Masar ta gano hubbaren wani babban jagoran addinin wanda ya kai shekaru kusan dubu hudu da dari biyar da mutuwa.
An dai gano hubbaren ne a daya daga cikin katafaren yankin Saqqara da ake da dalar Masar irin ta zamanin da.
Ma'aikatar adana kayayyakin tarihi ta masar ta ce hubbaren na wani
babban malamin addini ne na gidan sarauta da iyalansa a lokacin daula ta
biyar ta mulkin fir'aunan.
Bangon hubbaren na dauke da zane mutum-mutumin mutanen gidan da kuma
wasu zane-zane na kawa da ke nuna irin wasu ayyukan da sukeyi kamar tuka
jirgin ruwa, farautar tsunbtsaye da hadaya.
Sakatare janar na majalisar koli da ke kula da kayyakin tarihi na kasar
ta Masar, Dokta Mostafa Al-Waziri, ya ce a hubbaren akwai wasu sako-sako
wanda ke nuna cewa akwai alamomin wasu tarin kayayanki tarihi adane
acikinsa.
A wannan lahadin dai ake shirin soma aikin tono hubbaren wanda ake saran a sake gano wasu abubuwa tarihi da dama a ciki.
No comments:
Post a Comment