Da yawa daga cikin daliban dake karatu a jami'ar Umaru Musa Yar'adua dake Jihar Katsina (UMYUK), sun koka kwarai akan rashin tallafin da shuwagabannin yankin nasu Ke basu.
Mai magana da Yawun Daliban kuma P.R.O, Comrade Bashir Funtua, ya nuna bakincikinshi akan yadda shuwagabannin dake shugabantar yankin na Funtua sukayi watsi da su alhalin ko wane yanki na taimakawa daliban yankin.
Yace: " Wajibine a kaina, a matsayina na daya daga cikin manya manyan shuwagabanni masu wakiltar dalibai yan asalin karamar hukumar Funtua, (P.R.O)UMAR MUSA YAR'ADUA UNIVERSITY KATSINA da inyi kira ga shuwagabanninmu wadanda suka hada da Muntari Dan-Dutse, Honourable Abu Total, Senator Abu Ibrahim, dasu sani fa mu munga yanda sauran shuwagabanni na sauran constituency da zone suke yi dangane da tallafa ma dalibansu ta hanyar daukema marasa karfi kudin registration, bayar da jamb kyauta, bayar da scholarship ga dalibai masu hazaka da basira a kowace karshen shekara, tare da ziyartarsu a makarantunsu domin ganin yanda suke tafiyar da harkokin karatunsu, da kyautata mu'amalarsu dasu"
Daga karshe ya yi tambaya da 'Shin wai me yasa mu dalibai yan Funtua bamu da wannan gatan?"
No comments:
Post a Comment