©Sani Hamza Funtua.
.
Zai zama abin yaudara idan aka ce kowane dan kasa yayi murnar samun 'yancin shi shekaru hamsin da shida da suka wuce. Dan Nigeria [In Person], tun daga shekarar 1960 zuwa yau, bai samu cikakken 'yanci daga masu madafun iko na kasa da wajen kasa ba.
A wannan daya ga watan October, 1960, kasarmu Nigeria ta samu 'yancin zama da gindinta, 'yancin zama a karkashin mulkin 'yayanta, 'yancin rubuta kundin tsarinta duk da cewa kaso kusan 50 Nada nasaba da irin kundin tsarin turawan da sukayi mana mulkin mallaka Kafin zuwan wannan ranar.An tsara dokoki tare da shimfida 'yancin d'an Kasa, daga cikinsu akwai; 'yancin Rayuwa, 'yancin tafiye-tafiye, 'yancin mallakar wuarare ko ababe, 'yancin yin zabe ko a zabeka, 'yancin fadar albarkacin naki da sauransu. Sai dai, Har zuwa yanzu, tsawon shekaru hamsin da shida, dan kasa bai samu 'yanci ba, a rubuce akwai, amma a aikace wannan 'yancin ba nashi bane.
Dan kasa a yanzu, bashi da 'yancin fadar albarkacin bakinshi, koda kuwa abida zai fada ba cin mutunci ko batanci bane, ma damar abinda zai fada Gaskiyane, to bashi da wannan 'yancin. Da zaran ka fito kafafen watsa labarai ka fadi ra'ayinka, Kafin ka koma gidanka, jami'an tsaro sun zagaye shi, kana isa za'a jefa ka cikin mota a kulle ka a magarkama kamar wanda ya shekara yana yin fashi da makami. Fadar albarkacin baki ya zama jarfa a kasar Nigeria, da yawa kance: "Tun farko da ba'a kaga wannan dokar ba inhar ba za'ayi amfani da ita ba.
Ina daya daga cikin wadanda aka taba tauyewa hakkin fadar albarkacin baki, kwanaki Uku da yini daya ina kulle a magarkama tare da wasan da suka shahara a fashi da makami. Wani daga cikinsu yake sanar dani, shekarunsa Uku da rabi a gidan yari. Wani yace bakwai, wani biyar da sauransu. Laifukansu Nada yawa, wani fyade yayiwa karamar yarinya, wani sata yayiwa matar abokinshi, wani akace dilan kwayoyine, wani kuma sun kashe wani don karbe mashin dinshi, wani sun je fashi Har suka kashe dan sanda, da sauransu. Ni da aka kaini da laifin fadar albarkacin baki, ni da aka tauyewa hakki na 'yancin magana, 'yancin fadin ra'ayi, an kulle ni tare da Ire-iren wadannan mutane. A nan ma kadai, 'yanci Nawa aka tauyemin?
Ko a cikin Nigeria, Jihar Katsina ce mai muni wajen kama mutanen da fadin ra'ayinsu, a wata daya baya ta kama kusan mutane hudu, maban-banta ra'ayoyi, masu 'yancin fadin ra'ayoyinsu. Amma gwamnati ta fauce wannan 'yancin nasu. Jahohi da yawa na Fama da wadannan Matsalolin, dan kasa bashi da 'yanci, an hana mashi yanci ta kowace fuska.
Ni a wajena, 'yancin fadar Albarkacin baki ko ra'ayi shine babban 'yanci a wajena, don dashine zan Gina sauran 'yancin Nawa. Tunda an tauye shi lallai bani da 'yanci Kenan. Kasarmu Nigeria ta samu 'yanci daga Turawan mulkin mallaka. Amma mu 'yan kasar Nigeria mun rasa namu 'yancin daga masu Mulkarmu na Farar Hula.
No comments:
Post a Comment