, su cutar da Kasar Kano.

Ibrahim Garba Nayaya.
Ibrahimba183@gmail.com
02/10/2016.


Monday, 3 October 2016

JAMIAN SSS SUN KAMA MATASHI A MALUMFASHI KAN RUBUTU A FACEBOOK

Matashi Salisu Saminu Musa Ya Shiga Hannun Jami'an Hukumar Fararen Kaya Wato SSS Sakamakon Yin Rubutu a Shafinshi Na Facebook yana Bayyanawa Mutane Hanyar da Zasu Shiga Kungiyar Book Haram.

Salisu Saminu Musa Malumfashi


Wakilinmu na CLIQQ Magazine dake a garin Malumfashi, Ismail A Sanda, wanda ya tabbatar mana da afkuwar lamarin ya shaida mana cewa Jamian tsaron sun shiga Unguwar Tudun Bala da misalin karfe Uku a garin na Malumfashi. Jami'an sun je da Motoci kirar Helux guda Uku.

Matashi Salisu Saminu Musa, ya rubuta a shafin shi na Facebook kamar haka: "Kasan Yadda Zakayi Idan Kana So Ka Shiva Book Haram" sannan a kasan wannan rubutun ya rubuta adireshin yanar gizo kamar haka: "www.is.com".

Rubutun da Saminu Yayi


Jami'an tsaron dai sunyi amfani da na'urar gane inda mutum yake (GPS) wajen gano inda Salisu Saminu Yake, sannan suka yi amfani da lambar wayarshi wajen haduwa dashi. Mazauna unguwar sun shaida da faruwar lamarin inda wani mai shayi ya ce Har wayarshi suka karba don binciken lambar ta Salisu.

Tunda jami'an suka tafi dashi Har yau ba'a San inda suka kaishi ba kasancewar ba'a San daga inda suka fito ba.

CLIQQ MAGAZINE
07032183016

Saturday, 1 October 2016

A HUKUNTA RAHAMA SADAU

Bayan fitar bidiyon fitaccen mawakin nan Clasiq, wanda ya dauka tare da jarumar fina-finan Hausa Rahama Sadau. Wannan bidiyo dai ya jawo CeCe-kuce a cikin al'ummar Hausawa, inda Har wasu ke ganin cewa ya zama dole mahukuntan kamfanin fina-finan su dauki matakin gaggawa don ladabtar da ita.

Clasiq ya Goya Rahama Sadau


A cikin Bidiyon dai, Rahama Sadau ta cire kunyarta ta diyar Hausawa, sannan ta cire koyawar addinin Islama, inda ta baje jiki tana rungumar mawakin Clasiq da kuma Nawa bayanshi da sauransu.

Clasiq da Rahama Sadau sun rike hannu suna tafiya


Wasu daga cikin jaruman daga cikin jaruman da suke ganin ya zama dole a hukuntata sun dauki shiri yin hakan ta hanyar rubutawa a takarda tare da daukar Hoto suna dorawa a kafafen sadarwa don tabbatar da rash in kyautawar jarumar.

Dan Wasan Hausa: Nura yana nuna takardar a Hukunta Rahama Sadau.

 Rahama Sadau tayi five wajen Fina-finan Hausa, inda daga bisani ta koma fina-finan Kudancin kasar nan (Nigerian Film). A wata hira da jarumar tayi, ta nuna cewa tana sha'awar fina-finan Indiya, tana kuma sa ran fara daukar shirin nan bada jimawa ba idan damar hakan ta samu.

YANCIN KASA NE | BA YANCIN KAI BA.


©Sani Hamza Funtua.
.
Zai zama abin yaudara idan aka ce kowane dan kasa yayi murnar samun 'yancin shi shekaru hamsin da shida da suka wuce. Dan Nigeria [In Person], tun daga shekarar 1960 zuwa yau, bai samu cikakken 'yanci daga masu madafun iko na kasa da wajen kasa ba.

A wannan daya ga watan October, 1960, kasarmu Nigeria ta samu 'yancin zama da gindinta, 'yancin zama a karkashin mulkin 'yayanta, 'yancin rubuta kundin tsarinta duk da cewa kaso kusan 50 Nada nasaba da irin kundin tsarin turawan da sukayi mana mulkin mallaka Kafin zuwan wannan ranar.An tsara dokoki tare da shimfida 'yancin d'an Kasa, daga cikinsu akwai; 'yancin Rayuwa, 'yancin tafiye-tafiye, 'yancin mallakar wuarare ko ababe, 'yancin yin zabe ko a zabeka, 'yancin fadar albarkacin naki da sauransu. Sai dai, Har zuwa yanzu, tsawon shekaru hamsin da shida, dan kasa bai samu 'yanci ba, a rubuce akwai, amma a aikace wannan 'yancin ba nashi bane.

Dan kasa a yanzu, bashi da 'yancin fadar albarkacin bakinshi, koda kuwa abida zai fada ba cin mutunci ko batanci bane, ma damar abinda zai fada Gaskiyane, to bashi da wannan 'yancin. Da zaran ka fito kafafen watsa labarai ka fadi ra'ayinka, Kafin ka koma gidanka, jami'an tsaro sun zagaye shi, kana isa za'a jefa ka cikin mota a kulle ka a magarkama kamar wanda ya shekara yana yin fashi da makami. Fadar albarkacin baki ya zama jarfa a kasar Nigeria, da yawa kance: "Tun farko da ba'a kaga wannan dokar ba inhar ba za'ayi amfani da ita ba.

Ina daya daga cikin wadanda aka taba tauyewa hakkin fadar albarkacin baki, kwanaki Uku da yini daya ina kulle a magarkama tare da wasan da suka shahara a fashi da makami. Wani daga cikinsu yake sanar dani, shekarunsa Uku da rabi a gidan yari. Wani yace bakwai, wani biyar da sauransu. Laifukansu Nada yawa, wani fyade yayiwa karamar yarinya, wani sata yayiwa matar abokinshi, wani akace dilan kwayoyine, wani kuma sun kashe wani don karbe mashin dinshi, wani sun je fashi Har suka kashe dan sanda, da sauransu. Ni da aka kaini da laifin fadar albarkacin baki, ni da aka tauyewa hakki na 'yancin magana, 'yancin fadin ra'ayi, an kulle ni tare da Ire-iren wadannan mutane. A nan ma kadai, 'yanci Nawa aka tauyemin?

Ko a cikin Nigeria, Jihar Katsina ce mai muni wajen kama mutanen da fadin ra'ayinsu, a wata daya baya ta kama kusan mutane hudu, maban-banta ra'ayoyi, masu 'yancin fadin ra'ayoyinsu. Amma gwamnati ta fauce wannan 'yancin nasu. Jahohi da yawa na Fama da wadannan Matsalolin, dan kasa bashi da 'yanci, an hana mashi yanci ta kowace fuska.

Ni a wajena, 'yancin fadar Albarkacin baki ko ra'ayi shine babban 'yanci a wajena, don dashine zan Gina sauran 'yancin Nawa. Tunda an tauye shi lallai bani da 'yanci Kenan. Kasarmu Nigeria ta samu 'yanci daga Turawan mulkin mallaka. Amma mu 'yan kasar Nigeria mun rasa namu 'yancin daga masu Mulkarmu na Farar Hula.