Da yake jawabi a wani taron manema labarai da suka kira, Shugaban
Kungiyar ta Matasan Arewa Alhaji Shettima Yerima, yace ya zama wajibi a
garesu a matsayin su na Shugabannin Matasa a Arewa, su nuna damuwa da
bakin cikin su akan abinda ya kira zaben tumun Dare da suka yi kuma suka
sa Matasan Arewa su kayi ta hanyar zaben Buhari wanda suka bayyana a
matsayin mara kishin Arewa.
Shugaban Matasan Arewan ya kara da cewar, ko kadan Buhari bai dace da
shugabancin Nijeriya ba, domin a fili yake Babbar Kasa irin Najeriya ta
fi karfin Mutum irin Buhari, wanda bai da gogewa ta bangaren ilimi, ko
harkokin kasuwanci, hakan ya sa kullum Arewa sai kara fuskantar koma
baya take, Talauci na cigaba da kisan kare Dangi ga Jama'ar yankin, amma
abin mamaki Buhari ko a Jikinshi, sai cigaba da kwarabniya yake, ya
zama Misalin makahon direba ya kwashi Jama'a zai kai ga halaka.
Alhaji Yerima ya cigaba da cewar ya zama wajibi ayi taron Dangi a kawar
da Buhari daga mulki a 2019 kafin ya karasa kassara yankin Arewa, inda
yace wannan shine babban dalilin da yasa sanannen Dattijon nan mai
kishin Arewa Farfesa Ango Abdullahi ya fito fili ya ankarar da Jama'a
hatsarin cigaba da mulkin Buhari, saboda babu abinda Buhari yayi na
cigaba a Arewa, dukkanin ayyukan raya kasa an tattara su gaba daya a
Jihohin Yarbawa, saboda Manyan Ma'aikatun Gwamnatin Tarayya uku a dauka
an damkawa Mutum guda Bayarabe Fashola, wato Ma'aikatun Ayyuka da haske
Wutar Lantarki da Gidaje, shin babu Dan Arewan da ya Cancanta ne wanda
za'a dauki daya daga cikin Ma'aikatun nan a bashi ne? Amma maimakon a
fahimci maganar Ango Abdullahi sai aka fito ana ta zagin shi.
Shugaban Matasan Arewan ya bayyana cewar, Allah yayi wa 'Yan Arewa
ilhama, tun da Buhari da kanshi ya fito yace tattalin Arzikin Najeriya
ya karye, wato abinda hakan ke nufi shine 'yan Najeriya musanman'yan
Arewa zasu kara shiga cikin wata rayuwa mai kunci fiye da wacce suke
ciki a yanzu, kuma tuni matarshi wacce tafi kowa kusanci da shi ta fito
fili ta shelantawa Duniya cewar da akwai matsala a yadda salon
Shugabancin Mijinta ke tafiya, idan kuwa haka lamarin yake ya dace 'yan
Arewa su samawa kansu mafita, domin muddin Buhari ya yi Tazarce zuwa
2023 to tabbas Yarbawa zai mikawa ragamar mulki, idan kuwa mulki ya koma
hannun su kafin ya dawo Arewa sai yayi akalla shekaru takwas, saboda
haka dole mu dauki matakin maganin abin, ta hanyar duba wanda zai kai
Arewa ga Tudun Mun tsira, kuma a 'yan takarar da suka fito neman
Shugabancin Kasa a yanzu, Atiku Abubakar shine damar da ta ragewa Arewa,
inji shi.
No comments:
Post a Comment