Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben 2019, Atiku Abubakar
ya bayyana takaicinshi akan irin yanda shugaban kasa, Muhammadu Buhari
ko mataimakinshi babu wanda ya samu halartar jana'izar sojojin da suka
rasa rayukansu a harin Metele da aka yi yau, yace wannan abune wanda ba
za'a yadda dashi ba.
Atiku ya bayyana cewa, a cikin wata sanarwa da ya fitar da jaridar Thisday ta wallafa, ya ga hotunan jana'izar sojojin da suka rasa rayukansu a yakin da suka yi da Boko Haram a Metele kuma yana mika ta'a ziyyarshi ga dukkan jami'an soji da iyalansu sannan yana fatan Allan ya baiwa iyalan mamatan juriyar rashin da suka yi.
Ya kara da cewa saidai abin takaici shine rashin zuwan shugaba Buhari
gurin jana'izar sojojin ko kuma mataimakinshi Osinbajo ko kumama su
wakilta wasu jami'an gwamnati su halarci jana'izar dan girmama wadannan
sojoji da suka rasa rayukansu.
Atiku yace, wannan ba abune da za'a amince dashi ba.
Yace kwana daya kamin jana'izar sojojin shugaba Buhari ya ajiye dimbin
aikin dake gabanshi ya tara 'yan fim aka yi sharholiya amma ya kasa
halartar jana'izar sojoji wannan abin takaicine babba.
Yace yana girmama harkar fim kuma a lokacin da yake mataimakin shugaban
kasa ya bayar da gudummawarshi akai da kuma da yake zaman kanshi amma
abin takaicine ace ana da lokacin nishadi amma ba'a da lokacin girmama
masu bamu tsaron kasa.
No comments:
Post a Comment