Monday, 24 December 2018

MARTANI KAN BAYANIN DA DANDALIN APC BIYAYYA FORUM, TA FITAR A KATSINA RANAR 22 GA DISAMBA, 2018.



MATASAN KATSINA MASU SON CANJI
(KATSINA YOUTHS FOR SUSTAINABLE CHANGE) (KYSC).
MARTANI KAN BAYANIN DA DANDALIN APC BIYAYYA FORUM, TA FITAR A KATSINA RANAR 22 GA DISAMBA, 2018.
“ … Darakta-Janar na SMEDAN da Manajin Darktan FMB ne kawai suka ba da tallafin karfafa gwiwa don samun nasarar tafiyar sake zaben SHUGABA MUHAMMADU BUHARI a 2019…”

A iya saninmu wannan ikirari da ke sama, wanda aka jingina shi ga Mai girma Gwamnan jihar Katsina da Ciyaman na jam’iyyar APC a jihar Katsina karya ne, kuma kwata-kwata ba gaskiya ba ne!

Tuesday, 18 December 2018

Har Yanzu Ganduje Bai Daina Karbar Dala Ba

Ofishin da Ganduje yake karbar Daloli an cire wuta a ciki, zuwa ake kawai a ajiye masa shi kuma saiya zaga yaje ya dauka, Har gobe Ganduje bai daina karbar Dala ba 
Mal. Abdullahi Sani Rogo.

Monday, 17 December 2018

Kalli yanda Nazir Ahmad ke shirin nadin sarautar da Sarkin Kano zaimai

A ranar 27 ga watan Disambarnan da muke ciki ne idan Allah ya yarda me martaba sarkin Kano, Muhammad Sanusi na II zai nada tauraron mawakin Hausa, Nazir Ahmad Sarkin wakarshi.

Mun Yi Nadamar Zaben Buhari, Cewar Kungiyar Matasan Arewa

Da yake jawabi a wani taron manema labarai da suka kira, Shugaban Kungiyar ta Matasan Arewa Alhaji Shettima Yerima, yace ya zama wajibi a garesu a matsayin su na Shugabannin Matasa a Arewa, su nuna damuwa da bakin cikin su akan abinda ya kira zaben tumun Dare da suka yi kuma suka sa Matasan Arewa su kayi ta hanyar zaben Buhari wanda suka bayyana a matsayin mara kishin Arewa.
Shugaban Matasan Arewan ya kara da cewar, ko kadan Buhari bai dace da shugabancin Nijeriya ba, domin a fili yake Babbar Kasa irin Najeriya ta fi karfin Mutum irin Buhari, wanda bai da gogewa ta bangaren ilimi, ko harkokin kasuwanci, hakan ya sa kullum Arewa sai kara fuskantar koma baya take, Talauci na cigaba da kisan kare Dangi ga Jama'ar yankin, amma abin mamaki Buhari ko a Jikinshi, sai cigaba da kwarabniya yake, ya zama Misalin makahon direba ya kwashi Jama'a zai kai ga halaka.

An saka motar Cristiano Ronaldo ta farko a kasuwa

Motar farko da tauraron dan kwallon kafar kasar Portugal, Cristiano Ronaldo ya fara saye, kirar Audi S3 a shekarar farko da ya je kungiyar Man United ta shiga kasuwa za'a sayar da ita, saidai abinda yafi daukar hankalin mutane shine zunzurutun kudin da aka tsugawa motar.

Sunday, 16 December 2018

An gano kabarin wani malami na zamanin 'fir'auna'

Masar ta gano hubbaren wani babban jagoran addinin wanda ya kai shekaru kusan dubu hudu da dari biyar da mutuwa.

An dai gano hubbaren ne a daya daga cikin katafaren yankin Saqqara da ake da dalar Masar irin ta zamanin da.

Buhari nada lokacin tara 'yan fim a yi sharholiya amma be da lokacin halartar jana'izar sojojin da suka rasa rayukansu wajan tsaron Najeriya-Atiku

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben 2019, Atiku Abubakar ya bayyana takaicinshi akan irin yanda shugaban kasa, Muhammadu Buhari ko mataimakinshi babu wanda ya samu halartar jana'izar sojojin da suka rasa rayukansu a harin Metele da aka yi yau, yace wannan abune wanda ba za'a yadda dashi ba.

