Tuesday, 4 October 2016

KORAR RAHAMA SADAU | AN KASHE MICIJI NE BA A SARE KAI BA!!!


Bayan korar da hukumar MOPPAN reshen Jihar Kano ta yi wa Rahama Sadau daga harkar fina-finai, wata bakar kura ta lullube zauren fina-finan, inda wasu ke ganin ba ita kadai yakamata a kora ba, domin akwai iyayenta da kakanninta da yakamata a ce tuni an daina jin duriyarsu. Misali, ba tun yau aka fara irin wannan munanan dabi'u ba, domin Sani Musa Danja tuni ya jima yana yin kwatankwacin halayenta a industiri. Koma kan Ali Nuhu sanannen abu ne ya shahara wajen aika-aika sawa'un a fina-finai ne ko a wajensu. Bai jima ba, hotuna suka rinka yawo na irin lalata da yake yi da yan kudu. Haka abin yake ga Adam A Zango wanda yana daga cikin wadanda suka sabbaba lalacewar tarbiyyar matasa, ta hanyar mummunar shiga da sauran munanan halaye.

Ba wai ina goyon bayan Rahama Sadau ba ne, ko kadan, lalle na yi matukar farin cikin wannan kora duk da abin zai iya zama basaja. Sai dai korafin da nake, idan har za a kori Rahama Sadau wacce muka jima muna rubuce-rubuce akan lalle sai an dakatar da ita sakamakon mummunar shiga da daraktoci ko firodusoshi suka rinka umartarta, to wajibi ne a kori Ali Nuhu akan irin fasikanci da yake yadawa. Amma ba adalci ba ne ita a kore ta a bar iyayenta da kakanninta a fagen iskanci. Wani abu ma da ba a gane ba, ita ma wannan abin gada ta yi daga gurinsu, amma sai ta wuce gona da iri domin ne!arwa kanta karin matsayi da masoyi da wadanda za su taya ta domin fasikanci.

Har kullum abin da muke fada, tsarin fina-finan Hauda na yanzu, ya sabawa addini hatta na Kiristanci, da al'adun Hausawa. Mu Hausawa ne, bayan nan kuma daliban da muke nazarin harshen Hausa da al'adunsu a matakai daban-daban, babu inda muka taba karanta irin wannan karuwanci da iya shege da fitsara. Bal ma, a al'adun da muka sani, yau idan har yarinya ta zama karuwa, to nesantar garinsu take yi ma, amma sai ga shi yan fim a gidajen iyayensu suke abin da suke so. A irin wannan halin kuma a zo a ce wai za a yi Film Village, har aka samu wani shashasha, wanda a da muke kyautata masa zato saboda himmarsa da kwazonsa, musamman idan muka tuna rubuce-rubucensa na baya, da fina-finansa, irinsu Munkar da Salma-Salma-Duduf, ya yi rubutu mai taken KANWA TA KAR TSAMI...... inda ya ci mutuncin malaman Musulunci har ya rinka ambatarsu da aktocin fina-finan Hausa, ina nufin Bala Anas Babinlata. Yanzu gaya mini darasin da fim din ka na Salma-Salma-Duduf yake nunawa! Fim din da aka yi shi a gida guda har aka gaya! Yakamata mutane suna tunani kafin su yi magana, amma wauta da jahilci gami da sakarci ba za su haifar musu da komai ba face kaskanci.

Na'am, a cikin yan fim akwai wadanda muke kyautatawa zato, muke musu kallon dattijai, irinsu wane da wane. Wajibi ne a tsaya a tsaftace harkar, domin idan ba haka ba za su ci gaba da cutar da Musulunci, su cutar da al'adunmu da harshenmu, su cutar da Kasar Kano.

Ibrahim Garba Nayaya.
Ibrahimba183@gmail.com
02/10/2016.


No comments:

Post a Comment