A safiyar yau Talata, 5 ga watan 10, 2016. Kofar shiga Babban Asibitin garin Funtua [General Hospital] ya cika da mutane sakamakon hanasu Shiga da jami'an kula da Kofar shiga cikin asibitin sukayi.
Wannan ya biyo sabuwar dokar da dama can akwaita amma aka banzatar da ita, wato dokar ziyara ta karfe Uku na Rana zuwa Karfe Biyar na yamma na ranakun Aiki da kuma karfe Sha Biyu na Rana zuwa Biyar na yamma a ranakun Asabar da Lahadi. Sabo da rugujewar dokar a da ya sa duk Jama'ar da ke amfani da wannan asibiti sabawa da zuwa ziyara ko wane lokaci, amma dawo da dokar a dai-dai lokacin da ake ganin dokar bata dace tayi aiki ba ya sanya masu kula da marasa lafiya cikin Rudani da kuma nuna rashin goyon bayansu da maido da dokar.
Wakilin CLIQQ Magazine dake a Garin na Funtua, Sani Hamza Funtua, ya isa bakin kofar asibitin, inda ya taras da cinkoson mutane suna kokarin shiga amma Abu ya faskara. Ya samu zantawa da wasu daga cikin mutanen inda wata mata take cewa:
"Mun San cewa dama can akwai wannan doka, amma Sam a yanzu bai kamata a kawota ba. Ya kamata gwamnati ta sani cewa muna cikin halin babu da talauci, mu dake kai ziyara ga Mara lafiya mune ke zuwa mashi da abinci ko kudin da ake bukata a asibitin. Wanda Ke kula dashi a ciki, ba lallai bane ace yana da kudi, dole muna zamu kawo da safe, rana da kuma dare. To yanzu an sa doka akan sai karfe Uku, wannan ba adalci bane".
Wani dattijo kuma yake cewa: " Kaduba ka gani, yanzu diyata ce bata da lafiya, amma sun hanamu shiga wai kamar basu yarda bata da lafiya ba. To kusan haka suke yiwa kowa, da Mara lafiya da mai lafiya duka ba'a barinsu shiga Cewar wai ziyara suka kawo. Idan har ana so wannan doka tayi aiki, to a sanya mutane masu sanin mutuncin mutane a bakin kofar ta yadda zasu rika tausayawa mutane, amma ka duba yadda suke ture mutane. Wannan 'yar sandan har cire Bell tayi, kowa zata duka Oho".
Wakilin namu ya shaida mana yadda mutane sama da Ashirin zuwa Talatin suka taru a kofar shiga amma aka hanasu wucewa. Da yayi kokarin zantawa da MD na asibitin hakan bai yiyuba, illa ma MD din yace:
"Sauran asibitoci karfe Hudu ne, don haka bazamu canja wannan doka ba.".
Babban asibitin Funtua dai shine asibiti mafi Girma a garin na Funtua, inda daga garuruwa daban-daban makwafta da garin ke kawo marasa lafiya don a dubasu. Mahukuntan asibitin dai sun yanke hukuncin maido da wannan doka ta ziyara karfe 3 kwatsam a lokaci daya, inda mutane suka nuna rashin jin dadinsu akan dawo da wannan doka musamman yadda kasa ke a cikin halin babu.
No comments:
Post a Comment