Atiku ya bayyana cewa, a cikin wata sanarwa da ya fitar da jaridar Thisday ta wallafa, ya ga hotunan jana'izar sojojin da suka rasa rayukansu a yakin da suka yi da Boko Haram a Metele kuma yana mika ta'a ziyyarshi ga dukkan jami'an soji da iyalansu sannan yana fatan Allan ya baiwa iyalan mamatan juriyar rashin da suka yi.

MATSALAR TATTALIN ARZIKI: Gaskiya Ta Fito Daga Bakin Buhari

Ranar Juma’ar nan da ta shige ce Shugaba Muhammadu Buhari ya shaida wa daukacin gwamnonin Najeriya gaskiyar halin da tattalin arzikin Najeriya ke ciki, inda ya ce musu a gaskiya ya na cikin halin kaka-ni-ka-yi.

Buhari ya ce kafin a tayar da komadar da ta komadar da tattalin arzikin kasar nan, sai an yi da gaske, kuma su ma gwamnonin sai sun tashi tsaye wajen tsuke bakunan aljihun su.

Atiku ya kaiwa Sheikh Dahiru Bauchi ziyara

 
Dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar kenan a wadannan hotunan yayin da ya kaiwa babban malamin addinin Islama, Sheikh Darihu Bauchi ziyara a gidanshi.

Saturday, 15 December 2018

Sen Yakubu Lado ya tallafa wa marasa lafiya a kananan hukumomi guda hudu a yankin Daura



Dan takarar Gwamnan jihar Katsina na jam’iyar PDP Sen. Yakubu Lado Danmarke ya tallafa wa marasa lafiya a asibitin Daura.
Yakubu Lado ya baiwa duk marasa lafiyan dake asibitin naira dubu biyar (N5000) don rage masu radade wajen sayen magunguna. Da kuma garin Jani

Dan takarar Gwamnan Katsina Yakubu Lado bashi tsari (Blueprint) don tafiyar da mulkin Katsina



A satin da muke a ciki ne wasu jiga-jigan jam'iyar PDP suka yi wani taron sirri a Abuja a ofis din tsohon gwamnan Katsina Barista Ibrahim Shema.
Majiyarmu ta tabbatar mana da cewa taron ya hada da wadansu masu fada aji na jihar Katsina wadanda ke marawa jam'iyyar PDP baya da wadanda basa jin dadin yadda ake tafiyar da mulkin Katsina karkashin APC.

Gasar Sarauniyar Kyan Arewa: Kalli wadda tafi sauran 'yan matan Arewa kyau


 


Aisha Ibrahim ta kasance wadda ta lashe gasar Sarauniyar kyau ta Face of Arewa, na shekara ta 2018, da aka gudanar a jihar Kaduna. Aisha dai ta ce ta shiga gasar sarauniyar arewa, inda kimanin mata19 ne suka nemi gurbin zama zakarar gwajin dafi, na mace mafi kyau a yankin arewa, ta kuma sami nasarar lashe kambin.

Kalli hoton barkwanci akan yanda ake amfani da hukumar EFCC

Wannan wani hoton barkwancine dake nuna yanda ake amfani da hukumar EFCC akan 'yan Adawa.

Tuesday, 11 December 2018

AN KARRAMA SHAIHUNNAN MALAMAI TARE DA DANJUMA KATSINA.




Kungiyar marubuta ta kasa reshen jihar Kano (ANA) ta karrama wasu shaihunnan malaman Jami'a da suka  yiwa  harkar rubuce-rubuce hidima tsawon shekaru.
Taron karramawar na cikin taron da kungiyar ta saba yi duk shekara mai sunan  satin marubuta, wanda akan dauki sati guda cur ana gudanar da jawabai da mukaloli akan yadda za a bunkasa harkar rubutu a kasar nan.

Sunday, 25 November 2018

Atiku ya gana da manya-mayan 'yan Kannywood


Taurarin fina-finan Hausa masu goyon bayan dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar sun kaimai ziyara inda suka bayyanashi a matsayin dan takararsu.