"Batu akan gyaran asibiti, hakika mu munyi zaben tumun dare, chanjin da muke tunanin gaba daya munyi kumumuwar munyi da sunan anyi canjin gwamnati to ba shine muke gani a yanzu ba."
Muhammad Kamal Nasir Nasiha, sakatare ne na kungiyar Arewa Youth Development, ya kasance cikin masu yin sharhi akan abubuwan da suka shafi mulkin gwamnati da kuma batutuwan dake faruwa a kowane bangare dake cikin kasar nan musamman Jihar Katsina. A wannan karon, Muhammad Kamal Nasir Nasiha ya ziyarci Wakilin CLIQQ Magazine inda ya dauki batu akan Gyaran Asibitin da Gwamnatin Aminu Bello Masari takeyi na General Hospital Funtua.
Kamal Nasiha ya ke cewa: "A zahirin gaskiya, idan ka dubi wannan asibiti ta General da aka ce ana anayin gyara, to ni a tunanina ba wani gyara bane gilla Gyaran Gangar Auzinawa. An Gina wannan asibitin tun a lokacin Murtala, a lokacin an ginashi ne da zummar cewa zai iya biyawa mutanen Funtua bukatunsu na wancan lokacin.
"A nan ina magana ne tun shekarar 1976, daga wancan lokacin zuwa wannan da muke ciki kuwa yawan mutanen Funtua ya karu kusan sau hudu. Allah ya jikan Matawallen Katsina, Umaru Musa Yar'adua, yazo ya Gina karamin asibiti [Comprehensive] a Bye-Pass don ya taimakawa wannan asibiti na General wajen rage taruwa da cunkoson mutane.
Idan muka duba a cikin Comprehensive, akwai fili da zai isa a gina irin wannan Comprehensive din guda hudu. Amma saboda son zuciya da kuma wani ra'ayi wanda namu San suwa ke shawartar wannan gwamnati ba, sai taje ta cunkushe Asibitin General wacce dama can a cunkushen take.
Yau ka shiga General Hospital ka gani, idan da za'ace wannan aikin da akayi a ciki a Comprehensive aka yi shi, da sai yafi amfanar mutane, sannan sai anfi samun biyan bukata.
A cikin asibitocin guda biyu, idan ka je yanzu da niyyar samun magani, Wa'iyazubillah, Cuta zaka samu. Saboda yanzu maganar da nike yi har a Funtua ankai mizanin da Mara Lafiya shine zai je da Aizal da sauran Kayan magance cutuka wasan da za'ayi wanke-wanke da sauran abubuwan da asibiti ne ya kamata ace yana bayar da su kyauta.
Sannan babu likita kwara daya da zaka nuna yanzu a Comprehensive, a yanzu haka ward-ward din a cike suke da marasa lafiya. Hakan ya tilasta dole marasa lafiya a Waje ake kwantar dasu bama wai ko a "Corridor" ba, idan ka kawo Mara lafiya don baka samu cikin daki ba, babu halin ka koma dashi, a hakan kaima zaka sama mashi waje a Waje ka shimfidar dashi. Ko wannan ya isa ya zama bala'i da kawo cutar da tafi wacce Mara lafiya yazo da ita.
Babban abun ma a yanzu an kara kudin magani, hatta Katin da ada naira Ashirin yake, yanzu samunshi ya zama tashin hankali. Sannan an dauki wani nauyi an kara dorawa talaka, a asibitocin anki samar da magungunan da ya kamata ace an Samar. Gaskiya duk shugaban da ya rasa wadanda dasu Fadi mashi gaskiya to yayi asara." Cewar Muhammad Kamal Nasir Nasiha.
Kusan hakan ne dai ke faruwa a zahirance, saboda mutane da yawa na ganin cewa ba'a cikin General Hospital bane ya kamata ayi sababbin gine-gine, kamata yayi a je Comprehensive inda suke da isasshen Fili, in yaso ita General sai ayi mata kwaskwarima saboda cunkuson da ake samu na Mutane.
A gefe daya kuwa, korafin da mutane keyi ba zai wuce ganin zunzurutun kudin da aka kashe don yiwa asibitin na General Kwaskwarima da sababbin gine-gine ba, inda suke cewa gwamnati ya kamata ta kasance mai dogon tunani ba wai abinda zasuyi ya amfani mutane kalilan ba. Sun buga misali da yadda likitoci ke wasa da rayukan al'umma musamman idan ya kasance Mara lafiyan talaka ne, sannan suka kara nuna cewa Kudin da aka ware donyin wannan Kwangilar ko kusa ba za'a kashe rabinsu ba a zahirin aikin da za'ayi.
Haka zalika, a kwanakin baya ne dai Shugaban kula da harkar lafiya a cikin majalisar Zartaswa ta jiha, (House of Assembly), Dan Majalisa mai wakiltar karamar hukumar ta Funtua, Alhaji Abubakar Muhammad Total, ya taba kai yunkurin dakatar da wannan aiki na asibitin inda yake nuna rashin aiki na gari daga dan kwangilar da kuma tunanin ana almubazzaranci da dukiyar gwamnati.
Da wannan jawaban ne yasa Wakilin namu dake a yankin Funtua, ya dauki kudirin zuwa wajen wanda aka baiwa kwangilar gyara da kuma yin sababbin gine-gine don jin gaskiya akan hasashe da zargin da mutane keyi a kan maku dan kudaden da aka kashe alhalin suna ganin kamar kwalliya ba zata biya kudin sabulu ba.
No comments:
Post a Comment