Friday, 14 October 2016

Dalhat Usd Danja -:|:- BAKORI DA DANJA

Alhamdullillah Tabbas Social Media ta zama Tsani da mukan Iya Isar da kokenmu wajen da Mukeso yaje, Social media tana taka mahimmiyar rawa wajen Ganin cigaban Al'umma da kake rayuwa dasu Dole muyima Allah Godiya da wannan Ni'imar Ta Social Media daya kawo mana.

A Sakamakon Koken Gyaran Islamiyya da Abokin gwagwarmaya Wato Rabiu Yakubu Mila yayi Yanzu haka DanMajalisa mai wakiltar Bakori/ Danja wato Hon. Amiru Tukur Yayi Alkawarin Gina Aji guda biyu a wannan Islamiyyar kuma Tuni Har an Hada Rabi'u Yakubu Mila da Wanda Zai Jagoranci Aikin!

Tabbas ko wacce Al'umma na bukatar Shugaba mai Saurin jin koken Talakawanshi da shawarwari Kamar Yanda Hon. Amiru Tukur yakeyi Nasha Bashi Shawara kuma ya dauka Mungode Hon Allah Ya saka maka da Alheri! Ya kuma baka ikon cigaba da Ayyukan da sukafi wadannan Ameeen!

Comrade Dalhat Usd Danja
Coordinator Masari Awareness network (MAN)
Coordinator Masari Enlightenment Forum
Coordinator Karadua Concern media link!
14-10-2019

No comments:

Post a Comment