Sunday, 12 June 2016

#BUHARIYYA_GASKIYA_FA_ANAJI_A_JIKA (mutane nacin #TAFASA) Ameer Mahmud Dan'amarya


Kimanin shekara 6 kenan rabon da inyi arba da mutane suna cin #TAFASA, #KAWURI, DA #DINKIN, amma bana fa abin harma ba'a magana duk wata gona data fitar da ciyawar #TAFASA jama'a sun tsinketa sun cinyeta,  duk wata bishiya dake fitar da ganyen dinkin ko qawuri jama'a sun tsinketa sun cinye tasss.

Allah muna qara tuba agareka idan laifi mukai Allah kaji qanmu kayafe mana laifukanmu.

Mutane suna cikin wani hali , akwai guraren danasan anakai kokon azumi bara har ragowa ake jama'a wasu ko kallon gurin basayi, amma bana fa banan ce, jama'a tururuwa suke dan shankoko har fasa bokitin suke saboda kokarin suga sun samu.


Lallai yakamata gomnati tayi duba da tausayi na irin yalin da mutane keciki tabada lallafi na gaggawa, ta kuma yi kokarin bullo da dabarun da zasu taimaki jamaa dan rage masu radadin talauci.

Abangaren masu hannu da shuni suma suna da rawar dazasu iya takawa wajen taimakama Mutane da abinci musamman acikin wannan wata na Ramadan wanda ake nunnunka ladan aikin alkhairi....
Ya hayyu ya kayyum ya zuljalalu wal ikram muna tawassuli da azumin damukeyi da alfarmar wannan wata na Ramadan me albarka kakawo mana sauki acikin rayuwarmu tayau da kullum ka yassara ma ussirat alaina,

Ya Allah kataimaki shuwagabannin Mu kabasu ikon yimana adalci

Ameen
12-06-2016

No comments:

Post a Comment