Aisha Ibrahim ta kasance wadda ta lashe gasar Sarauniyar kyau ta Face of
Arewa, na shekara ta 2018, da aka gudanar a jihar Kaduna. Aisha dai ta
ce ta shiga gasar sarauniyar arewa, inda kimanin mata19 ne suka nemi
gurbin zama zakarar gwajin dafi, na mace mafi kyau a yankin arewa, ta
kuma sami nasarar lashe kambin.
Ta kara da cewa da farko dai ta fuskanci 'yar matsala na rashin yarda
daga wajen iyayenta, amma daga bisani sun aminta da sana’ar daga baya da
suka fuskanci, ba kamar sauran gasar sarauniyar kyau ba ne, da ke nuna
rashin tarbiya wanda ake fitar da jiki a waje.
Kasancewar ita dalibace, ta bukaci iyaye da su dinga marawa ‘ya'yansu, a
duk lokacin da suke yunkurin gudanar da wani abu dake bukatar yi,
matukar bai sabawa shariah na addini ko al’adda ba, tare da basu kwarin
gwiwa wajen cimma muradansu.
Daga karshe ta ce a wannan zamani ya kamata mace ta fita ta nemi hakkin
kanta, matukar ba zata taka ka’idojin adinin ta da al’adarta ba, zama
bana mata bane a wannan karni da ake ci ko da mace ta na da aure waji bi
ne su nemi na kansu.
Rariya.
No comments:
Post a Comment