Tun bayan dakatarwar da aka yi wa limamin masallacin Sultan Bello da ke Unguwar Sarki Kaduna, Shaikh Balale Wali, kawunan malaman da ke da hannu a sha’anin Masallacin ya rabu wurin nada wanda zai ci gaba da limanci.
Shaikh
Ahmad Mahmud Gumi da wasu da suka kira kansu da almajiran Shaikh Abubakar Gumi
sun fitar da sanarwar cewa ba su yadda da nada Babban Sakataren Jama’atul
Nasrul Islam, Dakta Khalid Abubakar Aliyu a matsayin sabon limamin masallacin
ba. Sun bayyana cewa hanyoyin da aka bi wajen zaben sa sun saba wa koyarwar
Alkur’ani da Sunna.
Sun
ci gaba da cewa ba a tuntubi wadanda ya kamata ba kafin nadin. Sannan ana
yunkurin karya tsarin da Shaikh Abubakar Gumi ya kawo a masallacin. Kuma an yi
hakan ne don a haifar da rikici a masallacin.
Shaikh
Ahmad ya zargi Dakta Khalid da cewa yana kulla makirci don ganin ya sami wannan
limancin ta hanyar zuga wasu daga cikin ‘yan kwamitin masallacin don su kawo tarnaki
ga koyarwar Malam. Daga nan ya kuma bayyana cewa Dakta Khalid Abubakar ba dan
makarantar Shaikh Abubakar Gumi ba ne.
Shaikh
Ahmad Mahmud Gumi ya roki mutanen da ke Sallah a Masallacin da kada su dauki
doka a hannunsu saboda a cewarsa maganar tana hannun hukuma.
A nashi martanin, shugaban Majalisar Limamai da Ladanai ta
Jihar Kaduna, Shaikh Usman Abubakar Baban Tune, ya musanta nadin Dakta Khalid
Abubakar Aliyu a matsayin Limamin Masallacin tare da nunar da cewa riko aka ba
shi kafin a warware matsalar da ake fama da ita.
Baban Tune ya ce ba su ji dadin abin da ya faru a
masallacin na Sultan Bello ba kuma tuni suka bayyana wa Limamin Masallacin,
Shaikh Balele Wali rashin hakurin da ya nuna kana suka tabbatar wa Shaikh Ahmad
Mahmud Gumi cewa bai yi laifi ba da ya jagoranci Sallar Idi a ranar Babbar
Sallah.
Ya kuma bayyana cewa Masallacin Sultan Bello yana
karkashin kulawar Mai Martaba Sarkin Zazzau ne da kuma Mai Alfarma Sarkin
Musulmi, don haka su suke da ikon cire Liman da kuma nada wani.
Ya nunar da cewa laifin da Liman Balele Wali ya aikata, ba
daidai ba ne. Amma tuni ya rubutar takardar ba da hakuri. Don haka ya ce ba a
sauke Shaikh Balele Wali ba har sai Sarkin Zazzau ko Sarkin Musulmi ya sanar da
cire shi.
Baban Tune ya jaddada cewa ba zai yiwu a bar masallacin ba
tare da jagoranci ba, shi ya sa aka nada Dakta Khalid Abubakar a matsayin wanda
zai kula da Masallacin har zuwa lokacin da za a warware matsalar da ake ciki.
Ya bayyana Dakta Khalid Abubakar Aliyu a matsayin wanda ya
cancanta da wannan riko musamman kasancewarsa daya daga cikin wadanda suke ba
da karatu a wannan Masallaci.
Asali: Leadership hausa
No comments:
Post a Comment